TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Adam yana ganin ya fito ya taso da sauri ya taho gurinsa, kallo daya zakayi masa kasan cewa hankalin sa a matukar tace yake dan yanzu a duniyar sa bayan Sumayya da iyayenta da suka karbe shi irin karbar da akeyi wa family member baya jin yana da kamar Hussain a duniya, shine gatan sa, shine tutiyarsa, a makaranta har kallon dan masu kudi ake yi masa saboda irin suturar da yake sakawa kuma duk na Hussain ne, babu wanda zai gansu tare yace drivern sa ne shi sai dai a dauka ko kaninsa ne.
Yace “oga Hassan ya jikin oga Hussain? Sun hanani shiga ciki tun dazu” Hassan ya bude motar yana duba wayarsa a inda ya zauna bai ganta ba amma sai yaga ta Hussain. Ya dauka ya fito yana kallon Adam da fuskarsa take nuna cewa yana gab da fashewa da kuka, ya dafa kafadar sa yace masa “Adam, Allah ya karbi oga Hussain” sai Adam yaji kamar bai ji sosai ba, sai yaji kamar bai iya hausa ba kuma, yace “what? Ban gane ba oga Hassan” Hassan ya tsaya kawai yana kallon sa ya kasa furta kalmar mutuwa tare da sunan Hussain a tare. Sai daya hadiye wani abu sannan yace “Adam Hussain ya mutu, Hussain ya tafi ya barni” sai ya dora kansa a kafadar Adam ya fara wani irin kuka wanda babu maiji sai Adam din da yake yi a jikinsa.
Adam ya sandare a tsaye, oga Hussain, oga Hussain din da suka taho yanzu tare suna hira suna dariya suna nishadi shine za’a ce ya mutu? Me ya same shi? Sai ya dora hannunsa a kafadar Hassan, yana jin yadda jikinsa yake motsawa da kukan sa, yanajin yadda hawayensa yake jika rigarsa da kuma yadda zafin jikinsa yake ratso har nasa jikin yace “innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ka ringa maimaita innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allah zai saka maka nutsuwa kuma zaka ji sanyi a zuciyarka. Kayi kukan kuma yana da kyau ga lafiyar ka, amma kar kayi mai kara dan yana kara azaba ga mamaci” Hassan ya cikashi ya koma ya zauna a cikin motar kafafuwansa a waje. Ya jingina kansa da head rest yana sauraron rarraunar muryar Hassan yana maimaita masa fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Shima sai ya fara fada har ya samu nutsuwa sannan ya bude wayar Hussain da take hannunsa. Missed calls din fatima ya gani har 30+, gabansa ya fadi, kar dai har taji? Amma in taji baya jin zata samu karfin zuciyar kiran Hussain. Amma baya so ya kirata dan vai san me zai ce mata ba, sai dai bai san wanda zai fara kira ba, Aunty? Ko kuma wani a cikin yaran gidan maza? Ko Gombe zai kira? Amma kafin suzo Kaduna fa?
A karshe ya yanke shawarar kiran Aunty yayi mata dabarar da zata kai Fatima part dinta sannan ta karbe wayarta. Sai dai bai san me zaice da auntyn ba. Amma kuma kafin ya kira sai ga kiran auntyn ya shigo wayar Hussain din. Ya runtse ido tare da gyaran murya ya dauka, kafin yayi magana ta fara magana ita “Hussain kuna ina? Kasan Fatima ta biyo ka Abuja kuwa? Yanxu na shiga gidan mai gadi yace min ai Lawan driver yace masa Fatima tace zai kawo ta Abuja. Me zata yi a nan din” Hassan ya rikice “Abuja? Fatiman?” Tace “Hassan? Ina Hussain din? Neme su a waya dan ance tare da Ruqayyah suka fito sun biyo bayan ku” Hassan yaji hankalin sa ya sake tashi, bai iya cewa da ita komai ba sai ya kashe wayar tare da dafe kansa yana digesting maganar, Fatima da Ruqayyah suna kan hanyar tahowa Abuja a mota saboda me? Kuma wai harda Ruqayyah, Ruqayyan da tun safe ta fita daga ce masa gata nan yanzu zata dawo amma har suka fito bata dawo ba kuma bata dauki duk kiran da yake mata da niyyar gaya mata zaiyi tafiyar ba. Yanzu kuma wai tabiyo Fatima sun taho Abuja.
