TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Da ka tara mutane da yawa ka basu abu kadan wanda wani ma a kudin motar komawa gida zai karar da abinda ka bashi gwara ka tara mutane kadan ka basu abinda in suka lallaba shi kum Allah ya sa ka musu albarka zasu rabu da talauci”

Hussain baya taba kyautar abu kadan. Shim Hassan haka yayi. Bayan an watse ne wajen laasar sannan ya samu ya tafi asibiti gurin Ruqayyah. Yauma Sumayya ce a wajenta, suka gaisa ya zauna yana lura da irin ramar da Ruqayyah tayi yace “kin rame da yawa. Hope ba wai har yau ba kya iya cin abincin ba?” Ta girgiza kai tace bacci ne bana iyawa. Tsorata nake yi duk dare.”

Haka ne, tun da Ruqayyah tazo asibitin bata iya bacci, in fact she is even scared of closing her eyes dan in banda gawawwaki babu abinda take gani. Gawar Minal, ta driver. In kuma tayi bacci mafarkin Hussain take yi, a very angry Hussain, abinda bata taba gani ba sanda yana raye amma yanzu a mafarkin ta tana ganin tsananin fushi a fuskarsa kuma yana binta kamar zai hallaka ta. Bata fada wa Sumayya ba, ta dai gaya mata tana mafarkin gawawwakin Fatima da ta driver a irin yana yin data gansu lokacin mutuwar su kuma Sumayya tagawa wa Inna Ade ita kuma ta bata adduoi kuma tayo mata rubutun da zai bata kariya daga tsorata. Dan sun san cew tsorata ce tayi. Sai dai kuma a mafarkin nata sai taga kafarta tana motsewa har sai ta koma irin ta jarirai sannan sai ta fadi tana kukan jarirai a haka har abinda ya biyo ta zai cimmata. Tayi kokarin yin addu’a akan hakan, tana so ta roki Allah ya yaye mata abinda yake damunta amma sai taji t kasa, me zata ce wa Allah a cikin addu’ar tata? Menene uzurin ta na aikata abinda t aikata? Duk wani link da take feeling a tsakanin ta da ubangiji idan tana addu’a a da yanzu jinsa take yi ya yi cutting, kamar ubangiji baya dubanta, bata son kuma tayi tunanin abinda hakan yake nufi dan amsar tunanin nata ba zaiyi mata dadi ba.

Bayan wannan kuma a duk lokacin da taji shiru babu maganganun mutane, sai taji kunnuwan ta sun cika da kukan jariri, kukan jaririn data ajiye a kofar orphanage.

A dole kullum ake yi mata allurar bacci, amma even with allurar baccin haka zata yi ta yi tana tsorata tana komawa tana dada farkawa har gari ya waye.

Amma ba zata gaya wa Hassan wannan ba. “Bana iya bacci ne mijina” ta maimaita tana kallonsa. Ya gyada kai “ki yi kokari ki cire abinda yake ranki kinji? Na san ba zaki manta ba, babu yadda za’a yi ki iya mantawa amma ki rage tunanin abin kinji? With time baccin ki zai dawo kamar yadda yake da” ta gyada kai kawai a lokacin da aka bide kafar aka shigo,suka juya ga aki daya. Maman Minal ce ta shigo tare da sallama, fuskarta jeme jeme kamar wadda ta kwana tana kuka. Ruqayyah ta kware da abincin da ta saka abakinta, Hassan ya tashi da sauri ya bata ruwa tasha yayinda Sumayya take yiwa maman Minal barka da zuwa tare da nuna mata kujera. Ta zauna duk suka gaishe ta, Ruqayyah ma ta gaishe ta ba tare da ta hada ido da ita ba. Sai matar tace “ya hakurin mu yaran nan? Allah yaji kansu yayi musu rahama. Ni naji labarin rasuwar amma ban dauka hatsari ne aka yi ba, ashe har da ke Ruqayyah a cikin accident din, Allah ya bami Lafiya” suka ce ameen, sannan tace “daga gidan ai nake, naje inyi muku gaisuwa kuma in tambaye ki labarin kawarki” Ruqayyah tace “ammmm……. ban ganta ba, ban san inda take ba. Ina nufin ba ta zo ta duba ni ba”

Maman Minal tace “baku yi waya da ita b kuma?” Ruqayyah tace “babu waya a hannuna ai, ta kone tare da…….tare da mota” Maman Minal ta share hawaye tace “kawarki yau kwanan ta uku rabont da gida. Ta tambayi mijinta zata je kasuwa ta karasa siyayyar kayan haihuwar ta, tunda ta fita shikenan. Anyi neman, duk inda muka san tana zuwa munje amma babu ita babu alamun ta.” Sumayya ta yi salati “mun shiga uku, abinda ya same mu kenan kuma? Allah in laifi muka yi maka Allah mun tuba ka yafe mana” Ruqayyah ta dauke kai gefe “ban ganta ba Mama. Na kwana biyu ban ganta ba” Maman ta bita da kallo sannan tace “amma mijinta yace tace masa gidan ki zata zo tare zaku tafi kasuwar. Har tace masa a can zai je ya dauke ta da daddare, kafin yaje daukanta ne akayi wannan rasuwar kuma da yaje ya tarar gidan a cike da mutane. Ya kura wayarta kuma a kashe” Ruqayyah ta kuma girgiza kanta tace “batazo ba gaskiya, ni ta jima ma rabon da tazo gidana” ta karasa tana kallon Hassan wanda ya tsare ta da ido yana lura da rashin gaskiyar da yake rubuce a fuskarta.

