TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Da dare Hassan ya koma gurin Ruqayyah, tare da Aunty da dukkan kannensa da aunties dinsa guda uku. Suka duba ta ita kuma tayi musu gaisuwa. Sannan suka yi mata sallama suka koma gida, Hassan ya karbi number din Alhaji Kabiru a hannun Sumayya, sannan shima ya tafi. Da safe ya kira shi suka hadu yayi masa bayanin da Ruqayyah tayi masa na inda suka rabu da Minal da kuma yadda suka yi. Ya kuma roke shi alfarmar cewa duk abinda ake ciki ake sanar dashi, duk kuma wani taumako da ake bukata na kudi ko na wani abu azo gurinsa zai taimaka. Da haka suka rabu. Sai yaji a zuciyarsa yana tausayin Alhaji Kabiru, batan mata matar ma kuma mai tsohon ciki lallai akwai tashin hankali a ciki…
Kwanaki suka wuce har akayi sati daya da rasuwar Hussain. A cikin satin nan ba karamar wuta Ruqayyah ta hura wa Hassan ba akan lallai sai ya fita da ita waje taga likita dan har yau wannan likitan da yake ganinta bai gama tabbatar da abinda yake damunta ba. Ita gaba ki daya a tunanin ta fita waje shine babban solution din problem dinta. Dole Hassan ya nema musu bisa ita da Sumayya zuwa Germany, inda aka hada shi da wani doctor da akace ya kware a bangaren jijiyoyi, a hakan ma sai data nuna rashin jin dadin ta dan ita tafi son su tafi tare tana ganin zata fo samun kulawa in tana tare da shi, shi kuma yaki binta saboda he is not mentally ready, ji yake yi kamar yau ne Hussain ya mutu.
Ya riga ya gama shirya musu komai, daga asibiti za’a turo mota har airport ta dauke su,a asibitin kuma suna da duk abinda zasu bukata na yau da kullum, a kwai kuma mota idan suna son shiga cikin gari su nemi wani abu da babu a asibitin, duk bill kuma za’a turo wa Hassan. A haka suka rabu, ya kai su airport suka tashi sannan ya juyo da niyyar dawowa gida.
Amma sai me? Tun kafin ya karasa gida sai ga kira da number din Sumayya. Yayi packing gefe yana jin hankalin sa yana tashi ya dauka “Sumayya lafiya? Naga fa tashin ku da ido na, me ya faru” muryarta yaji cikin karkarwar baki tana magana “yaya Hassan, gamu a Abuja” yace “Abuja kuma? Me ya faru Sumayya kiyi magana mana” tace “jirgin yana tashi Ruqayyah ta fara complain da kunnenta wai kamar zai yi bursting, na dauka raki ne sai naga ta rude har da faduwa kasa tana kuka tana cewa azo a taimaka mata. Muna dubawa sai muka ga jini yana fitowa daga kunnuwan ta. Dole jirgin yayi emergency landing a Abuja aka ajiye mu, kafin mu sauka har ta suma”.
Hassan ya dafe kansa yana maimaita innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Sai da yaji nutsuwa sannan yace “kuna ina yanzu?” Tace “muna hanya za’a kaimu asibiti. Ma’aikatan airport din ne suka dauke mu zasu kaimu” daga cikin wayar yana iya jiyo kukan Hussain Junior, Sumayya kuma duk a rude take kamar ma kuka take yi. Sai yace ta bawa driver wayar, ya tambaye su asibitin da zasu kai su suka gaya mishi sai ya kashe wayar sannan ya kifa kansa a jikin stirring yana mayar da numfashi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Me yake faruwa da su ne?
Daga nan bai karasa gida ba sai ya juya zuwa airport, bai kuma kira Aunty ya gaya mata ba saboda tana gudun duk wani abu da zai tayar mata da hankali. Sai daya je airport din sannan ya kira Jabir ya gaya masa in case ko za’a neme shi. Daga nan ya samu jirgi sai Abuja.
