TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Ruqayyah dai tana kallonsu suna ta magana, bata jin mai suke cewa tana dai jin mixed voices dinsu kamar masu rada da juna tace “me kuke cewa ne wai? Ai kin bai yi ba ko? Na gaya maka ai mijina, aikin nan ba kyau zaiyi ba kazo mu tafi Germany din, a warkar min da kafata shima kunnen ayi min aikinsa acan, anan babu abinda za’a samu sai wahala. Dan Allah Hassan kar ka bari na kurmance” ta karasa tana kuka. Doctor din ya kalle shi yace “baka gaya mata ba?” Ga mamakin ta sai taji taji wannan tas, ta juyo tace “menene za’a gaya min” yace “cewa ba zaki kuma hawa jirgin sama ba ballantana har kije wata kasar. Likitocin dai da suke Nigeria damu zaki yi hakuri ki lallaba har zuwa karshen rayuwarki” ta zaro ido tana kallonsa sannan ta kalli Hassan tace “he is lying” likitan ya dauki takardun sa yace “in baki yarda ba akwai hanyar tabbatar wa, ki tafi airport yanzu ki hau jirgi ki gani. Ina tabbatar miki dan guntun jin da kika fara samu zaki rasa shi gabaki daya”.
Daga haka ya fice ya bar su da rigima. Yasan bai kyauta ba yadda yayi breaking news din amma kuma shima haushinta dama yake ji yadda take ta nuna wa cewa basu iya aiki ba da sauransu, wai ita matar mai kudi. Yanzu sai yaga amfanin da kudin nata zaiyi mata.
Washegari suka bar asibitin dan Ruqayyah cewa tayi ba zata iya cigaba da zama ba. Hassan yayo mata order hearing aid din da zata ke amfani dashi, yaso kuma ace gida zasu koma amma taki komawa tace ita sai dai a chanja mata wani asibitin inda wani likitan zai sake duba kafarta tunda tana tsoron daring likitan kunne da yayi warning kar ta kuma shiga jirgi.
Wani private asibitin kashi ta tafi anan Kaduna, doctor din yayi mata alkawarin zai warkar mata da kafarta tana zuwa yayi admitting dinta ya fara karbar kudade yana sakawa a aljihunsa, tana asibitin aka kawo mata hearing aid dinta ta fara amfani dashi kuma alhamdulillah jinta ya dawo tana ji tas amma sai da shi, in ta cire sai dai taji kadan kadan kuma shima sai tayi stressing kunnenta tukunna. Daga baya ta fahimci cewa likitan bashi da clue akan abinda yake damunta dan haka ta nemi sallama kuma ya bata sai ta hada kaya sai Kano, AKTH, tana zuwa nan ma suka hau kanta da gwaje gwaje da hotuna da magunguna amma bayan shafe wata guda cur a cikin asibitin sai suka tabbatar mata da cewa su basu da idea me yake damun kafarta. A guri daya kuma kafar sai kara motsewa take yi kamar ta mai ciwon shan Inna, yanzu har kankancewar tata ya zama ana gani ake ganewa dan kana gani zaka gane daya kafar tafi dayar girma. A karshe sai likitoci suka yi mata cast, tun daga hips dinta har zuwa tafin kafarta dan ya taimaka mata wajen motsa kafar, daga nan suka ce babu abinda zasu kuma iya yi mata.
Ta zama mai kafa daya kamar yadda ta zama kurma.
Ina mai bawa wadanda suka sayi littafin nan hakuri na rashin jina da basuyi ba jiya, nayi tafiya ne kuma gurin da naje suna matsalar nepa, naso in muku typing da yawa dan in wanke muku zuciya amma shima ba zai samu ba. Ayi min afuwa. Biki ne muke yi na dana, zaku jini shiru yau da gobe amma insha Allah jibi za’a samu mai tsaho kuma mai dadi. Zamu ji third wave din da zata yi hitting Ruqayyah.
Ayi hakuri Please
Wannan littafin na siyarwa ne, in kin ganshi a wani gurin na sata ne. In kina son ki karanta halaliyar ki kiyi min magana through WhatsApp ta wannan number din 08067081020The Third Wave
Kusan watanni biyu kenan da rasuwar Hussain. Kusan watanni biyu kenan da rushewar farin cikin rayuwar Hassan. A cikin wata biyun nan ba zai iya tunawa da ranar da yayi murmushi ba ko da kuwa na yake ne, ba zai iya tunawa da ranar da yaji farin ciki a cikin zuciyarsa ba komai kankantarsa kuwa kuma baya jin zai kuma jin farin ciki a kusa, bao san abinda ubangiji ya tanadar masa in the future ba amma ya san da wahala ya samu waniabu da zai maye masa gurbin abinda ya rasa, babu abinda zai maye masa gurbin Hussain da family dinsa including his own family.
