TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Hassan yana zaune kawai hannunsa daya a dafe da gawar Hussain ya zubawa farin matafin da aka rufe shi dashi ido amma ba zai ce ga abinda yake tunani ba, tabbas kukan da yayi dazu a jikin Adam yaji dadin yinsa dan yaji nauyin da yake ji a kirjinsa ya ragu sosai amma duk da haka tunanin sa bai dawo dai dai ba. Suna kokarin barin gari ne wayar Hussain da take hannunsa tayi kara, ya duba yaga sunan Adam. Gaban sa ya fadi sai ya dauka da sauri “Hello, hello” amma baya jin magana clearly sai dai yan maganganu a can nesa, a cikin maganganun akwai muryar adam din amma baya fahimtar me suke cewa amma kamar shi da wani namiji suke magana. Ya katse kiran sannan ya sake kira amma har ta gama ringing ba’a daga ba, ya sake kira shima shiru. Sai ya kuma jin hankalin sa ya kara tashi. Ya dan daga labulen da aka rufe tagar motar yana lekawa yana jin a ransa yana so yake kallon hanya. Amma kuma babu abinda yake gani din.
Ya sake gwada number din Adam amma ba’a dauka ba still, ya kira wayar Ruqayyah bata shiga sai ya nemo number din Fatima ya kira itama not reachable, ya sake gwadawa sai taji ta shiga kuma lokaci daya aka daga “Hello” yaji muryar Ruqayyah, da alamar tashin hankali a tare da ita, yace “Hassana ina kuke ne ya akayi har yanzu baku je gida ba?” Cikin dimauta yaji tana magana da sauri “Hassan mun shiga uku, kuzo ku taimaka min, accident muka yi, duk sun mutu, duk sun mutu Hassan na shiga uku”.
Ya girgiza kansa da sauri sannan ya kalli wayar hannun sa yana so ya tabbatar daga ita ne maganar take fitowa, ganin seconds suna reading ya tabbatar masa da tabbas daga ciki ne kuma abinda ya ji gaskiya ne dan ta muryar Ruqayyah kadai yasan babu maganar masa a cikin bayanin ta. Sunyi accident, duk sun mutu saura ita kadai, su waye duk din? Fatimah? Abinda yake cikin Fatima? Dan Hussain? Is only link to Hussain? Ji yayi wayar ta zame daga hannunsa ta fadi a kasan motar. Kwakwalwar sa ta tsaya chak sannan kuma a hankali jikinsa ya zame daga kan kejerar ya fadi kasa.
Mutanen cikin motar ne suka fara salati, ma’aikatan lafiyar yayi sauri ya kai hannun sa wuyan Hassan yana feeling heart beat dinsa kuma ya tabbatar da akwai sannan ya fara bashi taimakon gaggawa yayinda daya daga cikin police din ya dauki wayar wadda suka tabbatar ta cikin ta aka gaya masa abind ya sumar dashi ya kara a kunnensa “hello” Ruqayyah tace “hello waye? ina Hassan?” Yace “wacece? Hassan gashi muna tare dashi, wacece ke?”
Duk da Ruqayyah taji wani iri kuma taji a jikinta wani abu ya faru da Hassan amma itama a yanzu taimakon take bukata ido rufe, tace “sunana Ruqayyah, ni ce matar Hassan Aminu Abdullahi. Ina cikin daji munyi accident tare da gimbiya Fatima matar Hussain Aminu Abdullahi da kuma drivern mu, motar mu ta kama da wuta, Allah yayi musu rasuwa, ni kadai na rage yanzu. Ina neman taimako dan bansan a inda nake ba” san sandan ya juya yana kallon yanuwan sa, sai kuma ya kalli gawar Hussain yana jinjina hikima ta ubangiji daya dauki ran mata da miji a lokaci daya ba tare d kowannen su yasan da mutuwar dan uwansa ba. Tabbas wannan labari ne da zai iya saka Hassan yayi abinda yafi suma ma ba suma ba, briefly ya fada wa sauran abinda matar tace, sai wani a cikin su ya karbi wayar yayi setting dinta ta yadda zasu ke tracking wayar hannun Ruqayyah suka ga inda take sannan suka sanar mata da cewa gasu nan zuwa, sai kuma suka yi waya station aka turo musu da wata motar suka hadu a hanya suka rabu biyu wadansu suka tafi gurin Ruqayyah wadansu kuma suka wuce da gawar Hussain da kuma unconscious Hassan.
