TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Yana shiga twins dinsa suka taho da gudu suka rungume shi. Ya durkusa a gabansu yana jawo su jikinsa tana jin wani iri a ransa, kamar yayi neglecting dinsu gashi uwarsu tana asibiti an barsu a gurin yan aiki. Shima kansa Hussain junior yana gurin mai reno tun jiya. Suna ta tsallen murnar ganinshi, sai kuma suka fara leka bayansa suna “ancol, ancol” ya runtse idonsa dan ya gane auncle din su suke nema. Sai ya rungume su yana maimaita “auncle is no longer with us, he is gone and he is never coming back” yayi ta fada yana maimaita wa a hankali duk da yasan ba fahimtar sa suke yi ba amma kamar kansa yake tunawa, kansa yake consoling.
A lokacin Sumayya ta shigo, ta taho daga asibiti zata daukar wa Ruqayyah abubuwan bukata. Ta tsaya tana kallon su tana jin abinda yake cewa, sai taji matuƙar tausayin Hassan ya kama shi, Allah ne kadai yasan abinda yake ji a zuciyarsa a yanzu, kuma ta jinjinawa jarimtarsa sosai da sosai dan duk da bata san me yake ji ba bata tunanin zata iya surviving irin situation dinsa, ita tana da uwa tana da uba tana da twin sister dinta, tasan kuma duk yadda take ji dasu a zuciyarta so she can’t imagine ace duk bata dasu, her life will have no meaning. But menene meaning din rayuwar ma? Dama ai Allah ya halicce mune with the sole purpose of worshipping Him dan haka duk wani abu da muke yi secondary purpose ne, worshipping din shine primary purpose din mu amma munyi neglecting munfi mayar da hankali akan abinda ba zai amfane mu ba.
Ta karasa shiga ta zauna akan kujera tana kallonsa, idonsa yana rufe, hawaye yana bin kumatunsa, bakinsa yana motsi a hankali yana ta maimaita maganganu daya. Ta hadiye abinda yake tsaye a makogwaronta, itama jiya yadda taga rana haka taga dare saboda abubuwa da yawa, na farko alhinin abubuwan da suka faru, na biyu irin yadda Ruqayyah ta ringa zabura tana sambatu, tunda take da Ruqayyah bata taba ganin tsoro a fuskarta ba sai jiya, kuma bata yi mamaki ba dan tabbas wanda yaga irin abinda Ruqayyah ta gani zai iya zaucewa ma ba sambatu ba, har sai da aka yi mata allurar bacci sannan ta samu ta rintsa, shima kuma tana yi tana firgita dan haka ita Sumayya ta zauna tayi da yi mata adduoi tana tofa mata.
Abu na biyu kuma shine Adam, tunda labarin mutuwar Hussain da Fatima ta same ta take kiran number dinsa wai dan ta samu tayi consoling dinsa dan tasan matsayin Hussain a gurinsa amma ta kasa samun sa, farko wayar tana ta ringing ba’a dauka daga baya ma kuma bama ta shiga, sai ta dauka rudewa ce ta saka yayi misplacing wayar tasa. Amma har gari ya waye shiru, har akayi janaza shiru, ba su Baba suka je asibitin ma sai data cire kunyar idonta ta tambayesu ko sunga Adam amma suka ce basu ganshi ba, sai dai babu wanda ya dauki abin da wani abu saboda irin yadda mutane suka cika a gurin dan baka ga wani ba ba zaka ce baya gurin ba. Yanzu ma da tazo gidan baza ido tayi tayi tana son ganinsa amma babu ko takalmin sa. Mai gadin gidan su Ruqayyah ta tambaya amma sai ya amsa mata da cewa “anya kuwa Adam ya kwana a gidan nan? Tun jira da suka fita tare da marigayi ban kuma ganinsa ba, motar daya tafi da ita ma bata dawo gidan nan ba” ya fada yana kara duba inda tarin motocin Hussain suke.
Wannan ya kara daga hankalin ta, me ya faru da Adam? Yana ina? Lafiya kalau yake?