Maman Minal tace “na shiga uku ni Hauwa. Yarinyar nan ita ta shiga da tsohon ciki? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun” Hassan yace “Allah ya bayyana ta. An kai cigiya gidan radiyo?” Maman Minal tace “mijinta ya kai, har hoton ta duk yakai a gidajen talabijin” Sumayya tace “Allah sarki Minal. Kai duniya. Allah ka bayyana mana inda wadannan bayi naka suka shiga” Maman Minal ta mike tana cewa “dan Allah, idan kunji wani abu ko kunga wani abu ku gaya mana. Duk wanda yake da saka hannu a cikin batan yarinyar nan insha Allahu ba zai gama da duniya lafiya ba. Ni na san saka hannun makiyane dam anga zata haihu” sai kuma ta saka kuka “wayyo yata, Allah kar ka basu ikon cutar min da yata”.

Duk sai da zuciyoyin su suka karye, Sumayya tana tayata kuka. Tana fita wayar Hassan tayi kara. Ya daga yana sauraro sannan yace “shikenan, gani nan zuwa” ya mike yana kallon Sumayya yace “anga motar da Adam ya taho da ita” ta mike itama tana dafe kirji. “Shi kuma fa? An ganshi?” Yace “an kusa dai” ya jura zai fita ta tari gabansa tace “me suka ce, dan Allah ka fada min” yace “a hannun wasu mutane aka kama motar, sunce wai tsintar ta suka yi a gefen hanya babu kowa a cikinta kuma da key a jikin ignition, da kuma waya ta a ciki, they may be lying, zanje gurin yanzu za’a kara tambayar su dan a tabbatar” ta rufe fuskarta da hannunta shi kuma ya wuce ta ya tafi.

Gurin police ya fara zuwa, yaga wadanda aka ga motar a hannunsu amma su sun dage basu ga Adam ba. Ya barsu a hannun police din ya koma gida yace a cigaba da bincikar du sai sun fito da shi. Yana zuwa gida ya shiga part dinsa ya hau saman sa ya dauko spare key din motar Ruqayyah ya sauko, tun sanda suke magana da maman Minal yasan da akwai wani abu da take boyewa kuma jikinsa ya bashi abin yana cikin motar ta. Dan a ranar tace masa zata je kasuwa, kuma ance Minal tace zasu je kasuwa tare.

Ya bude kofar motar ya shiga ciki yana ta dube dube bai ga komai ba, sai ya bude booth, idonsa ya sauka akan manyan ledojin kaya, ya saka hannu ya bude a hankali sai idonsa ya sauka akan kayan babies da tarkacen kayan haihuwa. Ya koma da baya yana dafe kansa yana tunawa da maganar Maman Minal “siyayyar kayan haihuwa zata karasa”.

Tabbas Ruqayyah tayi masa karya.First Wave

Ya mayar da booth din ya rufe yana jin ciwon kansa yana karuwa. Tun sanda tana magana yasan karya take yi, amma baya so ta karya ta ta sai ya tabbatar da cewa karya take yi din, wannan shi yasa ya bincika motar ta dan yasan cewa in dai sun fita tare da Minal to kuwa zai iya ganin shaida a cikin motar tata. Ya juya yana kallon gate zuciyarsa tana gaya masa ya koma asibiti ya tuhume ta akan karyar da tayi masa amma sai ya fasa, ya rufe motar ya koma cikin gida dan magrib ta gabato. Sai da yayi wanka sannan ya tafi masallaci aka yi Sallah yare da gabatar da Adduoi ga Hussain da iyalinsa sannan shi kuma ya shiga cikin gida gurin Aunty wadda har yau take kwance babu lafiya, jiya ma sai da aka mayarda ita asibiti saboda jinin ta daya kuma hawa, wannan ya sa ya kuma jaddada cewa babu zaman makoki dan ta samu ta huta, da yayi yayi da ita akan a mayar da ita asibiti tayi zamanta acan inda zata ke samun kulawar likitoci kuma ba za a dame ta ba amma taki, tana so ta zauna take karbar gaisuwar Hussain kamar yadda ta karbi ta yaya Hassana da Alhaji Aminu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button