Ruqayyah kam tsoro take ji, ta bar gurin motar tayi hanyar da zata mayar da ita kan titi dan ji take kamar gawawwakin da suke cikin mota suna miko hannu zasu jata zuwa cikin sauran wutar da bata karasa mutuwa ba. Sannan kuma tana jin tamkar Fatima tana binta a baya, tamkar nemanta da tayi ra rasa ta zama fatalwa ne zata galaka ta saboda yar mata da yaron ta da tayi. A idonta take ganin kamar wulkawar Fatima ta gefenta, in kuma ta rufe idon ko da da niyyar kifta shi ne sai taga idanun Minal suna kallonta kamar yadda ta ganta a cikin mota a mace. Ga kafa ta rike, sam taki lankwasuwa sai janta takeyi ta sandare kamar wani ita ce. Duk kuma wannan da sauki akan abinda take ji a zuciyarta, wani irin feeling wanda ba zata iya misalta shi ba.
Ta fara tuno masoyan ta, ƴaƴan ta guda uku, Sumayya, inna Ade da Baba, suleiman da Zunnur dan duk abinda take yi, duk wannan fadi tashin da take yi da wannan dakakkiyar zuciyar tata amma ita kanta ta san tana son su sosai sai dai kawai ita bata iya nuna soyayya ba, ga kuma Hassan , da kin ta da sonta he have come to be part of her, ba zata ce tana masa so na soyayya ba amma ta damu dashi. Ta runtse idonta tana matse hawayen daya taru a idonta yake disashe mata ganin ta amma kuma hoton fuskar Minal data gani shi ya saka ta yi saurin bude idon tana kokarin kara sauri ama kafa taki bada hadin kai. Gani take kamar gawawwakin ne suka rike mata kafar. A kunnuwan ta har ji taje yi kamar ana maganganu kasa kasa. Sai kuma taji kukan jaririn data ajiye yana amsa kuwwa a kunnuwan ta.
Kuka take yi sosai, tana kokarin yin sauri iyakacin iyawarta amma in ta waiga sai taga babu inda taje, still bata wani yi nisa da motar ba. Sai data kwashe lokacin da a gurinta kamar ya kai tsahon shekara guda sannan taji gunjin mota tana shigowa gurin, sai kuma taji hayaniyar mutane sannan taga an haske ta da fitila. Hasken da ta ji shi har cikin zuciyarta, ta sauke ajjiyar zuciya tana tunanin karshen wahalar ta yazo. But that is just the beginning.
Tana ji suka karaso inda take suka kamata suka sakata a motar da suka zo da ita sannan wasu suka tafi gurin accident din suna kokarin karasa kashe sauran wutar da take ci, tana jin su suna ta yawa suna fadar abinda ta gani, sun dan fara yi mata tambaya amma ganin yadda take a rikice yasa wani wanda take tunanin shine babban su yace su rabu da ita kawai, a lokacin wata motar ta karaso kamar ta fite service da kuma wata karamar mota again, taji suna ta maganar abin taji kuma sun ambaci mutuwar Hussain, sun kuma fahimci abinda take so su fahimta na cewa Fatima matar Hussain ce a cikin motar, sun kuma fahimci wacece Fatima dan take taji wani yana waya Kano cewa a sanar da gidan sarautar kano sunyi rashin yarsu, gimbiya Fatima.
Ta lumshe idonta tana jingina da jikin kujerar motar, the dead is now complete, ta haka ta binne sirrinta babu gudu babu ja da baya, amma kuma ina Fatima take? In kuma bata mutu ba fa? In kuma tashi tayi ta tafi fa? In kuma yanzu already tana hanyar Kaduna kuma fa? In ta fada tace ta haihu ta bawa Ruqayyah dan ya zata yi kenan? Me zata ce?
Ta girgiza kanta da sauri tana cewa “uhm uhm” a fili kamar wata zararriya. It is going to be her words against fatima’s. Zata musa ne da duk iyakacin iyawarta tace ita bata karbi da ba, tace Fatima sharri take yi mata. To amma kuma in aka tambayeta game da gawar da take cikin mota wadda ta riga ta furta cewa ta Fatima ce fa? Me zata ce akan hakan? Tabbas bata haƙa ta binne sirrinta ba, tabbas yana nan a bude kuma yana tare da Fatima a duk inda take. But What if ta mutu da gaske wani ne ya dauke gawarta, ko matsafa, ko naman daji? There is still hope for her amma bata da tabbas, kuma tasan wannan rashin tabbas din tabbas zai ke hana ta bacci. A koda yaushe, Fatima zata iya bayyana kuma bayyanar ta yana nufin bankaduwar sirrinta.