TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta mike ta fita daga dakin, Sumayya ma ta ajiye kayan hannunta ta kuma ajiye yan biyun da suke ta zillo sunga uwarsu. Sannan ta fita itama. Ya jawo kujerar da Inna ta tashi daga kai ya zaune yana kallon yadda kirjin Ruqayyah yake hawa da sauka kamar wadda tayi gudu ko kuma take cikin jin tsoro. Sai ya kamo hannunta guda daya a cikin nasa biyu ya rike yana cewa “it is okay Hassana. You are safe kinji? Kina tare da mu yanzu, babu abinda zai same ki kuma. It is over” ta gyada kai hawaye yana zuba daga idon ta, sai ya hau kan gadon sosai ya jawo ta jikinsa ya rungume ta yana dan jijjiga ta kadan. Ta zagaye shi da hannayenta tana cigaba da kukan ta. “sun mutu Hassan sun mutu, gaba dayan su sun mutu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun” ya kara rungume ta a jikinsa yana jin tsananin tausayin ta, what she went through, what she witnessed, yana jin rayuwarta ba zata taba komawa dai dai ba kamar yadda yasan ta sa rayuwar ba zata koma dai dai ba. Ta dago kai tana kallon sa, “na dauka mutuwa zanyi mijina, na dauka ba zan kara ganin ka ba mijina” ya saka hannu yana goge mata hawayenta “am here, ina nan tare da ke babu abinda zai same ki insha Allah” sai ta juya tana kallon kafar tace “kafata ce take ciwo mijina, na kasa motsa ta, tsoro nake ji kar in zama gurguwa” ya girgiza kansa “uhm uhm ki daina fada, babu abinda zai samu kafar ki kinji? Me Doctor din yace?” Ta nuna masa takardar da likitan ya kawo ta hoton da yayi wa kafar dazu da safe tace “yayi hoto, yayi bayani no ban gane me yace ba. Ni tsoro nake ji kar in rasa kafata. Bana so in zama gurguwa Hassan” ya dauki takardar yana dubawa sannan yace “yace zasu yi wani hoton ai ko? Ki daina kuka please mu bari su sake yin wani hoton mu gani kinji? Sun san abinda suke yi duk abinda ya kamata suyi akan kafar zasuyi” ta rike hannunsa tana girgiza kai “ni dai kawai ka fitar dani waje, ai kuna da doctors masu kyau a waje wadanda zasu kyara min kafata a lokaci daya. Ka fitar dani kawai waje tun kafin lokaci ya kure suce an makara” yayi ajjiyar zuciya yana jin kansa yana fara ciwo, ya kamo fuskarta a cikin hannunsa yace “Hassana. Hussain ne ya mutu, shi da Fatima da babyn su gaba ki daya. Jiya suka mutu, yau aka binne su. Hassana ba zan iya daukan ki mu fita kasar waje yanzu yanzu ba, gidan ma yanzu dan ina son in ganki ne kawai yasa na yi karfin zuciya na fito na taho nan, amma ba zan iya barin garin nan ba ballantana kasar nan. Kiyi hakuri. Wannan likitan is the best a garin nan, in mun fita wajen ma irin sa zamu gani ko kuma ma wanda bai kai shi kwarewa ba, matsalar kayan aiki ne, idan yaga cewa kina bukatar kayan aikin da basu dashi a nan shi da kansa zai fada kuma yayi referring dinki zuwa kasa da kuma asibitin da yasan suna da kayan aikin da kike bukata” a karasa yana jin babu dadi dan ba zai iya yi mata abinda take so ba, amma wani barin na zuciyarsa yana ganin bai dace ba tambayar tasa ma da tayi bayan tasan halin da yake ciki, amma considering halin da ita din take ciki sai ayi sauri ya kawar da batun daga zuriyar sa. Yayi ta rarrashin ta har ta daina kukan sannan yayi kokarin kara mata kwarin guiwa, ya kuma yi mata bayanin abinda yasa ba zai zauna tare da ita a asibiti ba tunda ya bar mutane masu zuwa gaisuwaa waje.

