TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Kamar daga sama taga wani katon gini a gabanta, a jikin gate dinsa an rubuta baro baro “Nationa Orphanage of Nigeria” ta tsaya tana kallon rubutun sannan ta kalli yaron da yake hannunta “orphane” bashi da uba bashi da uwa dan haka orphane ne kuma babu inda ya dace dashi irin Orphanage. Ba tare da tunanin komai ba tabi inuwar jikin ginin zuwa bakin gate din sannan ta sunkuya ta ajiye shi tana kawar da ganinta daga kansa dan kada tausayin sa ya hana ta aikata abinda ta riga ta yanke shawara.
Ta juya da sauri tana barin gurin, sai kuma ta tuna da dankalin ta da yake jikin yaron, evidence ne, za’a iya amfani dashi a binciko wadda ta ajiye shi dan haka ta koma da sauri ta zare dankwalin nata daga jikinsa ta koma cikin bishiyoyi da sauri, tana jin gurin gabaki daya yana amsa kuwwa da karar kukansa. Ta saka hannayenta ta toshe kunnuwan ta tana kara sauri, zuciyarta tana gaya mata yanzu za’a dauke shi dan ta tabbatar kukan ya shiga har cikin gidan.
Sauri take yi sosai tana retracing steps dinta har ta dawo gurin accident din, wutar har tayi kasa sosai ta kusa karasa mutuwa, a gefe taga jakar Minal tare da karafunan motar da suka fita, ta dauka ta jefa ta cikin wutar tana kallon ta ta kama tana konewa, tana jin wani abu a zuciyarta wanda ta kasa fasaltawa.
Babu wanda yasan sun taho da Minal, maybe mai gadi ya ganta shima kuma in ya fada zata iya cewa a hanya suka ajiyeta ta tafi gida, babu mai musa mata. In akazo gurin motar abinda za’a gani shine gawar driver da mace mai ciki a gaba, babu wanda zai ce ba Fatima bace ta mutu tare da abinda yake cikin ta. Problem solved.
Ta juya tana kallon hanyar inda Fatima ta haihu, ta kunna fitilar wayar Fatima da take hannunta ta tafi gurin tana tunanin yadda zata yi ta kawar da gawar .
Amma………
Babu gawar Fatima babu alamar ta…….
Ta cigaba da haske haske a gurin amma babu ko trace na Fatima sai jini a inda akayi haihuwar. Hankalin Ruqayyah ya tashi. Taji kafarta da taji ciwo ta rike, ta kama ta amma sai taji ta sandare, sai ta fara janta tana barin gurin, tsoro kuma yana zuwa mata zuciyarta. Kamar daga sama taji wayar Fatima da take hannunta tayi kara, network ya dawo kuma, “Mi Amour” taga an rubuta, ta dauka da sauri “hello” taji muryar Hassan da alamar tashin hankali a tare dashi “Hassana ina kuke? ina Fatima? Ya akayi baku karasa gida ba har yanzu” a rikece ta amsa masa “Hassan mun shiga uku, kuzo ku taimaka min, accident muka yi, duk sun mutu, duk sun mutu Hassan na shiga uku” shiru taji a wayar, sai hayaniyar mutane a background amma babu muryar Hassan.
**. **** *
Adam yana ta kwarara gudu a hanya, hankalin sa a tashe, lokaci zuwa lokaci yana share kwallar idonsa da take kokarin kare masa ganin titin da yake gabansa, yana kuma dudduba motocin da yake wucewa ko zai ga motar da su Fatima suka taho da ita. Mutuwar Hussain ta daga masa hankali ba kadan ba, yaji duniya gabaki daya ta fita daga kansa yaji duk wasu birikan sa ashe duk shiririta ne. Duniya gabaki dayan ta zancen banza ne.