Shi bai ma san ta inda zai fara ba, da abinda yake ji a zuciyarsa zai fara ko kuma da gawar Hussain da take kwance a daki tana jiran a shiryata ga magrib tana dosowa ko kuma da tracing Fatima da Ruqayyah a garin Abuja, ko kuma da rarrashin sisters dinsu da yasan labarin mutuwar Hussain yana gab da zuwa gurin su. Ya sake daukan wayar ta nemo number din Ruqayyah ya kira. Bugu daya ta dauka tana cewa da Fatima “ga mijin naki nan yana kiran wayata” Fatima tayi zumbur ta mike daga kwanciyar da tayi bayan ta gaji da kiran number din Hussain. Ruqayyah ta ce “Hello, yallabai” sai taji muryar Hassan yace “Hassana kuna ina yanzu?” Ta dan kalli Fatima tana girgiza mata kai sai tace “yanzu muke shigowa garin Abuja ni da Fatima, muna ta missing dinku a gida shine muka biyo ku dan ba ………..” Yace “listen to me please. Ki gaya wa Lawan ki ce inji ni nace ya juya mota ku koma Kaduna yanzu, muma mun gama duk abinda muke yi yanzu muke shiga mota zamu taho” tace “to mu karaso mana sai mu dawo tare?” Yace “Ruqayyah, just do what I said please. Ina Fatima?” Ta kalli Fatima da take zaune a edge of her seat tace “gata nan muna tare” yace “ki kula da ita please Ruqayyah, kuna zuwa gida u tafi part din Aunty ku jira mu karaso please. Dan Allah Ruqayyah kiyi haka kinji?” Tace “me ya samu muryarka ne?” Yace “mura nake yi” ta dan tabe baki tana jin haushin yadda yake jaddada mata ta kula da Fatima kamar wata yar gold, tace “shikenan, za’a yi duk abinda kace” yace “good” ya katse wayar.
A lokacin ne wani Doctor ya fito yana yi masa maganar yazo ya bude dakin da Hussain yake za’a yi preparing dinsa for release. Sai yaki basu key din instead sai ya mike da kansa ya tafi zai bude musu, dai dai nan yaji gabansa ya fadi, ya juyo da sauri yana kallon bakin gate yana jin zuciyarsa tana ingiza shi kamar ya fita da gudu ya tafi kaduna a kafa,ya juya kuma ya kalli cikin asibitin yana tuno gawar Hussain a daki. Sai ya dawo da baya ya samu Adam yace “Adam dan Allah tafi kabi su Fatima, in ka gansu a hanya ka kula dasu and make sure sunje gida lafiya, ni zan tsaya mu taho da Hussain a ambulance. Please. Adam ka kula da Fatima kaji?”
Adam ya gyada kai yana ganin ba sai an roke shi ba, abinda Hussain yayi masa ya wuce haka a gurinsa dan haka zai iya ajiye rayuwarsa for Fatima. Ya shiga motar da suka zo da ita ya tayar ya bar compound din asibitin.
A wata mota a gefen asibitin, wanda yake gaban stirring yace “oga, gashi nan ya fito, kuma kamar shi kadai ne a motar” wanda aka kira da oga yace “then what are you waiting for? Follow him. Maybe mu samu chance din kama shi shi kadai”
**. **. ***
Fatima ta kalle ta “ba Hussain bane ba? Me yasa bai kira wayata ba bayan yaga ina ta kiran sa?” Ruqayyah tace “ba Hussain bane ba, Hassan ne yace mu juya mu koma gida suma gasu nan har sun gama zasu taho” Fatima ta fara girgiza kanta tana bubbuga hannunta a jikin kujera “ba dai Hussain ba, Hussain ba zai taba haduwa da Sadiq abokinsa bayan tsahon lokaci sannan su gaisa briefly ba, wani abun ne ya faru, wani abun ne ya faru da Hussain dina”
Sai Ruqayyah taji jikinta yayi sanyi dan itama taji abin odd, mai yasa Hassan zai kira ta da wayar Hussain bayan kuma Hussain din ai biyo lodin kiran da Fatima take masa ba? Bayan kowa yasan irin tsananin son da yake yi mata. Amma sai bata ce komai ba ta gaya wa Lawan sakon Hassan. Bai musa ba ya rage gudun motar lokacin duna gab da shiga cikin gari sannan ya fara kokarin juya motar ya koma hannun dawowa. A lokacin ne sukaji Minal da tun dazu ta dukufa akan wayarta tana ta danne danne ta rafka salati, “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun” Fatima ta yunkuro kamar zata mike tsaye, babyn cikin ta ya harba da karfi. Minal ta juyo tana kallonsu idonta kamar zai fado kasa tace “Ruqayyah? Hussain din ku ba shine Hussain Aminu Abdullahi ba” Fatima bata ce komai ba, saboda ba zata iya magana ba, Ruqayyah tace “shine? Me kika gani? Me ya faru?” Ta juyo musu da screen din wayar ta tace “Ya mutu? Gashi nan ana fada a twitter ya mutu a wani asibiti a Abuja”