TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Mai martaba sarki duk da cewa ya dimauce ya gigice da alhinin mutuwar yar tasa amma duk da haka sai ya hada kan ya’yansa maza gabaki daya suka hau jirgi a daren suka tafi Abuja. Da assuba suka yiwa gawar da suke tunanin ta yar uwar su ce sutura tare da ta driver aka yi musu sallah sannan aka binne su a gurin da suka mutu. Daga nan kuma sai ya juyo ya koma kano dan fara karbar taaziyya daga mutanensa, yayan sa kuma ya tura su Kaduna dan su halarci jana’izar Hussain wadda aka daka karfe goma sha daya na safiyar asabar.

Abinda yake bawa kowa mamaki a gidan gaisuwar shine Hassan. Da kansa yayi wa gawar Hussain wanka ya kuma suturta ta tare da taimakon limamin gidan tun cikin dare. Kallonsa kadai idan kayi ya isa abin tausayi amma zuciyarsa tana tsaye. Yana zaune a gaban gawar yana yi masa addu’a kamar yadda cikin gidan da wajen gidan yake cike da mutane da suke masa addu’a har gari ya waye. A lokacin yan Gombe suka karaso, dangin maman su da dangin babansu. Da gari ya waye ne Hassan ya kira Aunty, wadda duk ta gama fita daga hayyacinta, tare da dukkan yan uwansu mata su biyar yace su zo suyi sallama da Hussain. Kuka suke suna karawa, haka yahada su ya rungume duk a jikinsa in ya share hawayen wannan sai ya share na wannan yana cewa “ku daina masa kuka kuyi masa addu’a, ku ringa cewa innalillahi wa inna ilaihir rajiun zaku ji sanyi a zuciyoyin ku” sai daya kaisu sannan ya dawo ya kama Aunty da kyar ya daga ta ya tafi daita itama. Suka zagaye gawar Hussain suna ta karanta masa suratul ikhlas suna maimaita wa, yadda suke kallon Hussain a kwance a cikin likkafanin sa duk sai sukaji duniyar gaba ki daya ta fita a kansu, suna tuno da sutturu irin na Hussain wanda baya saka kaya idan ba na zamani ba, komai nasa latest ne, in kuwa akayi wani design din to ya daina saka wancan design din. Amma yanzu gashi da brand din kaya irin wanda ake sakawa tun dubunnan shekaru da suka wuce, babu safa ballantana takalmi, babu agogo da sauran kayan adon maza, sai dai in suka kalli fuskarsa sai suji dadi a ransu, yayi kyau irin wanda bai taba yi ba koda kuwa yayi ado da kwalliyar. A hankali suka daina kuka suka cigaba dayi masa addu’a tare da sallamar bankwana, ban kwana na har abada, ban kwana na sai a lahira kuma ba dai a duniya ba dan haduwarsu a duniya ta kare. Sai dai ko bayan sun daina kukan ma in suka tuna da Fatima sai su sake wani, a lokacin babu abinda ba zasu bayar babko da kuwa kawunan sune, babu abinda ba zasu iya yi ba idan za’a dawo musu da Fatima da abinda yake cikinta. Musamman Khadijah wadda tun zuwan Fatima gidan ita ce suka fi shakuwa akan duk sauran, kullum suna tare, tasan irin son da Fatima da Hussain suke yiwa cikin Fatima ta kuma san irin shirin da suke yi na taryar sa, ashe ba mai rayuwa bane ba, ashe ko numfashi bashi da rabon shaka a duniya.

Auncle din su ma da aunties dinsu duk sun shigo sunyi sallama da Hussain, yaron da yayi achieving abinda mutum goma in aka hada ba zasu iya achieving ba. Shi mutum daya ne tamkar dubu. Mutum ne da su kansu sunsan za’a jima a dangi ba’a samu irinsa ba a arziki, alkhairi, kyautata wa da kuma yawan jama’a. Mutuwar Fatima itama ta daga musu hankali ba kadan ba, dan da tana nan da suna saka ran zata haifar musu abinda zasu ke gani suna tunawa da Hussain.

Abokan Hussain, abokan business dinsa da sauran abokan muamalar sa duk sunzo jana’izar sa, a ciki har da Sadiq wanda mutuwa ta riski Hussain a hanyar sada zumunci tsakanin su. Ya koka sosai da mutuwar abokin nasa kuma ya jinjinawa karfin hali irin na Hassan. “Ban san bashi da lafiya ba, bai taba gayamin bashi da lafiya ba. And his family, ohhh dear God. Fatima and His baby! Kullum sai sai ya bani labarin Fatima ta kusa haihuwa. Wannan mutuwar mutuwa ce da ba zamu taba mantawa da ita ba”.

