TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Bayan sun hau kan titi sosai ne katon wanda yake gaba yace cikin budaddiyar murya “ina dan uwan nasa yake?” Wanda yake zaune a baya yace “yayi tafiya, ina jin ma ƙasar ya bari” mai tuka motar yace “what? To a gurin uban wa zamu karbi kudin tunda baya nan? Tunda kasan bayanan ba sai ka gaya mana ba mu bari sai ya dawo sannan mu dauki wannan ɗin? Yanzu anything can happen kafin ya dawo din, kuma bamu da number din da zamu same shi a can ɗin” na bayan ya gyara zamansa yana murmushi yace “kun san kuwa yadda yake son dan uwan nan nasa? Da zai san mun dauki dan uwansa a yanzu, da zai iya biyan ko nawa ne dan jirgin da yake ciki ya juyo ya dawo dashi Nigeria” ya karasa maganar yana dariya, na gaban duk babu wanda ya taya shi dariyar har ya gama sannan katon yace “to yanzu ta yaya zamu gaya masa mun dauki wannan ɗin” na bayan yace “Hassan ba zai rasa wayar sa a jikinsa ba, Hussain yana sauka wanda zai fara kira ya gaya wa ya sauka shine Hassan, mu kuma sai mu dauki wayar…..ina tabbatar muku da cewa next jirgin da zai dawo Nigeria da Hussain a cikin sa” ya sake yin wata dariyar “nasan mutanen nan kamar yadda nasan tafin hannuna”.
Babu wanda ya kula shi a na gaban amma kuma duk sun yarda da abinda yace, a hankali suke tafiya da motar da normal speed dan gudun jan hankalin mutane zuwa gare su, har suka yi nisa sannan suka sauka daga titi suka fara shiga cikin unguwa, unguwar rimi, suka ringa wuce gida je har suka zo wani incomplete gida, suka shigar da motar cikin kofar da ba’a saka wa gate ba suka yi packing, na bayan motar ne ya fita ya tsaya yana yi musu gadi su kuma biyun suka bude booth suka fito da Hassan suka shiga dashi cikin gidan zuwa wani daki sannan suka bude kofar bandakin da suka riga suka yiwa aiki suka saka mata lock suka jefar dashi akan simintin toilet din, sannan suka dauko igiyar su da suka riga suka tanada suka daure masa hannayensa a bayansa suka kuma hada ƙafafuwan sa guri daya suma suka daure sannan suka dauko masking tape suka nannade masa bakin sa. Sai da suka gama sannan suka lalube jikinsa sula cire wayoyinsa da ID cards dinsa da duk abinda yake jikinsa, suka dauke shi hoto da wayarsa sannan suka fita suka rufe kofar dakin da key.
Suna fita katon ya jefa wa wanda ya zauna a bayan motar key din motar yace masa “discard the car, kafin safiya nasan police zasu fara neman ta”.
************************************
Washegari Saturday, babu school, dan haka kamar yadda yake alada a gidan Inna Ade tunda suka tashi sukayi sallar asuba sai suka zauna suna tilawar karatun Alqur’ani har gari ya waye, sannan suka fara ayyukan gida. Yammatan suna gyaran gidan wanda kusan kullum kalkal yake cikin tsafta, ita kuma inna Ade ta hada wuta ta dora musu dumamen tuwo ta kuma kunu. Tana saukewa kuma ta dora musu ruwan wanka. A lokacin ne Baba ya fito daga daki da radiyo a hannunsa, Sumayya ta shimfida masa tabarma ta saka masa pillow ya zauna, duk suka gaishe shi. A lokacin samarin suma suka shigo duk suka gaishe shi ya amsa.
