TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai taji ranta yayi mata dadi, zuciyarta tayi fari tas, yace “kin amince da hakan?” Ta gyada kai tana murmushi, still fuskarta a boye, ita da ace amimcewarta kadai ake bukata da zata iya auren Adam ko da bashi da wannan aikin, koda sadaki kadai zai bayar babu lefe babu komai, thats how much take son shi. Da zasu rabu ya jaddada mata “you know I love you right?” Ta danyi murmushi tana kallon cikin idonsa ta gyada kai, sannan kuma kamar ba zata yi magana ba sai tace “and I love you too”.
Har yanzu, har bayan ta wuni sir a makaranta ta dawo gida a gajiye da yunwa da ƙishirwa amma bata daina jin kaifin kallon da yayi mata a jikinta ba. Tana cin abinci tana zuba murmushi ita kadai, tayi sallah tayi wanka ta fito tama shiryawa Inna Ade ta shigo tana kallon ta. “Ke kuma fa kike ta farin ciki kamar anyi miki albishir da kujerar makka? Au ashe ba kinje, dan haka ba lallai ne ma kiyi farin cikin da kike yi yanzu ba” samayya tayi dariya, “haba Inna, farin ciki ma kuwa ai har marar misaltuwa zanyi in za’a mayar dani in sake ganin Ka’aba. Amma dai duk son da nake yiwa komawar in dai aka bani a yanzu sai dai in baki ko Baba tunda ni na sauke farali” Inna ta zauna a gefen gado tace “to gaya min abind yake saka ki wannan farin ciki haka”Sumayya ta zauna a kusa da inna tana kare mata kallo. Cikin yan shekarun nan da suka dawo gidan nan baba kuma ya samu aiki duk Inna ta chanja, jikinta ya murmure sosai babu wannan muguwar ramar fatarta tayi kyau tayi haske, kyawunta ya sake fitowa sosai. Sai Sumayya tace “kawai dai ina duba rayuwa shine naji raina yayi dadi sosai. Ina duba halin da mutanen da nake tsananin so suke ciki misali ku Iyaye na, Ruqayyah, kannena da sauran su duk kowa yana cikin rayuwa mai kyau sai naji zuciya ta tayi dadi sosai” Inna tace “banji kin lissafa da Adam ba” Sumayya ta sunkuyar da kai, Inna tace “ko shine da sauransu din?” Sai Sumayya ta rufe fuskarta, a dai dai lokacin wayarta tayi kara, ta bude idon ta tana kallon bakuwar number din da bata sani ba sannan ta dauka a hankali tare da sallama “Assalamu alaikum” daga daya barin taji muryar Ruqayyah “Sumayya nice, yar uwarki Ruqayyah ce. Accident muka yi ni da m………. nida Fatima, Allah ya musu rasuwa ita da driver. An tafi dani asibiti ni kuma”
Sumayya ta zaro ido cikin tashin hankali “accident? Mutuwa? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ya kike Ruqayyah me ya same ki ke? Wanne asibitin?” Ta jera mata tambayoyin cikin tashin hankali. Ruqayyah tace “da sauki. Asibitin da nake haihuwa. Ki gaya wa su Inna” sai ta kashe.
Inna Ade da dama tun da taji Maganar accident ta mike tsaye tana kallon Sumayya tace “me ya samu Ruqayyah? Hatsari suka yi?” Sumayya ta gyada mata kai already hawaye yana zuba a idonta tace “hatsari sukayi wai Fatima ta mutu. Allah sarki Fatima. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun” ta fada tana neman hijab dinta. Sannan suka fito palo tare da Inna ita kuma tana nemna waya ta kira Baba ta gaya masa zasu tafi asibiti gurin Ruqayyah, a lokacin ne shi kuma baban suka shigo sun dawo daga masallaci tare da Suleiman. Sulaiman yana goge hawaye, Sumayya tace “kunji labarin kuma ko? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Allah yaji kan Fatima” Baba yace “wacce Fatima ce kuma ta rasu? Mu yanzu ake gaya mana mutuwar yaron nan dan uwan Hassan. Hussain. Yanzu aka kawo gawarsa daga Abuja”
Sumayya ta dora hannu aka Baba ya daga mata hannu, “kar kiyi, ba da haka zaki nuna wa Ubangiji godiyar ki daya baki rai shima ya bashi rai sannan ya ƙaddara saduwar ku a duniya ba” Sumayya ta sauke hannnun tana sheshshekar kuka, Inna Ade tana tayata. Sannan Inna ta gaya musu kiran da Ruqayyah tayi musu da sakon data sanar dasu. Nan take suka shirya gabaki dayan su suka hau Napep din Sulaiman suka tafi asibitin.
