TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Wannan kuma yana nufin rasa komai nata………
Including iyayenta, dan tasan direct Baba zai tsine mata inna Ade kuma tace babu ita babu ita har abada
But for now, shin gawar Minal tayi konewar da ba za’a Iya gane ta ba? Ta tambayi kanta tana lekawa ta taga, kamar amsar tanbayarta taji wani a gurin yana cewa. “Ayi wa yanuwansu waya, sai dai a binne su anan dan ba zasu dauku ba, sun zama gawayi” ta lumshe idonta da niyyar yin ajjiyar zuciya amma fuskar Minal data gani ya saka ta bude idon da sauri.
Motar da take ciki aka bawa umarnin ta tafi, a kaita Kaduna gidan mijinta, wannan yasa taji hankalin ta ya kwanta, sai dai suna barin gurin ta juya tana kallon gurin. A nan ne rayuwarta ta kare, anan ne kuma rayuwarta ta fara. Su Kusan rai shida suka bar Kaduna a mota, amma a cikin su ita kadai zata koma garin Kaduna.
. ***. **
Da taimakon maaikacin lafiyar da yake cikin ambulance din Hassan ya fara dawowa hayyacin sa, amma sai dai shi har cikin zuciyarsa bai so dawowar tasa ba, so yake ya tafi shima, so yake yabi Hussain, baya so ya cigaba da rayuwa. Wannan wacce irin jarabawa ce uban giji yake yi masa?
Ya kamo hannun Hussain ya rike “Hussain! Ka tafi dani nima mana! Hussain Fatima ta bika ka roka min ubangiji nima ya dauke ni in biku! Hussain Fatima ta tafi , ta taho tare da abinda yake cikin ta. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun” duk rarrashin duniya babu wanda ba’a yi masa ba amma ya kasa yin shiru. So yake wai maybe in ya ishe su da magana su gaya masa cewa ba gaskiya bane ba, su gaya masa Fatima da abinda yake cikinta suna raye, su gaya masa Ruqayyah ba gaskiya ta fada ba ko kuma anje an tarar basu mutu ba but instead of su ce haka sai yaji suna waya da yanuwansu na can akan a gaya masa gawar Fatima ba zata dauku ba sai dai a binne ta a can.
Girgiza kansa kawai yake yi, so yake yayi kukan amma ya kasa sai magana kawai yake yi da gawar Hussain kamar wani tababbe. Tabbas mutuwar Hussain ta taba shi amma bata yi masa dukan da wannan ta Fatima tayi masa ba. Saboda dama yasan Hussain bashi da lafiya, kuma a hannun sa ya mutu. Amma Fatima fa? Hussain yana mutuwa ba abinda yake so sama da abinda yake cikin Fatima amma ashe ko ganin sa ba zai yi ba, ashe ko numfashi ba zai shaka ba. Wannan wacce irin jarabawa ce? Anya zai iya ci kuwa? Ace a rana daya babu Hussain babu family dinsa? Babu komai sai memory dinsa?
Memory mai dadi…….
Memory mai zafi…….
Memory mai tsayawa a zuciya……
Yana jin wayar Hussain tanata ringing amma ya kasa kallon ta ma ballantana yayi tunanin dauka. Ba zai wuce mutanen gidan su ba, ba zai wuce aunty ko yan uwansu ba, sun kira shi suji da gaske ne? Da gaske Hussain dinsu ya tafi ya barsu? Da gaske Fatima tare da babyn su sun bi shi inda ba’a dawowa?
Ba zai iya amsa musu ba…..
Ba zai iya kallon wayar ba…..
Ba zai iya kallon hoton Fatima hannayenta a dafe akan cikin ta tayi shape din heart da yatsunta a kan cikin ba, wanda shine hoton da yake kan wayar.
Sai ya saka hannu ya kife wayar, baya jin zai iya magana da kowa.
Ya tuno da nasihar da Adam yayi masa dazu “innalillahi wa inna ilaihir rajiun” ya fara fada yana maimaita wa hannunsa biyu rike dana Hussain “innalillahi wa inna ilaihir rajiun” sauran mutanen motar suka cigaba da taya shi har suka iso Kaduna suka je gida.
. *** *****
Tun tafiyar su Hussain Aunty take zarya a falo, in ta hau sama sai ta sauko sai ta kuma komawa sama ta kwanta sai ta tashi ta dawo kasa ta zauna. Ta rasa me yake yi mata dadi. Su Zulaihat suna kallo a palo ta kora su daki ta kashe kallon, ji tayi bata son karar tvn, bata son karar komai.
Ta jima a nan sai kuma ta koma sama ta saka hijab dinta ta fita da niyyar shiga part din Hussain ta duba gimbiya Fatima, dama tunda cikinta ya girma kullum sai taje ta dubata. Sai dai a compound din gidan ta hadu da maigadi wanda yayi mata bayanin cewa ai Fatima bata nan yaji Lawan driver yace tace zai kaita Abuja “tare suka tafi da Aunty Ruqayyah”
Wannan yasa a take ta dauko wayarta ta kira Hussain dan taji dalilin da zaisa ya bar Fatima ta bi bayansa da tsohon ciki. Sai dai Hussain din bai dauka ba sai Hassan, ta gaya masa abinda ake ciki sannan ta koma gida ta cigaba da zaman jiran dawowarsu.