Inna Ade tace “Baban biyu yau ba zaka fita bane ba? Naga ka dauko radiyo” yace “zan fita, labarai dai nake so inji ko zanji sanarwar sunayen wadanda aka dauka aikin nan da muka je nema jiya” Sumayya tayi dariya tace “Baba jiya fa kuka yi interview din, daga jiya zuwa yau har a sanar da wadanda suka ci?” Yace “ahau, ba aikin kamfani bane ba, ai su basu da bata lokaci sha yanzu ne magani yanzu ba kamar aikin gwamnati ba da za’a yi ta fama kamar cin kwan makauniya. Su kuwa wadannan tunda sunyi mana intabiyu shikenan” yaran duk suka kwashe da dariyar yadda yayi pronouncing interview din, yayi musu dakuwa yace “ku ungo ku raba, ni kuke wa dariya” Ruqayyah tace “Baba interview ake cewa ba intabiyu ba” yace “ko ma inta uku ne ku kuka sani,ni dai abinda na sani shine a bani aiki kawai, kunga inna samu aikin gadin nan sai innar ku take yi min abin siyarwa ina tafiya dashi ina siyar mata a bakin gate” Zunnur yace “baba ni zan taya ka dauka” Baba yace “makarantar kuma fa?” Sumayya tace “Baba ni zan daukar maka tunda kaga mu mun kusa gamawa, kafin ka fara aikin mun gama sai in ke kai maka” yayi murmushi yace “Husaina in dai har ina da rai kuma ina da lafiya ai ba zaki yi talla ba. Har kar neman kudin da zaki yi idan ba sana’a a gidan mijinki ba to sai dai aikin office” Inna Ade tace “allahumma ameen Baban biyu, Allah ya nuna mana wannan rana ya Allah” yace “ameen. Kinga yaron da yayi mana intabiyu din nan, wallahi ya burge ni sosai yaron nan, sai naji ya kwanta min a rai ina kallon sa nace Allah ameen, Allah ka muna min Suleiman dina watarana kamar haka. Dan saurayi dashi fa wai amma shine mai gurin gabaki daya” Suleiman yace “Baba ba H & H ba? Ai yanzu su suke tashen kudi a garin nan, wannan kamfanin da za’a bude na goma kenan fa kuma ance ogan ko aure bai yi ba” Ruqayyah tace “kai Suleiman banda kari, yanzu har sunyi goma?” Sai kuma ta langwabe kai gefe tace “sunji dadin su, wasu mutanen da sa’ar su suke zuwa duniya” Baba yana kallonta yace “Hassana ni banji kin ce zaki tayani daukan kayan abinci mu siyar a bakin gate ba” ta sunkuyar da kanta tana zuba kunu a cup tace “Baba in nace ma cewa zakayi a’a shi yasa ban ce ba” ya dauke kansa yana maida hankalinsa kan tuwon da Inna Ade ta ajiye masa a gabansa yace “insha Allahu ina samun aikin nan zan fara tara kudin da zan biya muku kudin jami’a. Insha Allahu ba zan kasa biya muku ba kamar yadda na kasa biya muku kudin wannan jarabawar”.
Kasa kasa Ruqayyah tace “hmmm. Allah yasa. Necon ma dam gwamnati ce take biya da cewa za’a yi ita ma mu hakura babu kudi” Inna Ade tace “me kike cewa ne Ruqayyah?” Ta dago kai tace “cewa nayi Allah yasa, Allah yayi jagora” duk suka amsa da ameen.
A bangaren su Aunty kuwa da safe, Aunty ta sauko daga samanta idanun ta akan dining table tana lura da cewa ba’a taba abincin gurin ba, tasan kuma Hassan kullum shine na farkon tashi a gidan dan kusan kullum akan dining take samunsa. Ta karaso tana bude warmers din taga babu alamar an taba abincin. Ta ja kujera tana kwalla wa Safiyyah kira amma maimakon taji ta amsa daga san su sai taji ta tana amsawa daga bakin kofa, da alama daga waje take, Aunty tabi fuskarta da kallo har tazo ta zauna a kusa da ita tace “wai har yanzu baki samu number din Hassan ba?” Safiyyah ta ce “ban samu ba Aunty. Da daddare wayar tana shiga amma yanzu da safe a kashe take” Aunty tace “je ki duba mim dakinsa, tashi da sauri” Safiyyah bata motsa ba fuskarta kamar zata yi kuka tace “daga can nake aunty. Yaya Hassan bai kwana a gidan nan ba, motar daya fita da ita ma bata nan. Tun daya fita kafin magriba mai gadi yace bai dawo ba”.
Aunty tayi shiru tana kallon gefe daya, sannan kuma sai tayi saurin dauko wayarta tana kiran Hassan, switch off taji, ta katse kiran ta ajiye wayar tana jin yunwar data sauko da ita tana guduwa tana barinta. “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun” ta ringa fada tana maimaita wa “ina yaron nan ya tafi? A ina ya kwana?” Tunda take da Hassan bai taba kwana ba’a gida basao lokacin da yana makaranta kuma shima dan a hostel ya zauna. Ta juya tana kallon Safiyyah wadda idanunta suka cicciko da kwalla tace mata “maza ki kirawo min Jabir” Jabir shine babban abokin Hassan wanda kuma za’a iya cewa shine kadai abokin sa bayan Hussain, shine kuma saurayin Safiyyah.