Asibitin da aka kai Ruqayyah dana shine asibitin da suke zuwa, dan hka suna zuwa ba tare da wani matsala ba aka karbe ta aka bata taimakon gaggawa kafin karasowar likita. Kafin likitan yazo su Baba sunzo, sun kuma ji dadin yadda suka ganta complete ba tare da ta rasa wani abu na jikinta ba a hatsarin da ita kadai ta fita da rai. Wannan babban abin godiya ga Allah ne. Bayan likitan yazo yayi mata complete check up sai ya fahimci ko karaya bata dashi sai tarkade a hannun ta na hagu wanda ita Ruqayyan ma bata san dashi ba sai kuma ciwon da taji a cinyarta, wanda karfe ne ya soke ta a gurin. Amma problem din shine complain da take yi cewa kafar ta makale, ta kuma fadi cewa farkon data tashi tana iya motsa ta amma yanzu ta kasa. Sai doctor din ya rubuta mata hoto da za’a yi mata a kafar da safe yadda za’a fi ganin komai. Daga nan ya barta aga yanuwanta.
A gurin su ne ta kuma tabbatar da labarin mutuwar Hussain. Ita kuma tana kuka tana basu labarin mutuwar Fatima “tunda na tashi dama na fahimci cewa ta mutu, nayi nayi kokarin in fito da gawarsu daga cikin motar ita da driver amma na kasa, ga wuta kuma ta kama” sai ta rufe fuskarta tana rusa kuka Sumayya tana taya ta. Tace “wuta ta kone su kurmus. Ance ma ba za’a iya dauko gawawwakin su ba sai dai a binne su a can” Sumayya ta share hawayen ta tana tuno kyakykyawar fuskar Fatima, sai kuma ta kara karfin kukanta data tuno da tsohon cikin da Fatima take dauke dashi. Dai kuma Hussain, ta tuno ganinta dashi na karshe sanda taje gidan ta hadu dashi. Cikin barkwanci irin nasa yace “Sumayya kin kuwa san gimbiya ta tsohon ciki ne da ita?” Tayi dariya Tace “na sani mana, na shiga ai mun gaisa” yace “to ki je gida ki fasa bankin ki ki tattara kudaden ki ki sayi lace dan yayi ki kai wa tailor yayi miki dinkin zamani dan suna ne za’a yi shi irin wanda ba’a taba yin irinsa a garin kaduna” sukayi dariya gaba daya. Yanzu gashi babu shi babu matar babu dan. Duniya labari, duniya zancen banza, duk wanda ya dauke ta gurin zama tabbas yana tare da babbar nadama.
Baba ne yace da Inna Ade tazo su tafi gidan mutuwar, Sumayya kuma da Sulaiman su zauna a gurin yar uwarsu a asibiti gobe sa je suyi musu gaisuwa. A gidan mutuwar ne suka tarar da abin mamaki, layin gabadaya a cike yake da mutane maza da mata daga lunguna da sakuna na garin kaduna, wasu a zazzaune wasu a tsatstsaye kowa yana addu’ar samun rahama ga Hussain da iyalinsa saboda Hussain yana da wata al’ada ta kyautata wa duk wanda ya hadu dashi dan yana cewa
“ita haduwa kaddara ce, rabuwa dole ce. Duk mutumin da ka hadu dashi a rayuwa to kayi amfani da wannan damar wajen kyautata masa dan babu tabbas din zaku kuma haduwa, ko baka bashi komai ba kayi masa magana mai dadi, ko baka yi masa magana mai dadi ba kayi masa murmushi dan shima sadaka ne”
Cikin gidan kuwa da Inna ta shiga dakunan duk a bude suke kuma duk da mutane a ciki duk kuwa da cewa yan Gombe basu karaso ba, kowa kuka, musamman ma’aikatan gidan da suke ganin ba zasu kuma samun wani uban gidan kamar Hussain Aminu Abdullahi ba.
Labarin Mutuwar Fatima ya dira tamkar kibiya a zuciyoyin iyayenta, yanuwanta da masoyansa ta. Nan take masarautar kano ta hargitse kowa kukan rashin Fatima musamman da suka ji irin mutiwar da ake tunanin tayi. Wai ko gawar ta ba zasu gani ba, wai ko sun gani din ma ba zasu gane taba saboda ta zama gawayi. Fatimah dai ta su, Fatima da suke ji da Ita tamkar kwai ita ce ta mutu kuma wuta ta kone ta. Wannan wanne irin tashin hankali ne?