TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Sai yaga dukkan jikinsu yayi sanyi. Yaji shima zuciyarsa ta karye, yana tunawa da duk irin fadi tashin da Hussain yayi gurin kafa Kamfanin, but keeping kamfanin ba zai amfani Hussain da komai ba a yanzu, bai kuma bar dan da zai gaji sunansa ba ya kuma cigaba da running kamfanin, shi kuma da ya ke da share mafi yawaya gadonsa bashi da wani interest a yin kudi ko kuma living lifestyle irin na Hussain, bashi da interest din zama Hussain dan yasan shi ba Hussain din bane ba, shi a yanzu ma bashi da wani interest na rayuwa kawai dai yana yin ta ne. Abinda zai amfani Hussain kawai yake nema dan da ace idan yayi sallah za’a kaiwa Hussain ladan da kullum in yayi tashi sai yayi masa shima. Dan haka ya yanke wannan shawarar…..
Bayan ya koma gida ya dauko wayarsa da take ta faman ruri tun dazu amma baya cikin mood din amsa waya dan haka yaki dauka, sai da yayi packing sannan ya daga yaga sunna Ruqayyah, sai da gaban sa ya Fadi dan yasan complain din wani abu zata yi masa ko kuma kuka zata yi masa. Ya dauka, kukan kuwa yaji tana yi “tun dazu nake kiran ka mijina kaki ka dauki wayar” yace “am sorry Hassana. Ina meeting ne da lauyoyin H and H shi yasa ban dauka ba” ta danji sanyi a ranta, at least dai dukiyar ta na nan, at least dai komai nakasarta still ita matar mai kudi ne, still ita matar CEO din H and H ce dan haka zata shana kuma zata huta ko da kuwa a Nigeria din ne kadai. In ma kuma kasar take son bari ai ana iya tafiye tafiye a mota ko a jirgin ruwa, yes, zata iya yin tafiya a jirgin ruwa tunda dai mijinta yana da kudin da zai kaita duk inda take so.
But before that, tana bukatar kafarta.
Tace “doctor ne dama ya rubuta mana sallama” Hassan yace “to alhamdulillah. Masha Allah” ta fara kuka “haka ma zaka ce? Ba zaka kira shi ka gaya masa cewa ban warke ba? Ta yaya zai sallame ni bayan ban warke ba?” Ta kwantar da kansa yana dora hannun sa a goshinsa yace “Hassana alhamdulillah fa nace, idan bam godewa Allah ba me kike so ince masa? Ko a bakin kura nake dole ne na godewa Allah tunda har ya halicce ni kuma yasa na rayu cikin imani har lokacin da yayi niyyar daukan raina” tace “kullum haka kake cewa, sai kake acting kana making dina ina feeling guilty ina jin kamar bana godewa Allah bayan da bana gode masa da yanzu zuciya ta ta buga na fadi na mutu” yace “ni ya akayi tawa zuciyar bata buga na mutu ba? Bani da uwa bai da uba dan uwana kuma ya tafi, ina ma zamu iya exchange din guri ni da ke? A dawo min da iyayena da Hussain a karbi kafata daya da kunnuwa na, ke ni ko da idon aka ce za’a hada zan bayar dan nasan Hussain zai kula da ni kamar yadda Sumayya take kula da ke. But you never appreciate her. Ban taba jin kin gode mata ba ko kuma kinyi mata magana mai dadi ba duk da kokarin da take despite halin da ita ma tata zuciyar take na rashin masoyinta” ai kuwa kamar ya tsokano wata rigimar “ni ina mamakin ku kai da Sumayya, yanzu duk halin da nake ciki amma wai baku manta da maganar inyamurin drivern nan ba, baku san irin takaicin da kuke saka min a zuciya ta in kunyi maganar sa ba…..” Sai ya cire wayar daga kunnensa ya ajiye ta a gefe ya lumshe idonsa, baya bukatar wani bacin ran in ba so yake shima nasa jinin ya hau ba, sai da ya bar wayar ta huta a gefe sannan ya dauka ya mayar kunnensa yace “hello” tace “shine kayi shiru ko?” Yace “to ai babu abinda zan ce miki ne. Gobe zan taho kanon da wuri insha Allah, ku shirya kafin inzo, ina zuwa sai mu karbi takardar mu taho gida” daga nan ya katse kiran sannan ya kashe motar ya fita, ya daga kai yana kallon gidan Hussain wanda har yanzu yake a rufe, har yanzu ya kasa samun courage din shiga ballantana ya samu damar duba personal kayayyakin Hussain.
