TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai tayi shiru ta kwantar da kanta a kirjinsa tana mayar da ajjiyar zuciya. Sai da yaji numfashin ta ya dai dai ta sannan yayi mata tambayar da take cinsa a rai tun jiya. “Me yasa jiya kika yi min karya Ruqayyah?” Ta dago kai tana kallonsa, irin kallon da taga yayi mata ne ya saka ta yi saurin mayar da kanta ta sunkuyar sannan ta tashi daga kirjinsa ta zauna sosai tana wasa da yatsun hannunta, ta san wacce karya yake magana akai kuma ta gama shirya amsar da zata bashi.

Yace “jiya kika ce da babar kawarki ba kwa tare ranar Friday, kika ce ba tare kuka je kasuwa ba kuma bayan tare kuka je, naga kayan da ta siya a booth din motar ki” ta dago kai tana kallonsa, bata san binciken nasa zai je har cikin motar ta ba tace “kayi hakuri mijina. Na fadi haka ne dan kada ranka ya baci tunda nasan ba ka son mu’amala ta da Minal, ta kira ni tace min zata zo muje in raka ta tayi siyayyar haihuwa ni kuma bansan me zance mata ba, babu dadi wanda yake kula ka kai kuma ka dinga wulakanta shi bana so tayi tunanin ko dan miji na yafi nata ne ko kuma wani abi daban, sji yasa mace tazo muje din, bayan mun gama kuma naso in sauke ta a gida sai tace min wai gidana zata taho muyi hira kafin dare sai mijinta yaje ya dauke ta, ninkuma bana son ka dawo ka tarar da ita a gidan ka ga kamar bana jin maganar ka shi yasa muna shiga na ga Fatima zata tafi Abuja sai nace zan bita ba wai dan ina son zuwa ba sai dan ina so Minal din ta hakura da shiga gidana tunda ta ga nima fita zanyi, shine ta bar kayan ta a mota ta tace zata aiko driver ya dauka, sai ta bi mu muka fita da ita bakin hanya muka sauke ta zata hau taxi ta tafi gida. Wannan shine karshen gani na da ita” ta karasa tana rintse idonta a ranta tana bitar ƙawancen su da Minal tun yarinta, is the money really worth it? Amma ta riga ta shiga iya wuya kuma babu damar fita ba tare data tarwatsa komai nata ba.

Hassan ya mike ya tafi bakin tagar dakin ya tsaya yana kallon bishiyoyin da suke wajen, koma na labarin Ruqayyah ya tafi dai dai babu tangarda sai abu daya, abu dayan nan shine labarin is so perfect yafi kama da labarin da aka zauna aka jima ana tsara shi ana kuma bitar sa har sai da aka tabbatar babu giɓi a tare dashi. Bai yi kama da true life story ba. Ya juyo yana kallonta, itama shi take kallo tace “kayi hakuri dan Allah, na fadi haka ne jiya dan kar in bata maka rai” cikin fada yace “amma kin fahimci cewa ran kawarki ne kika yi wasa dashi saboda kar ki bata min rai? Kin fahimci cewa rayuwarta tana cikin hadari amma ke kina karya dan kar inyi miki fada? Wacce irin kawa ce ke? Bata fa aka ce tayi? Kwana hudu yau ba’a san inda take ba amma kina tunanin kar raina ya baci in kin fadi gaskiya. Ba kiyi tunanin cewa ke ce mutum ta karshe da ta ganta kafin batanta ba? Ba kiyi tunanin cewa yanuwanta da mijinta ya kamata su san gaskiyar magana ba? Baki yi tunanin abinda zaki fada zai taimakawa police gurin binciken inda take ba?” Tayi sauri ta dago kai tana kallonsa jin ya ambaci police, ita sam bata dauka zai dauki zafi haka ba dan tasan ba wai ya damu da Minal din bane ba, a sali ma ba ya son muamalar ta da ita, ta dauka zasuyi maganar su a tsakanin su su gama ta bashi hakuri shikenan maganar ta wuce, amma gashi taji yana ambaton yan sanda.

Ta sake cewa “kayi hakuri dan Allah” ya dawo ya tsaya a gabanta, so tall and so strong, hannun sa a aljihun sa yace “kar ki sake yi min karya irin wannan. Banaso” ta gyada kai da sauri, yace “idan kin fadi gaskiya zanyi miki fada, amma fadan nawa na yan mintuna ne shikenan ya wuce, amma idan kika yi karya zaki kara yin wata karyar ne dan ki kare waccan daga nan kuma ki sake yin wata dan ki kare wannan a karshe sai ki ga kin zama makaryaciya. Kina da ilimi kinsan menene karya, fadin Annabi ne yace karya tana daga alamomin munafiki, kin kuma san hukuncin munafiki Allah da kansa yace ba zai shiga aljanna ba. Ballantana karya irin wannan da zata saka ran kawarki a hadari” tayi shiru kanta a kasa, ita dai so take ya gama fadansa amma kar ya kuma ambaton police din nan.