Da kyar ta cika shi, ita tana ganin bai kyauta mata ba da ba zai fita da ita waje ya nema mata magani ba ko kuma ya zauna yayi jinyarta ba, bayan kuma a ganinta a yanzu babu wanda ya kaita muhimmanci a gurinsa tunda dai Hussain din da yake ta ambato to yanzu babu shi. Ta kara jin dadin hukuncin da ta yanke akan dan Hussain dan tasan da yana nan da bata jin ko kallo ita da ƴaƴan ta zasu ke samu daga gurin Hassan da yanzu yana can yaa rainon sa. Dan haka sanda zai tafi ma fushi ta nuna tana yi, wannan ya kara masa rashin jin dadi a zuciyarsa amma kuma a hakan dole yayi mata sallama ya kuma yi sallama da ya’yan sa ya fito. Sumayya ta biyo shi a baya, taa ta so ta tambayeshi Adam amma kuma tana ganin kamar hakan ba dai dai bane ba considering halin da yake ciki. Har sai da yaje bakin mota zai tayar sannan ta daure tace “Adam acan Abuja kuka bar shi ne?” Sai da yayi blinking idonsa sannan ya juyo yana kallon ta, tabbas bai ga Adam ba, tunda ya dawo bai ga Adam ba kuma bai tuna da neme shi ba.

Ya dafe kansa da hannu daya yace “noo, ba acan muka baro shi ba. In fact, ya riga ni tahowa ma, shi yayo gaba neman motar su Ruqayyah ni kuma na tsaya na taho da Hussain. Kin neme shi a waya?” Idonta ya kawo kwalla, tace “nayi ta kiransa tun jiya wayar tana shiga baya dauka, daga baya kuma bata shiga sam, yanzu ma kafin ka fito sai dana kira amma switch off” yace “kar ki damu, am sure mutane ne da kuma alhinin wannan abin ya hana shi dauka. Amma in naje gida I will get him to call you” ta goge hawayen ta tace “baya gidan, bai koma gida ba, bai dawo daga Abuja ba” yayi shiru yana kallonta bai ce komai ba, tace “dazu da naje gidan na tambaya duk babu wanda ya ganshi. Mai gadi ma yace bai shigo gidan ba, yace motar da kuka fita da ita ma bata dawo gidan ba”. Sai Hassan ya rasa me zaice mata, yaji hankalin sa yana tashi amma sai yayi karfin hali yace mata “am sure yana wani gurin ne, ko school ya tafi ya kwana acan kinsan tunda gidan da mutane ba zai ji dadin zama ba” ta girgiza kanta again tace “na kira abokin sa na makaranta baya can, sunce suma nemansa suke yi they were supposed to meet yau da safe suyi karatu” yanzu hankalin sa ya kuma tashi, but baya so ya nuna mata yace “still, think positive Sumayya, yana da abokai a cikin gari wata kila yana tare dasu ne. Shima nasan wannan mutuwar ta taba shi, maybe he just needed space ne ya danyi cooling down” ta gyada kai da sauri trying to believe him, hoping abinda ya fada shine abinda ya faru din. Sannan taja baya shi kuma ya tayarda motar ya tafi.

Amma shi zuciyarsa duk ta tsinke, me ya faru da Adam? Babu wanda ya ganshi, shi kuma yasan babu yadda za’a yi Adam yayi missing jana’izar Hussain in dai har yana da rai yana kuma da lafiya, sannan kuma zai kira Sumayya yagaya mata lafiya kalau yake, dan haka shi kansa bai yadda da abinda ya gaya wa Sumayya na cewa yana wani guri ba.

Yana zuwa gida mai gadi ya sake tambaya, ya kuma maimaita masa abinda ya gaya wa Sumayya, sai ya duba gurin motoci da kansa ya tabbatar babu motar da suka tafi da ita Abuja, daga nan ya tafi part din da Adam yake kwana tare da sauran yaran gidan ya tambaye su duk duka ce basu ganshi ba. “Kuma wayarsa bata shiga” wani daga cikin su ya kara jaddada masa. Sanda ya bar part din kansa har juyawa yake yi yana jin jiri, abubuwa sunyi masa yawa, ga mutane duk inda yayi kowa yanaso yayi masa gaisuwa kowa yana so yayi masa magana. Haka ya samu ya dan zauna kadan a cikin mutanen da suke jiransa sannan ya tashi ya shiga gidan sa yana jin kansa yana tsananin sarawa. Menene yake faruwa a rayuwarsa? Hussain, Fatima and now Adam? Me ya samu Adam? Ko shima yayi accident ne a mota kuma babu wanda ya ganshi? Dan suma su Ruqayyah dan ita ta rayu ne ta nemi taimako ba dan haka ba da zasu iya kwana daya ko biyu ma ba tare da an san inda gawawwakin su suke ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button