TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
A lokacin ne ta zaunar dashi briefly ta saka aka zuba masa abinci ta matsa masa sai da ya dan ci kadan, dan shi mantawa yake yi ma ana cin abinci in yana ci din kuma baya jin taste kwata kwata sai yaji kamar magani yake ci, bakin sa har daci yake yi, amma haka ta matsa masa ya cusa kadan ya sha kunun gyada. Ya kuma dudduba kannensa sannan ya fita ya koma gidan sa.
Direct dakinsa ya wuce ya rufe kofa ya kwanta a kan gado rigingine yana kallon ceiling, hannayensa biyu a harde akan kirjinsa yana sauraren yadda zuciyarsa take bugawa. Ya rufe idonsa hawaye yana gangarowa ta gefen idon zuwa wajen kunnensa. Kwana ukun nan da yayi a duniya alhalin Hussain baya cikinta ji yake sune mafiya kuncin kwanakin da yayi a duniya so far, bai san abinda rayuwa zata zo masa da shi ba nan gaba amma ya san ba zai kuma jin zuciyarsa ta dawo dai dai ba, saboda Hussain ya cire wani part na sa ya tafi dashi kuma baya jin zai kuma jinsa complete sai dai ko a lahira amma ba’a nan duniyar ba.
Sosai yake bukatar wanda zai lallashe shi ya gaya masa maganganu masu dadi amma waye kenan zai masa haka, wa zai runguma yayi kuka a jikinsa yaji sanyi a zuciyarsa? Wa zai gaya wa damuwarsa ko da kuwa ba zai masa magani ba? Yan uwansa duk mata ne suma karfin halin da suka ga yana nunawa shine a binda yake kara karfafa su to in sunga yayi rauni kuma suyi yaya da kansu? Ga Aunty tana fama da hawan jini kuma yasan daga strenth dinsa ita ma take samun nata Strength din na facing rayuwa a yadda ta zo musu. Ruqayyah? Ruqayyah tunda akayi rasuwar bai ji ta ambaci sunan Hussain ba ballantana tace Allah yaji kansa, abin ya tsaya masa a ransa amma koda yaushe sai zuciyarsa take bata uzurin itama halin da take ciki, a tsorace take sosai dan idonta zaka kalla kawai kasan a tsorace take. Maybe rudewa ce ta hana ta yi masa gaisuwar. Maybe.
Sai kuma ya tuno da kalaman Sumayya da tayi masa ranar nan, yaji dadin maganganun ta sosai kuma irin su yake so ake yi masa, a ranar ya fara sanin tana da hankali dan shi kullum kallon marar nutsuwa yake yi mata. Amma sai yaji tayi masa magana mai dadi mai ma’ana, sai yaji yana fatan idan Ruqayyah ta warke, idan ta dawo cikin hayyacin ta itama take gaya masa irin wadannan maganganun.
Sai kuma yayi bitar abinda ya faru yau, karyar da Ruqayyah tayi masa akan Minal, yana trying to make sense out of it, me yasa zata yi kokarin boye fitar da sukayi da Minal? Me ya faru da Minal? Me Ruqayyah ta sani a ciki me kuma take boyewa? Yasan Minal kawarta ce sosai duk da cewa shi ba son kawancen nasu yake yi ba amma yasan Ruqayyah ba zata hada baki da wanda zai zalinci kawarta ba.
Ya mike zaune yana girgiza kai, in bai bi a hankali ba shima sai nasa jinin ya hau soon irin yadda na Aunty ya hau koma zuciyarsa ta buga yabi Hussain, sai yaji wani bari na zuciyarsa yana son hakan ta kasance amma kuma kamar yadda Sumayya ta tuna masa sai ya tuno da ƴaƴan sa da kannensa, idan ya fadi ya mutu ina rayuwarsu ta dosa?
Ya tashi ya shimfida carpet dinsa na sallah sannan ya zauna akai ya jawo Alqur’ani ya fara tilawa, tabbas bashi da wanda zaije ya rungume yayi kuka a jikinsa amma yana da Allah, shi zai rarrashe shi ya karfafa masa zuciyarsa ya cigaba da facing rayuwarsa komai dacin ta.
A kan sallayar ya kwana yau ma kamar jiya da shekaran jiya, ya fita masallaci yayi sallar asuba sannan ya kuma komawa dakinsa ya kwanta yayi bacci mai cike da mafarkan Hussain, sweet memories din rayuwarsu tare, sai daya farka ya fahimci ashe mafarki yake yi kuma sai yaji yana so ya koma ya kwanta ya cigaba da wannan mafarkin har abada. Amma dole ya tashi, dole yayi facing rayuwarsa.
Ya shiga yayi wanka ya shirya sannan ya fito daga dakinsa ya shiga dakin Ruqayyah ya sake daukar mata wasu kayan tare da na little Hussain duk da cewa bata bukata ba, ya sauka kasa dakin twins ya dibar musu nasu kayan jaka guda, so yake su cigaba da zama a gurin Inna for now, sai in anyi bakwai yan Gombe sun fara komawa sannan sai ya karbo su ya dawo dasu gurin Aunty kafin Allah ya bawa Ruqayyah lafiya, in kuma ta samu lafiyar kafin lokacin shikenan.