Sai ya zauna a kujera yana kallon ta yace “kin ga motar da ta shiga” tayi sauri ta gyada kanta tace “taxi ce” yace “zakiniya tuna plate number dinta?” Tace “a’a, ban ma kalla ba. Sabuwa ce dai motar” ya dafe kansa yana daidai ta numfashin sa saboda yadda yaji kan ya dauki zafi, yana tsoron kar jininsa ya hau, har yanzu yana ganin alamun karya a fuskarta. Yace “sai menene ya kamata in sani?” Ta girgiza kanta tana daukar Hussain data fara mutsu mutsu zai tashi daga bacci tace “shikenan, shikenan nima abinda na sani”

Ya jima a zaune yana kallon ta tana feeding Hussain sai kuma ya mike yace mata “zan dawo da daddare, if you need anything call me” har ya kai bakin kofa kuma sai ya juyo yace “bani wayar Fatima da take hannun ki” tace “to ai da ita nake amfani” yace “bani, zan kawo miki wata da daddare in na dawo” still bata bayar ba tace “to da wacce zan kira ka in ina bukatar wani abun?” Ya dafe kansa yace “Ruqayyah ki bani wayar mutane, fa Inna nan ga Sumayya duk suna da number ta, wannan wayar ba tawa ba ce ba ba taki bace ba ba kuma ta gadon Hussain bace ba” ta mika masa watar ganin ya dauki zafi kamar zai rufe ta da duka. Ta bishi da kallo har ya bar dakin sannan ta mayar da idonta kan kafarta marar lafiyan, a idonta sai taga kamar kafar ta fara kankancewa kamar yadda take gani a mafarkin ta.

Yana kokarin fita Sumayya tana shigowa, kallo daya yayi mata taji tausayin ta ya kama shi gaba daya tayi zuru zuru kamar wadda ta tashi daga jinya. Ta gaishe shi sai ta tsaya bata ce masa komai ba amma yasan tana son jin yadda aka kwana a neman Adam, sai yace “munyi magana dasu, suna yin iyakacin kokarin su. Kiyi hakuri kinji? Za’a ganshi insha Allah” ta gyada kai kawai, har zai wuce ta sai ya kuma ya dawo yace “kiyi murmushi mana. Nafi son inga kin ware kina harkokin ki yadda inya dawo zaiji dadin ganin ki ba wai ya tarar da ke kin zama kashi ba” still bata yi murmushin ba, shi bai taba ganin ta a wannan yanayin ba shi Sumayyan da ya sani kullum cikin dariya take har gani yake kamar ta fita sakarci. Sai ya kasa wucewa yace “kin manta Adam din naki ne? He is strong, yayi going through abubuwa da dama Allah ya jarabce shi ta hanyoyi da dama am sure wannan ma wata jarabawar ce yaje yi kuma he is going to come out stronger and better” ta gyada kai tace “insha Allah. Nagode” ya kuma yin kamar zai tafi sai ya kuma dawowa yace “dan Allah, ina son ki binciko min number din mijin Minal kawarku, ina son yin magana dashi akan case dinta” tace “Okay insha Allah” yace “in kin samu sai ki ajiye min a gurinki, zan dawo da dare sai in karba” ta amsa masa sannan ta wuce ciki shi kuma ya fita waje. Yana ji a ransa cewa dole ya shiga cikin neman Minal tunda matarsa ita ce last person da ta ga Minal din, zai kuma yi iyakacin kokarin sa wajen ganin case din to the end.

Bai tafi gida ba duk da wayarsa ta yaji tana ta kara kuma yasan daga gidan ne ake nemansa, yasan wasu ne suka zo masa gaisuwa amma idan ya koma gidan ba lallai bane ya kuma samun damar fitowa ba sai kuma dare, kafin nan police sun tashi. Station din jiya ta sake komawa, har yanzu yaran da aka kama da motar suna tsare, sai dpo din ya shigar dashi office dinsa suka zauna yace “yaran nan ina ganin iyakacin gaskiyar su suka fada, bana jin sun san inda yaran nan yake. Barayi ne, irin kananan barayin nan na unguwa masu sane da satar waya, suna yafiya kawai suka ga motar a bakin hanya ita kadai, sun dauka ko mai motar ya fita ne zai kama ruwa shine suka tsaya da niyyar su tsorata shi su karbi wayar sa da yan kudaden hannunsa. To sai suka ga babu kowa a cikin motar, ga kuma key a jikin ignition shine kawai suka dauko motar suka shigo da ita Kaduna da niyyar su siyar da ita, to amma kasancewar motar babba ce dan irin ta guda uku ce a Kaduna sai ya sa suka kasa batar da ita, ta ki siyuwa har aka kama su da ita. Sun ga wayarka a cikin motar, sun cefanar da ita” Hassan yayi ajjiyar zuciya yace “wayar yaron fa?” Yace “basu ganta ba, mun duba motar kuma ba mu ganta ba muma”. Hassan ya mike yace “ku yanke musu hukuncin duk daya dace, ni bani da case dasu, ni case dina shine na yaron nan” dpo ya mike shima yace “muna iyakacin kokarin mu, amma yaron tamkar wanda ya bace ne a cikin iska”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button