Gidan Aunty ya shiga, ya tarar tana cin abinci shima ya zauna ta zuba masa da kanta ya fara chachchakula kamar mai cin magani, tunda akayi rasuwar nan haka yake cin abincin sa dan shi kansa ba xai iya tuna ranar da yayi enjoying abinci ba. Ta zuba masa lemo tana cewa “Fulani Hadiza, kishiyar Maman Fatima tayo min waya jiya” ya tsaya da taunar abincin ya dago kai yana kallonta yace “me tace?” Tace “cewa tayi gobe idan Allah ya kaimu zasu aiko a debi kayayyakin Fatima” ya ajiye chokalin yana jin abincin ya tsaya masa a kirjinsa, a idonsa yana tunawa da ranar da aka zo akayi jeren kayan Fatima ana ta kide kide da fara’a da wasa da ɗariya, babu wanda zaiyi tunanin shekara biyu ne kadai ya rage mata daga ita har mijinta a duniya, yatuna da irin lodin kayan da aka zuba mata har sai da aka juya da wadansu duk kuwa da yawa da kuma girman dakunan ta.
Can cikin makwogwaron sa yace “Allah ya kaimu goben. Akwai keys a nan ko?” Tace “eh akwai” sai ya gyada kai kawai yana ture abincin. Zuciyarsa tana yi masa zafi, tragic deaths of family din dan uwansa yana dawo masa sabo. Aunty ta lura da chanjin yana yin sa sai ta fara kokarin cheering dinsa ta hanyar bashi labarin twins dinsa da da irin rigimar da suka yi tayi mata da taje gurin Inna ganinsu suna cewa sai sun biyo ta,ta san babu abinda yake faranta masa kamar labarin ƴaƴan sa amma sai taga ko murmushi bai yi ba ballantana dariya, yi yayi ma kamar baya jin abinda take cewa har sai da yaji tayi shiru sannan ya mike yayi mata sallama ya fita.
A ranar da daddare ya bude gidan Hussain ya shiga. A palon farko ya tsaya ya kunna fitila, idonsa ya sauka a kan katon hotonsu shi da Hussain, ya taka a hankali ya je gaban hoton ya tsaya ya a kallon fuskar Hussain, a kansa yana bitar maganganun da suka yi lokacin da akayi hoton da yadda Hussain ya ringa gyara zama wai shi lallai sai yayi zaman da yafi kyau. “Ka tabbatar na fishi kyau fa!” Ya gaya wa camera man din. Hassan ya saka hannu ya shafa fuskar sa, a hankali yace “ranar da ka bar duniya kafi kyau akan kowacce rana”.
Sai ya juya ya doshi stairs din da sauri kafafuwan sa har suna hardewa cikin junansu. Bangaren Hussain ya shiga ya kunna fitila yana kallon gurin kamar yau ya fara shiga, taste din Hussain yana da karfi sosai dan haka sai yake ganin kamar komai na gurin kama yake yi masa da Hussain. Sannan ya wuce cikin Bedroom dinsa, ya tarar da komai a gyare tas kamar jiran mai dakin ake yi yazo, sai dai yar kura da dakin yayi. A kan bedside ya ga hoton su replica na wanda yake dakinsa, ya dauka yana kallon yace “mai gasa kawai. Dan na saka a dakina shine kasa a dakin ka ko?” Sai yaji a ransa kamar Hussain yace masa “ni ba zanyi fada da kai ba” shima sai yace “nima ba zanyi fada da kai ba” sai ya ajiye hoton ya zauna akan gado, har yanzu ya kasa yanke hukuncin abinda zaiyi da gidan, shima da yayi niyyar zai siyar da shine kamar yadda zai siyar da duk sauran gidajen Hussain amma yanzu da ya shigo gidan, da yaga gidan, sai yaji kamar ba zai iya siyarwa din ba, akwai memories na mutanen gidan sosai a cikin gidan, sweet sweet memories da ba zai so ya rabu dasu ba. Da ya shigo dakin sai yaji ya rage jin loneliness, kamar Hussain din yana tare da shi.
Ya ja pillow ya dora kansa yana tuna ranar da Hussain yaje kan gadonsa ya kwanta har ya tsokane shi yace pillow din Ruqayyah ya kwanta akai, shima sai ya ture pillow din kamar yadda Hussain ya ture a lokacin, a nan ne idonsa ya sauka akan diary din, diary din da Hussain kullum yake ta faman rubutu a ciki kuma ya hana kowa karanta wa. Ranar nan babu yadda baiyi ba ko page daya ya bashi ya karanta amma ya hana shi. Ya saka hannu ya dauka a ransa yana tambayar kansa if it’s right ya karanta a yanzu. Shin Hussain zai so ya karanta a yanzu da bashi da rai ko kuma zai so yayi destroying ba tare da ya karanta ba? Ya jima yana lissafin abin sannan a karshe ya yanke shawarar zai fara karantawa amma in yaji abin da bai kamata ya karanta bane ba zai fasa karantawa sai ya kona shi.