Yana barin gari ne ya hango wata mata tana tafiya a gefen bishiyoyin bakin titi, hannunta kamar da jariri kanta babu dankalin, ta mirror ya ga kamar tayi masa kama da Ruqayyah. Sai ya dan daga motar yana so ya gani sosai amma sai ya neme ta ya rasa, ya girgiza kansa, maybe idonsa ne yake yi masa gizo. Yana yin gaba kadan kuma sai yaga wani abun daya daga masa hankali ya saka ya taka burki da sauri. Fatima, a tsaye a bakin titi, jikin ta futi futu kamar tayi wanka da kasa. Ya yi packing ya fito da sauri yana kallon ta dan ya tabbatar ita din ce, kallon sa kawai take yi kamar bata gane shi ba sai kuma ta miko masa hannu tace “help me”
Ya lurada ciwo a kafadar ta yana jini, sannan ya lura da kasan rigar duk jini da kasa, sai kuma ya fahimci babu ciki a jikinta. “Madam? Me ya faru daku? Accident kuka yi, ina sauran suke” tace “Hussain. Ka kaini gun Hussain dan Allah” ya ji zuciyarsata karye, hankalin sa kuma ya tashi, daga gani a rude take bata san ma me take cewa ba, ya fara kalle kalle dan ya tabbatar a kusa da gurin ne suka yi accident din tunda ya ganta a gurin kuma a kafa. Ya kama ta ya zaunar da ita sannan ya dauko wayar sa ya fara neman number din Hassan amma bai san ma me zai ce masa ba, yana tsananin tausayawa halin da Hassan din yake ciki, ga mamakin sa sai yaji wayar tana kara a cikin mota, sai ya katse ya fara neman ta Hussain, sai dai kafin ta shiga yaji tsayawar mota a bayansu, ya juya da sauri, abinda ya gani shi ya saka shi sakin wayar ya juya kamar zai fita a guje sai kuma ya tuna da Fatima sai ya dawo ya tsaya a gabanta yana kare ta daga wandanda suke tahowa.
Babansa ne mahaifi, tare da wasu maza karfafa su biyu. Ya dauke kansa yana kallon gefe a ransa yana tsananin mamakin yadda aka yi suka iya biyo shi har nan. Uban yace “Joseph? Wannan shine taryen da zaka yiwa babanka? Ka gama guje gujen?” Adam ya girgiza kansa yace “sunana ba Joseph ba, sunana Adam, Joseph din da kuka sani ba shine wannan ba” uban yace “say whatever you want to say, call your self whoever you want to call your self amma ni nasan you are my son, my responsibility, and I am taking you home” Adam ya girgiza kansa, “ni ba danka bane ba, kuka babu inda zanje” sai ya juya ya kalli wadanda ya taho dasu yace “ku dauko min shi” Adam ya sake yin kamar zai gudu amma kumaba zai iya barin Fatima ba wadda duk abinda suke yi take binsu da ido. Ya kalle ta sai ya daga hannunsa yace “zan bika, ka barni in taimaka mata please, in ka barni na taimake ta bazan kuma guduwa ba” mutumin ya kalli Fatima yace “wacece ita? Your girlfriend?” Adam ya gyada kansa yace “yes. She is injured, let me help her please”
Uban yayi murmushi, a ransa yana ganin ya samu weakness din dan, ya dauki wayar adam da ta fadi a hannunsa ya yi jifa da ita cikin ciyayi sannan yace ya dauko Fatima ya shigo da ita cikin mota su tafi, sai da suka shiga motar sannan yace “say bye bye to the north. You are never coming back here”.
This is the Intermission of the Story
Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020.Broken
Tunda Hassan ya tura Adam yabi bayan su Fatima hankalin sa bai kwanta ba, magana likitan yake yi masa amma shi hankalin sa ya kan kofa, yana ta kallon hanya yana jin kamar ya bi bayan Adam din dan ya tabbatar ta samu su Fatima ya mayar da su gida lafiya lau. Amma kuma baya sin ya tafi ya bar gawar Hussain tare da mutanen da bai yarda dasu ba duk kuwa da cewa yanzu police sun zo asibitin kuma su zadu raka gawar Hussain har Kaduna. Sama sama yake jin abinda suke cewa, aka miko masa takarda yayi signing duk da bai san signing din me yayi ba but yasan ba zai wuce ta sallamar su ba. Sannan aka dora Hussain akan gado mai taya aka turo shi zuwa waje, inda by now mutane sun fara tsatstsayawa a waje suna kallo, wasu da wayoyi a hannunsu suna daukan hoto, Hassan ya kara tabbatar da cewa duk jikin Hussain a rufe yake babu abinda ake gani sannan ya sa aka kawo bakin ambulance din dai dai kofa yadda suna fitowa kawai shiga ciki sukayi shi da police guda biyu da kuma maaikacin lafiya guda daya, sannan aka rufe kofa. Daya police din kuma ya zauna a gaba tare da driver suka dauki hanyar kaduna.