TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya dauko wayar Hussain wadda da ita yake amfani yanzu ya kira number din Jabir. “Please ka sa a binciko motar da muka tafi da ita Abuja jiya, I will send you the plate number din yanzu” Jabir yace “lafiya? Ta bata ne?” Hassan yace “ba ta motar nake ba, ta yaron da yake cikin motar nake”.

Har dare babu labari, har gari ya waye babu labarin Adam. A lokacin hankalin Sumayya ya kai makura gurin tashi, ta gaya wa inna halin da ake ciki ita kuma ta gayawa Baba wadanda a take suka fara addu’ar Allah ya bayyana shi. Suna cikin jajantawa da kuma tunanin zuwa suyi reporting gurin police Hassan ya shigo dakin asibitin. Ya gaishe su yana kallon Ruqayyah da take bacci dan jiya ma sam bata samu baccin kirki ba. Baba yace “Hassan da kokari da kayi zamanka ai” ya danyi murmushi kadan, sai ya kalli Sumayya yace “bai kira ba?” Ta gyada kanta kawai tana kallon wayar hannunta dan number dinsa cewa akai tana dialing, kamar jan charbi ta mayar da kiran number dinsa daga jiya zuwa yau. Baba yayi musu sallama ya fita sai Inna tabi bayansa. Ya zauna akan kujera yana kallon Sumayya yace “za’a ganshi insha Allah kinji?” Ta gyada kai tana kokarin mayar da hawayen idonta. Allah kadai yasan yadda take ji a zuciyarta, sai yanzu ta san zafin batan mutum da ake cewa gwara kaga gawarsa a gabankaakan ace ya bata baka san halin da yake ciki ba. Tun jiya babu abinda take yi sai sake sake na irin halayen da yake ciki, maybe yayi accident ya mutu babu wanda ya ganshi, maybe masu garkuwa da mutane ne suka kama shi yana hannunsu, maybe yana can yana neman taimako kuma babu wanda zai taimaka masa. Ta fara hawaye, Hassan ya jingina da jikin kujera yana kallon ta. “Ki daina kuka fa, zai dawo gurinki indai yana raye I promise you this kinji?” Ta gyada kai amma hawayenta yaki tsayawa, she just can’t get it through her head cewa Adam ya bata, ya za’a yi ya bata kamar wani thing ba mutum ba?

A lokacin Ruqayyah ta bude ido, ashe tun shigowar Hassan idonta biyu ta rufe idon ne tana jin abinda suke cewa, ta yi kokarin mikewa zaune, Hassan yayi saurin taimaka mata yana yi mata sannu ta zauna tana kallonsa tace “Adam din Finally ya tafi kenan” yace “me kike nufi Finally ya tafi?” Ta danyi murmushi tace “wai da kun dauka zama zaiyi? Me naji kna cewa? A gabasa fa Hussain ya mutu kuma ka bashi mota kace ya taho Abuja, yanzu wannan motar idan ya siyar da ita ba yayi arziki ba, ai kawai ku fitar da ran ganinsa kawai na san ya debi rabon sa ne ya kara gaba” ran Sumayya ya baci, ta taso kan Ruqayyah da sauri “kar ki kara! Kar ki kuma alakan ta shi da sata ko cin amana, ba halinsa bane ba, motar banza motar wofi, ana tunanin ima mutum yake kuma wanne hali yake ciki ke kina zancen mota? Wacce irin zuciya ce a kirjinki Ruqayyah?” Hassan ya dafe kansa yana jin kamar zai tsage, sai Sumayya ta ja da baya tana jin babu dadi tayi masa hayaniya aka Sannan ta juya ta bar dakin da sauri tana hawaye, a ranta kuma tana Allah wadai da halin Ruqayyah da har after all what happened zata iya fadar abinda ita kanta tasan karya ne akan wani, wanin ma kuma wanda ake tsammanin yana cikin matsala.