Har magrib tayi, sai ta kuma dauko waya ta kira Hassan amma bai dauka ba, ta kira Fatima not reachable Ruqayyah switched off. Ta kira Hussain shima ba’a dauka ba. Hankalin ta yayi dubu ya tashi, ta shiga dakin Khadijah ta tarar da ita a kwance wai zazzaɓi takeyi, ta dafa jikin ta taji zafi sosai, sai ta koma dakinta ta dauko mata magani ta taho da niyyar zata bata sai taga kira daga Bauchi. Babban yayan su Alhaji Lukman, tayi gyaran murya ta dauka tana gaishe shi, sai taji yayi shiru kafin ya amsa sannan yace mata “duk kuna gida tare da yara?” Tace “eh” tana mamakin tambayarsa, sai yace “shikenan ku zauna a gidan gamu nan tahowa komai dare insha Allah” sai ya kashe wayar ya barta da sakakken baki. Me zai zo yayi komai dare? Koma menene a barwa gobe mana?
Ta samu gefen gado ta zauna kusa da kafafuwan Khadijah tana cigaba da kiran number din Hassan da Hussain amma duk babu wanda ya dauka. Ta gaji ta tashi ta daga window tana hangen titi ko zata hango tahowar su amma babu alamar su.
A lokacin ne taji an rusa ihun kuka da muryar Nafisa, taji wani abu ya tsirga mata tun daga kanta har tafin kafarta. Taji wani irin daci a makwogwaron ta. Sai taji sautin kukan Nafisa yayi mata kama da sautin kukanta a lokacin mutuwar Alhaji Aminu uban ƴaƴan ta.
Khadijah da take kwance ta mike da sauri ta tafi dakin Nafisa tana hardewa, a hanya suka hadu da Zulaihat itama tana dosar dakin Nafisa. A dai dai lokacin Aunty taga tsayawar ambulance a kofar gidan. Ta sandare a gurin tana kallo aka bude gate aka shigo da ambulance din sannan akayi packing aka bude baya, taga police sun fito, sannan taga Hassan ya fito amma bata ga Hussain ba sai taga an turo gado da wani abu da yayi kama da gawa akai. Ta saki labulen sannan a hankali ta zame ta zube a gaban tagar.
Hassan yabi gawar Hussain da kallo ya tabbatar an shiga da ita ciki sannan ya juya gurin limamin unguwar su da ya biyo bayan motar rasu. Ashe har sun samu labari sun zauna jira. Hussain mutumin kirki.
Liman yace “dare yayi yanzu, sai dai yayi kwanan keso sai da safe ayi masa sallah” Hassan ya gyada kai kawai. Liman din yace “da assuba zan tura aje makabarta a haka kabari, yanzu kuma zan sika a siyo likkafani, sai asa lokaci saboda yan uwanku su sami sallah” sai Hassan ya girgiza kansa yana kallon garden din gidan, inda tun suna raya suke yin shuke shuke shida Hussain har suyi rigima in wani ya tabata wani yace “anan za’a binne shi, a cikin garden din mu. Nayi masa alkawarin zanke zuwa kabarinsa kullum ina masa addu’a. Anan za’a binne shi a kusa dani”
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kin ganshi a wani gurin na sata ne, in kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana ta WhatsApp through wannan number 08067081020
Sorry about the typos please
Mai sharing littafi, bana ganin ki Amma Allah yana kallon ki kuma na barki da shiHidden Strength
Sumayya yau bata tashi daga school ba sai da akayi kusa kiran sallar magrib. Ta gaji likis saboda yau sun safe suke lectures babu kakkautawa, dan yau sau daya taga Adam shima briefly yazo wai zasuyi sallama zai je Abuja tare da oga Hussain. Tana murmushi tave masa “kwana nawa zakuyi?” Yace “yau zamu dawo” tace “yau zaku dawo din shine harda sallama?” Ya langwabe kai “kika sani ko kawai so nake yi in ganki shine na fake da sallama” ta dan rufe fuska da mayafi, ya kama mayafin yana leka fuskar. Ta rufe idonta “ka bari fa” yace “ni ba zan bari ba, kallon fuskarki ma yanzu na fara” ta kwace mayafinta tana kara rufe fuskar dashi, yayi murmushi yace “kinsan wani abu?” Ta girgiza kai, yace “so nake in mun gama semester din nan inyi wa oga Hussain maganar mu, so nake a fara maganar auren mu tun yanzu ba wai sai mun gam school ba tunda kinga ai ina da aikina kuma ina samun kudi ba laifi, tunda na fara aikin kuma nake tarawa ba wani abin nke yi dashi ba. In nayi masa Magana nasan zai yi min jagora a maganar auren insha Allah”