Tana shigowa cikin gidan kuma sai ta tarar da wannan tashin hankalin. Dan halin da taga Hassan a ciki ya taba zuciyarta sosai. A hankali ta kira sunan sa “Yaya Hassan” ya dago kansa yana kallon ta da jajayen idanuwan sa. Tace “Allah yana nan. Yana kallon halin da kake ciki kuma yasan zaka iya daukan wannan kaddarar shi yasa ya dora maka ita. Allah baya taba dora wa bawansa abinda ba zai iya ba. Nasan kayi babban rashi wanda ni ba ma zan iya kwatanta yadda kake ji a zuciyarka ba. Amma ina so in tuna maka wani abu, kalli nan…” Ta fada tana numa masa yaran da suke gabansa. Ya kalle su sannan ya kuma kallonta, tayi masa murmushi tace “su wadannan yaran misali ne na irin Blessings din ubangiji gare ka. A duk lokacin da ka rasa wani abu da kake so kar ka kalli irin girman rashin da kayi but ka kalli irin abubuwan da kake dasu. Always count your blessings not your losses, a lokacin zaka san how blessed you are. You have a hidden Strength wanda kai kanka baka san kana dashi ba sai yanzu da wannan abin ya same mu sannan zakayi finding dinsa, kai kanka sai kayi mamakin what you can do alone in kayi concentrating on your blessings. Ka kuma godewa Allah da niimar sa. A lokacin shi kuma zai cigaba da tallafa maka”.
Ya dauke kansa daga kanta ya kuma kallon yaran da suke ta jan rigarsa suna masa gwaranci sai ya samu kansa da yin murmushi, yana goge hawayen idonsa yace “Nagode Sumayya, nagode da kulawarki gare ne. Nagode da kika bude min idona naga haske” sai ya mike yana daukan yaransa ya tafi dakin da ya ke tunanin an kai Aunty can. Ya samu tana bacci sai Khadijah a tare da ita tana karatun Alkur’ani. Ya karbi bayanin da likita ya rubuta ya karanta sannan ya kuma daukan yaran ya fita dasu kar su dame ta.
Yana fitowa Sumayya tana saukowa daga sama da karamar jaka a hannun ta, ta karbi Yusuf tace “kawo su in tafi dasu can, sai Inna ta tai dasu gida su zauna acan. Dama dazu na aiko Zunnur ya karbi Hussain ya tafi dashi dan tun jiya bai sha nono ba” ya dafe kansa yana tunanin kamar ya gaza, tunda har ya manta cewa Hussain yana bukatar uwarsa. Sai yace mata ta jira shi ya dauko key din mota su tafi tare ya gano Ruqayyan. Ta jira shi ya hau sama ya sauko sannan suka fita tare, ita da Yusuf a hannunta shi kuma da Aminu suka je gurin mota suka saka yaran a baya sannan suka shiga gaba suka fita. Sai da suka dauki hanya sannan yace mata “ya jikin nata? Akwai wani major ciwo ne?” Ta girgiza kanta tace “Babu. Kafa ce kawai ta rike ta kasa motsa ta har yanzu, anyi hoto ance jijiya ce ta tabu, in an jima zasu sake wani hoton dan suga exactly inda ta tabun” tayi shiru tana kallon gabanta sannan tace “sai kuma tsorata” ya gyada kansa cikin fahimta, a ransa yana jin dadin yadda bata samu babbar matsala ba, yace “dole akwai tsorata dama, dan ma dai Ruqayyah ce” ta gyada kanta itama tace “dan ma itace. Da ni ce da sai na samu mental problem or worst” ya kalleta yace “yanzu kike min magana akan inner strength, da ke ce you will find out that you are stronger than you think”.
Wannan littafin na siyarwa ne, in kika ganshi a wani gurin na sata ne, idan kina son ki karanta halaliyar ki ki yi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020A Lost Soul
A zaune suka tarar da Ruqayyah akan gado tana shan tea, Inna Ade tana zaune akan kujerar gaban gadon da Hussain a hannunta tana fada “in baki samu kin sha tea din ba yaron nan ba zai samu abincin sa ba fa shima. Ki daure ko rabi ne ki sha, ai yayi kokari ma” sallamar su ta saka Inna dago kai tana kallon su, Ruqayyah ma haka. Kallo daya ta yiwa Hassan ta sunkuyar da kanta kasa, ji tayi ta kasa hada ido da shi, wani irin nauyi take ji a zuciyarta in ta kalle shi. Musamman da taga irin yadda ya koma a cikin kwana daya. Shima a nasa bangaren kallon baki da ramar da tayi a cikin kwana daya yake yi, tayi zuru zuru idanunta duk firfito waje. Ya dan durkusa yana gaishe da Inna ta amsa masa cikin muryar tausayi tana kara yi masa gaisuwa “ya karin hakuri? Ohh Allah. Insha Allah Hussain da Fatima suna aljanna, kowa yana yi musu kyakykyawan zato kaji? Allah kai kuma ya kara maka hakuri tare damu baki ɗaya dan rashin na kowa da kowa ne” kansa a kasa yace “ameen Inna. Nagode.” Yana jin wave din zafin mutuwar Hussain tana kara dukansa, haka yake ji duk sanda wani yayi masa gaisuwa, kuma yasan haka zai cigaba da ji har ranar da shima zai daina numfashi.