Bayan tafita Ruqayyah ta bi ta da kallo sannan ta dawo da dubanta kan Hassan tace “kayi hakuri da halin Sumayya, tana da problem musamman in akaxmce akan wannan stupid yaron ne, ga gaskiya kiri kiri amma ba zata ganta ba, yaron nan ya saci mota ya gudu, period” Hassan ya girgiza kai yace “you are wrong Hassana, bana jin gudu wa yayi, you need to see yadda hankalin sa ya tashi a lokacin da Hussain ya rasu, he gave me support and a shoulder to cry on. Da yana son ya saci mota da tun da yake gidan zai sata, keys din Hussain duk suna hannunsa ko ni lokuta da dama a gurinsa nake karbar key din wasu motocin, in yana son ya dauki mota ya gudu da tuni ya dauka ya gudun” Ruqayyah tace “to ai lokacin yasan mai motocin yana da rai, yanzu kuwa yana ganin sun zama kayan gado shi yasa zai kwashi rabonsa” yayi shiru yana kallonta kawai yana lura da yadda ta ambaci gadon. It never occurred to him cewa kayan Hussain sun zama na gado ba, shi komai na Hussain ne a gurinsa duk kuwa da xewa tun kafin Hussain ya bar duniya ya mallaka masa rabin duk abinda ya Mallaka. Sai kawai ya girgiza kansa a ransa yan aiyana rigimar da zasuyi da Ruqayyah duk sanda ya gaya mata kudurin da ya yanke a zuciyarsa na abinda zaiyi da duk abinda Hussain ya bari. But he has already made up his mind tun kafin Hussain din ya bar duniya.

Yau ma sai da ta sake yi masa maganar fita waje, ya kira Doctor din yazo a gabanta suka yi magana yayi masa bayanin problem din da yake tunanin ya samu kafar da kuma solution din daya yanke. “jijiyar ce ta rike ba wani abu ba. We can treat her here, duk abinda za’a mata a waje zamu yi mata anan ma in dai har ta bamu dama” Hassan yace “babu problem, just do your best but in kunga akwai problem sai ku fada da wuri dan musan abin yi. Kana ganin zat warke ai ko?” Doctor din yayi murmushi yace “ras kuwa. In no time zata cigaba da amfani da ƙafafuwan ta. Garin accident din ne kashi ya bude a hips dinta sai jijiya ta shiga ciki, wannan yasa ta zata ita motsa kafar voluntarily ba sai dai in ta saka hannu ta motsa ta. Manually zamu fito da jijiyar daga cikin kashin sai mu daura mata belt a gurin mu barta tayi healing shikenan” Hassan y gyada kai cikin gamsuwa yace “shikenan Doctor” Ruqayyah kuma sai tace “amma Doctor ba tunda akayi accident din bane ba ta rike, nayi amfani da ita sai daga baya ta rike” Hassan yace “kinyi amfani da ita? Ina kika je?” Ta dauke kanta tana kallon gefe tace “na…. Ammmm naje nayi……na dan zagaya ina neman network zan kira ka” ya kalli Doctor din yace “to kaji, she used the leg after the accident” doctor yace “I can’t say me ya faru gaskiya, it maybe sanda take tafiya ne, ko kuma wannan ciwon da taji, but hoton mu bai nuna mana komai a keg din ba shi yasa mukayi tunanin daga hip bone be, but zamu sake dubawa”.

Doctor din yana fita ta fara mita “kaji ko? Basu ma sani ba, basu ma san aikin su ba. Wannan mutanen babu abinda zasu iya yi min, idan kai ba zaka iya hakura da abinda kake yi ba ka taho mu tafi ba ni ka barni in tafi ni kadai” ya mike yana kallon ta, baya son ta kara masa wani tension din akan wanda yake ciki already yace “in zuwa karshen satin nan basu tsayar da matsaya ba zan nemi Doctor din da zai duba ki a waje sai ku tafi tare da Sumayya” tayi murmushi tana bayyana jin dadin ta tace “yauwa. Ko kaifa. Allah ya kaimu” ya juya ya fita yana lura da yadda bata ce masa a dawo lafiya ba, sai kuma ya tuna cewa har yanzu bata yi masa gaisuwar Hussain ba ballantana ta Fatima.

Ranar sadakar uku gidan gaisuwar ya cika har ma yafi ranar da akayi jana’iza cika. Dan yan uwan Fatima ma duk anan suka zo aka hada akayi musu addu’a tare, sannan aka fito da dukiya akayi ta bayarwa sadaka da niyyar Allah ya kai ladan kabarin Hussain da iyalinsa. A ranar saida Hassan ya karar da kudin da yaje cikin account din Hussain kaf, amma yayi noticing amount din dan yasan ba shi kadai ne yake da gadon Hussain ba. Kuma sadakar da yayi irin wadda yasan Hussain yana yi ce da Hussain ya kan ce

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button