Karfe goma da rabi aka fito da gawar Hussain daga cikin gida, abinda ya saka yanuwansa suka kara rikicewa, Khadijah da Hassana suka zube a kasa. Sha daya dai dai aka yi masa sallah a cikin compound din gidan Aunty, amma mutane sun rufe gabaki daya titin unguwar har da bayan layin da cikin gidajen mutane, kowa yana so ya halarci zanazar Hussain saboda ya taba rayuwarsa in positive way. Dama shi alkhairi haka yake, in ka shuka shi to kuwa zai bika ne tun a duniya kafin ka je lahira, shima kuma sharri haka yake, babu yadda za’a yi ka shuka dawa ka kuma girbi shinkafa.

Hassan da hannunsa tare da taimakon Jabir mijin Safiyya, Saeed mijin Hassana, uncle Mustapha kanin Alhaji Aminu da Baba Amadu yayan su aunty suka saka Hussain a cikin kabarinsa akan barin sa na dama sannan fuskarsa tana kallon gabas, sai kuma aka jejjera itatuwa a saman gawar tasa aka kuma bi da kwababbiyar kasa aka lullube itatuwan tare da like duk gurin da yake da kofa. Sannan aka mayar da kasar da aka fito da ita daga gurin sai kuma aka yayyafa ruwa a saman kasar.

Sai aka durkusa kuma aka yi doguwar addu’a ga ruhin Hussain, masu kuka a hankali nayi nasu dauriyar zuciya nayi har aka shafa sai kowa ya fara kama gabansa. Hassan yana tsugune, tunda ya saka Hussain a cikin ramin ya koma gefe ya tsuguna yake kallonsa har aka rufe shi da itace ta daina ganin sa amma bai dauke idonsa daga inda yake ba, yana kallo aka gama komai aka kuma yi addu’a, ya daga hannunsa, duk da cewa kunnuwan sa basa fahimtar me ake cewa amma yasan addu’a ce akeyi ga Hussain. Yana kallo aka shafa shima ya shafa. Sai kuma yaga mutane sun fara tashi suna tafiya, na kusa dashi kowa in zai tafi sai yazo ya dan dafa shi alamar bada hakuri sannan ya wuce, a haka , a hankali a hankali har kowa ya watse, har aka barshi shi kadai tare da kabarin Hussain.

A hankali yace “Hussain. Amanar da ka bar min ta danka ban sami damar rike ta ba saboda shima ya biyo ka, shi da Fatima, ina fatan zai zamo mai ceto a gare ku damu baki daya” sai ya mike tare da daga kansa ya kalli dogon gidan Hussain wanda tun daga nesa ake hango shi saboda girmansa da kuma kyawunsa, sannan ya sunkuyar da kansa ya kalli kabarin Hussain. Lallai wannan ma wani darasi ne da mutum mai hankali ne kadai zai iya ganewa.

Yana komawa cikin gidan ya karbi gaisuwa daga mutanen da suka taru suna jiran sa, sama sama yake ganesu, sai ya sanar musu da cewa babu zaman makoki kowa ya tafi gida yayi wa Hussain addu’a daga can. Ranar sadakar uku sai azo ayi addu’a a kuma watsewa ranar bakwai ma haka dan baya so yadda mutane suke da yawadin nan a zauna ayi ta zaman hira zaman gulmar mutane, wasu ma har mamacin gulmarsa suke yi a gurin zaman makokin sa. Dan haka sai yaga zaman bashi da wata ma’ana tunda ubangiji yana ko’ina kuma yana amsa addu’a duk daga inda aka yi ta.

A haka ya lallaba ya shiga cikin gida, inda ya tarar fa labarin wai an tafi da Aunty asibiti saboda jininta ya hau sosai. Shi bai san Aunty tana da hawan jini ba sai dai in yanzu ta samu. Ya tuna Ruqayyah, tun da akayi accident din ma bai ganta ba yaji dai ance tana asibiti amma ko waya bai samu yayi mata ba. Ba zai iya zama ba dan yana son ganin jikin Aunty dana Ruqayyah sai dai kuma mutane ta ko’ina tahowa ake yi zuwa yi musu gaisuwa musamman wadanda basu samu janaza ba, kuma kowa yazo shi yake nema tunda duk auncles din su da cousins dinsu ba’a san su ba sai few wadanda suke aiki a kamfanin su. Dan haka dole ya dan zauna sama sama yana amsa adduar mutane har lokacin sallar azahar yayi suka tashi sukayi jam’i aka sake doguwar addu’a ga Hussain da iyalinsa sannan aka gaya masa cewa an dawo da Aunty daga asibiti, sai yace a kaita part dinsa inda babu hayaniya dan ta samu ta huta sosai. Shima kuma ya samu ya zare jiki ya tafi, yana tafiya kamar iska zata kayar da shi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button