Kafin ya sauka har anyi admitting Ruqayyah kuma likitan kunne ya hau kanta yana bincikar abinda ya kawo mata ear bleeding. Sai bayan ya fito sannan Hassan ya karaso dan haka direct office dinsa ya wuce sai doctor yayi masa bayani kamar haka. “I am sorry sir, but matarka ta hadu da ear problem a sanadiyyar shiga jirgi da tayi with an ear infection wanda kuma it is not advisable. Ear drum dinta yayi bursting, sai munyi mata surgery a kunnuwan ta duk biyu sannan maybe jin ta zai dawo, but bani da tabbas din zai dawo dai dai. Sannan kuma abinda nake da tabbas akai shine, ko anyi nasarar aikin ko ba’a yi nasara ba, kar a kuma barinta ta hau jirgin sama ever again, in ta kuma hawa kuwa, zata yi loosing hearing dinta completely ko ma ta rasa ranta baki daya”
Wannan littafin na siyarwa ne, idan kika ganshi a wani gurin na sata ne, idan kina so ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020.The Second Wave
Hassan ya saki baki yana kallon doctor din, ya girgiza kansa yana dan dukan goshinsa wai dan ya farka idan bacci yake yi amma sai ya ganshi still a gaban doctor din da yake kallonsa. Ya bude bakinsa amma ya kasa magana. Ya kasa tabbatar da cewa dai dai kunnuwan sa suka jiyo masa, kamar fa ji yayi likitan yana cewa Ruqayyah ta kurumce. Matar sa Hassana. Precious wife dinsa.
Yace “doctor? What are you trying to say? Ni duk ban gane bayanin ka ba kayi min gwari gwari Please. Kana nufin Hassana ta kurmance ko me kake so ka gaya min” doctor din ya gyada kansa yace “haka nake nufi, ina nufin dodon kunnenta na dukka kunnuwa biyun ya samu matsala. A yanzu haka bata ji, in kayi mata magana ba zata ji ka ba but in ka saka hannu anyi mata aiki da gaggawa zata iya dawowa tana ji kadan kadan ba kamar da ba. Sai dai kuma kamar yadda na fada ina bada shawarar kar ta kuma attempting shiga jirgi ko da kuwa nan da Kaduna ne”
Hassan ya kuma dafe kansa yana ambaton innalillahi wa inna ilaihir rajiun, daga neman kafa kuma yanzu shikenan sai a rasa kunne kuma? Kunne fa, shi fa a gurinsa yana ganin kunne duk yafi muhimmanci a cikin sense organs na jikin mutum, saboda shine yake responsible for balance in baka da kunne kana rasa balance ne yadda ko tafiya ma wahala take zamar maka, wani rashin kunnen ma ya kan taba har da kwakwalwar mutum sai mutum ya zama kamar mai mental problem, shi yana ganin anya ma kuwa kunne bai fi ido muhimmanci a jiki ba?
Ya dago kansa yana kallon likitan da yake kallonsa seriously, sai ya mika masa hannu yace “kawo takardar inyi signing” ya mika masa ya saka hannu yace “yaushe za’a yi mata aikin?” Doctor yace “as soon as possible, kamar tomorrow morning insha Allah” Hassan yace “tomorrow morning? Ba za’a iya yi mata yau ba? I mean ba za’a iya yi mata yanzu kafin ta farka ba?” Doctor ya girgiza kai yace “noo, ba za’a iya ba. Muna bukatar preparation ita ma kuma muna bukatar preparing dinta. Dan ma kune, kuna da kudi, idan babu kudi wani ya kan dauki weeks ba’a yi masa aiki ba wani ma months, wani ma har abada ba za’a yi masa ba haka yana ji yana gani zai zama kurma” Hassan ya gyada kai a ransa yan godiya ga Allah, there is always something to be grateful for. Sai kuma yaji ya samu idea akan wani abu daya kamata yayi da kudin Hussain.
Sai dai kuma he is not looking forward to seeing Ruqayyah, dan bai san me zai ce mata ba kuma ko ya fada din ma ba jinsa zata yi ba. Yaji hawaye ya taru a idonsa, yana matukar tausayin ta a ransa, wannan shine ana kukan targade ga karaya ta samu. Ya fita ya tafi dakin da aka kwantar da ita, ya tarar tana bacci, fuskarta duk jirwayen hawaye, tana ta zabura alamar tsorata take yi a cikin baccon nata, Sumayya tana zaune a gefenta tana rera kuka a hankali, ga Hussain a hannunta. Yana shiga Sumayya ta mike tana kallonsa, tana jin kamar wani babban solution yazo da zaiyi maganin problem dinsu, sai dai abinda ta karanto a fuskarsa yasa ta koma ta zauna tana sake wani sabon lalen a kuka. Ya zauna a bakin gadon yana dora hannayensa akan goshin Ruqayyah, ya fara shafa gashinta a hankali sai yaji ta sauke ajjiyar zuciya. A ransa yace ina ma dai zata cigaba da baccin nan har zuwa sanda za’a yi mata aikin? Baya son tayi experiencing total deafness yafi son in akayi aikin ko yaya ne tana ji hankalin ta ba zai tashi kamar yadda zai tashi in taji dif ba.