Ya fito yana kallon gidan Hussain, standing so tall and mighty but empty. Dan tun washegarin da akayi rasuwar duk ma’aikatan gidan suka fito aka rufe kofar gidan aka kai wa Aunty keys din. Ya dauke kansa ya wuce zuwa mota ya zuba kayan hannunsa yana kallon motar Ruqayyah yana tunawa da kayan da suke cikin booth, ya wuce ya shiga part din Aunty ya gaishe ta, ya lura da mutanen gidan sun fara raguwa, duk kannne sa suka gaishe shi yana lura da yadda duk suka rame annurin fuskokin su duk ya dusashe.
Yanzu ma sai da Aunty ta matsa masa ya ci abincin, ya gaya mata zai je asibiti gurin Ruqayyah, duk suka tambayeshi ya jikin nata duk da Inna tayi musu bayanin ciwon na Ruqayyah, shi ma kuma ya kara jaddada musu cewa babu wani major problem. “Babu karaya babu tsagewar kashi, ko daddaujewar kirki babu, kafar ce kawai ta rike kuma likita ya gaya min insha Allah babu matsala zata warke” duk suka ji dadi kuma suka tabbatar masa zuwa yamma zasu je su dubata.
Yau Inna ya tarar a dakin Ruqayyah tana ta karanto addu’a tana tofawa Ruqayyah. Ya gaishe ta yana karanto yanayin damuwa a fuskarta, ta amsa tace “yarinyar nan har yanzu ta kasa samun bacci mai nauyi, dama Sumayya ta gaya min zabura take ta yi cikin dare tana firgita sai jiya nima da na kwana na gani da idona. Nayi mata rubutu ta sha dai, sai an hada da addu’a gaskiya” ya mike yana kallon yadda Ruqayyah take ta jujjuya kanta a cikin bacci yace “haka ne Inna, sai an hada da addu’a, kuma nasan kina iyakar kokarin ki. Allah ya saka da alkhairi” maganar da yake yi ta farkar da Ruqayyah ta mike da sauri tana cewa “Fatimah ta dawo? Tana ina?” Yi take kamar zata mike daga kan dagon amma babu kafar tashi, Inna ta rike ta tana karanto mata adduoi har ta sami nutsuwa sannan ta lura da Hassan a tsaye, ya ja kujera ya zauna yace “Ruqayyah, Fatima ta rasu, wanda ya mutu kuma baya taba dawowa kinji? Ki rage, ko yaya ne ki rage saka damuwa a ranki kinji? Kiyi kokari kike tunanin wani abin daban ba abinda kika gani ba, sannan ki ringa addu’a sosai ki na karanta Alqur’ani zai saka miki nutsuwa” sai ta fara kuka, tana kokarin yin addu’ar amma sam bata jin alamar addu’ar ta tana karɓuwa, daga ta daga hannunta da niyyar addu’a sai taji munanan aiyukan ta sun dawo ranta, sai taji ta kasa samun kalmomin da zata yi amfani dasu gurin rokon ubangiji bukatar ta. Amma kuma babu wanda zata iya gaya wa wannan.
Ta gyada kai kawai, sai ya karbi Hussain daga bayan Inna ta fita ta basu guri, shi kuma sai ya zauna a bakin gadon, ya kwantar da Hussain a gefenta ya jawo ta jikinsa yana tsananin son jin dumin jikinta, ta kwanta a jikinsa tana shaƙar kamshin sa tana jin ta dan yi missing dinsa ba laifi, yace “it is all going to be alright kinji? Ki daina damuwa kiyi ta addu’a” ta gyada kai tana jin hawaye yana sake taruwa a idonta, tace “promise me zaka kashe ku nawa ne, zaka yi duk anything possible dan ka samar min lafiya” yayi ajjiyar zuciya sannan ya dago kanta da hannunsa yana kallon cikin idonta yace “zanyi duk iyakacin iyawa ta dan in nemar miki lafiya Hassana, amma bani zan samar miki lafiya ba suma doctors din basu zasu samar miki lafiya ba sai idan Allah ya baki lafiya. Idan har Allah ya riga ya rubuta rashin kafa a cikin kaddarar ki, idan har amfani da zakiyi da wannan kafar taki ta kare to babu yadda zanyi babu kuma yadda likitoci zasu yi dole mu hakura” ta fara ture shi tana kuka ya sake kamota yace “look at me Hassana, ki tuna da rayuwar Hussain, ki tuna da irin dukiyar sa da yadda jama’a suke sonsa amma duk hakan bai sama masa lafiya ba. Kudin sa basu samar masa lafiya saboda Allah ya riga ya rubuta ciwon nan shine sanadin sa” ta fara girgiza kanta “bana so in rasa kafata Hassan bana so in zama gurguwa ka taimaka min mijina” yace “Ruqayyah, kwana hudu da suka wuce Hussain yana da rai, haka ma Fatima tare da abinda yake cikin ta, amma yanzu sun rasa rayukansu gabaki daya, ki duba Adam da kawarki Minal, babu wanda yasan inda suke babu ma tabbacin in suna raye, sai mu gode wa Allah da ya saka mu muke da ranmu kuma tare da yan uwan mu Ruqayyah, menene kafa? Allah ba shi ya baki kafar ba? Da yaso tun daga ciki zai yi halittar ki babu kafa kuma me zakiyi akai? Me zaki ce masa? An yi accident din nan kin fita lafiya, kafar nan tana nan ba wai guntulewa tayi ba kuma akwai tsammanin cewa zata warke. Menene abin damuwa a ciki? Mu gode wa Allah Ruqayyah”.