Amma kuma duk da haka yasan abinda ya rasa, bayan rashin Hussain ya rasa wanda zai rarrashe shi ne kuma wannan rarrashin da kalamai masu dadi da kantar da hankali su yake bukata, soyayya da kulawa yake bukata, babu kuma abinda ba zai iya bayarwa ba dan yaga ya samu abinda yake so amma shima kanta yasan abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Dan inda zai samu wannan, wadda take da hakkin bashi wannan ita yanzu sam hankalin ta baya kansa ma kwata kwata yana kan nemawa kanta lafiya. Yes, yasan abinda ya faru da ita is quite unfortunate yasan dole ita din abar tausayi ce amma abinda yaso tayi shine ta fawwalawa Allah komai ta gode masa akan niimomin da already ya riga yayi mata bawai ta tayar da hankalin ta kamar yadda ta tayar a yanzu ba. Ba zai iya tuna ranar da yaje dubata ya tarar bata kuka ba, ko kuma ranar da suka yi waya yaji muryarta babu alamar kuka ba. Yanzu gashi doctor din da yake dubata yanzu yace jinin ta ya hau, on top of everything kuma tana kokarin ta dora wakanta hawan jini.
Tunda aka yi mata aikin kunne aka samu nasara kuma aka saka mata hearing aid jin ta ya dawo yaso ace ta dauki kaddara ta dawo gidan ta ta zauna a hankali har asan yadda za’a yi da matsalar kafarta, tunda dai kafar ba wai ciwo take yi mata ba amma sai taki yarda ta tubure masa ta fara bin asibitoci desperately tana neman miracle, kuma kowanne likita in taje gunsa abinda zai gaya mata daban da wanda wani likitan ya fada. Yayi yayi taki hakura, su Baba ma sunyi taki jin maganar su, har ta fara tunanin wai dan nakasa ta same ta shine ba zasu taimaka mata ta samu lafiya ba, shi kuma tace masa dama ba sonta yake yi ba so yake ta zama nakasashshiya dan ya ajiye ta a gefe ya sake sabon aure, shi yasa yace ba zata nemi lafiya ba.
Jin haka yasa ya rabu da ita, kuma duk bill din da akayi masa na magani yana bayarwa amma baya zama tare da ita yana gida yana jinyar tasa zuciyar, dan shi yanzu sam baya son barin gida, baya son abinda zai saka yayi nisa da kabarin Hussain inda kusan kullum nan ne gurin zamansa. Indai ana nemansa a gida nan ake zuwaa same shi ya tasa kabarin a gaba ya zuba tagumi yana tunani, nan ne spot dim tunaninsa tunda dama Hussain ne abokin shawarar sa to yanzu tunda babu Hussain din shine ya mayar da garden din da aka binne Hussain gurin zam yayi tunani, a cikin tunanin ne kuma ya yanke shawarar da tun sanda Hussain ya raba dukiyar sa biyu ya bashi yabi ya fara yinta. Kuma babu gudu babu ja da baya abinda zai yi kenan.
Ya nemi lauyoyin H and H group of companies sun zauna meeting, ya gaya musu kudirin sa kuma kamar yadda ya riga yayi tsammani sun nuna masa rashin amincewarsu. “Ba haka ake business ba Sir” ya mike yace “am not a business man, dan haka ba business ne a gaba na ba. Hussain ne business man kuma yanzu baya duniyar, cigaba da business daga inda ya tsaya ko kuma akasin haka ba zai kare shi ko ya rage shi da komai ba. An riga an rufe littafin sa, abinda zai amfane shi kawai shine sadakatul jariya da yayi sanda yana da rai ko kuma akayi da sunan sa. Ko kuma sadakar da akayi da sunan sa bayan bashi da rai, ko kuma yayan da ya bari a duniya, to shi bai bar Da a duniya ba dan haka abinda ya rage wanda zai amfane shi a yanzu shine sadakar da akayi da sunan sa” ya jawo takardar da already ya riga yayi drafting har ya saka hannu ya mika musu yace “I am going to sell H and H group of companies and all its assets. Zan kuma rabar da dukkan kudin, nawa share din da nasa, ga mabukata da niyyar Allah ya kai ladan kabarin Hussain”