TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A zauna akan study table da yake can gefe ya kunna lamp din gurin sannan ya fara karantawa.

Dear baby ….

A hankali yake bin handwritten rubutun Hussain yana karantawa har ya gama page din farko ya bude na biyu, a lokacin ne ya fahimci wasiyya ce Hussain ya rubuta zuwa ga abinda Fatima zata haifa. Sai ya rufe diary din yana jin hawaye yana sauka a gaban rigarsa ba tare da yasan lokacin da suka fito daga idanun sa ba. “Yah Allah, kai ka barwa kanka dalilin da yasa wannan abin ya faru, ya Allah ka bani zuciyar dauka”.

Bai kuma bude diary din ba saboda baya jin zuciyarsa zata iya daukan abinda yake ciki, musamman idan ya tuna da cewa shi wanda ya rubuta din bai san cewa wanda ya rubutawa ba zai zo duniyar ba ballantana har ya girma har ya karanta. A dakin ya kwana ranar, amma sai ya kasa daukar komai kamar yadda yayi niyyar daukan very personal abubuwan Hussain. Da safe ya tashi yayi sallah a dakin sannan ya dauki diary din ya je karshen sa ya rubuta date din da Hussain ya rasu sannan ya bude safe box din Hussain, wadda su biyu kadai suka san code din ya saka a ciki ya rufe. For some unknown reason sai yaji yana so ya ajiye diary din, duk da cewa a zuciyarsa yana jin komai dadewar mutuwar Hussain ba zai iya karanta wa ba.

Bayan ya koma part dinsa ya shirya sai ya dauki hanyar kano shi kadai. A kan hanya ne ya yanke hukuncin zai saa sake bincika masa kwararren likita guda daya wanda Ruqayyah zata ke gani amma kuma zai gaya mata da kakkausar murya cewa shi kadai zata ke gani babu chanji, sai su jira kuma suga abinda hali zaiyi.

Yana zuwa gurin likitan dayake dubata ya fara zuwa, dama sunyi waya tun kafin ya karaso, sai likitan yayi masa bayanin cewa sunyi iyakacin kokarin su wajen ganin cewa sun fahimci inda ciwon Ruqayyah ya dosa amma basu fahimta ba, in sunbi ta nan sai kuma suga wani abu daban. “Sai dai in zaku gwada wani asibitin kuma ko kuma ku fitar da ita waje” Hassan ya gyada kai yace “haka ne, mungode sosai. Allah ya saka da alkhairi” daga nan bai kara komai ba.

Yana zuwa gurin su Ruqayyah ya tarar sun shirya, sai dai wai tun da assuba Ruqayyah taki saka hearing aid dinta taki yiwa Sumayya magana duk da ita Sumayyan bat san laifin da tayi mata ba. Shima ya yi kokarin yi mata magana amma ta dauke kanta gefe taki kula shi duk da tasan magana yake yi mata. Tunda yaga haka sai ya rabu da ita suka gaisa da Sumayya wadda already har ta saka hijab dinta tana ganinsa ta dauki jaka, dama duk zaman asibitin ya ishe ta. Sai ya daukar mata daya jakar ya juya kallon Ruqayyah yace “mun tafi” yasan ta fahimci abinda yace, kamar ba zata tashi ba kuma sai ta yunkura ta tashi tana kokarin gyara karfen da aka saka mata a kafa, sai ya ajiye jakar hannunsa ya durkusa yana gyara mata sai ta ture hannun sa, a idonta yaga hawaye ya taru sai yaji babu dadi a zuciyarsa, tabbas ita din abar tausayi ce. Ya dago kai yana kallon ta cikin ido yace “am sorry” ta fahimci abinda yace daga motsin bakinsa, sai ta dauke kai ta mike tsaye ta fara tafiya tana jan kafa har ta bar dakin.

Ya juyo yana kallon Sumayya wadda itama shi take kallo fuskarta da alamun tausayi, tace “kayi hakuri, haka take very edgy. Yau kuma tafi kullum zama worst” ya gyada kai yace “ke zan bawa hakuri ai, zama da Ruqayyah a irin wannan yanayin nata sai ke din. I was selfish dana tafi na barki da ita. Ya kamata ace na zauna tare da ku” tace “babu komai, ai kana kokari ma tunda ba wai baka zuwa bane ba kullum kana kan hanya, sannan kana da abubuwa da yawa a gabanka” yaji dadin fahimtar sa da tayi sai ya dauki jakar itama ta dauki tata suka fita tare, suna hango Ruqayyah har ta danyi nisa, Hassan ya kara sauri dan ya kamota, tare suka isa gurin motarsaya bude mata ya sake kokarin taimaka mata wajen shiga amma taki karbar taimakon nasa ta shiga ita kadai ta zauna tare da rufe idonta.

Sumayya ta shiga baya shi kuma ya tayar da motar, sai Sumayya taga ya kamata tayi masa maganar da tunda tazo kanotake zuciyarta kawai dai bata son ta takura masa ne saboda ganin yadda abubuwa suka cunkushe masa, amma ganin dama tana so ta barta sai tace “yaya Hassan, dama tunda muka zo nake wani tunani” bai kalle ta ba yana kallon gabansa yace “wanne tunanin fa?” Tace “Adam. Nan ne garin su, ban sani ba ko kana da address din gidansu?” Ya dan kalle ta ta mirror yace “gidan su? Wai kina tunanin ya tafi gida ne? After what he went through kina tunanin zai juya ya koma gidan su kawai saboda Hussain ya mutu? Abandoning karatun sa? Abandoning you?” Ya danyi shiru sannan ya dora da “abandoning his religion?” Ta girgiza kanta “no, Adam ba zai taba yin haka intentionally ba. But what if he was forced to go? Maybe iyayensa somehow sun samu labarin inda yake kuma suka zo suka dauke shi forcefully, ina nufin what if he was Kidnapped by his own family?” Hassan yayi shiru, tabbas maganar ta abin dubawa ce, jin yayi shiru sai tayi ajjiyar zuciya tace “nasan hakan is not possible, sorry for bothering you, kawai dai hausawa sunce idan rakumin ka ya bata har cikin kuratandu kake nemansa” bai ce mata komai ba sai taga yayi setting wani address a Google map sannan sai yayi u turn kamar yadda map din ya nuna masa, da sauri tace “ina zamuje?” Yace “let’s check out gidan nasu mu gani” taji wani irin dadi a ranta dan tana ji a jikinta cewa ko da ba’a samu Adam a gidan ba za’a samu wani hint na inda yake.

Ruqayyah tana jin su suna maganganu sama sama amma bata fahimtar su sosai, amma kuma tana so ta san me suke magana akai sai dai kuma duk su biyun fushi take yi dasu, gani take yi kamar basu damu da samun lafiyar ta ba dan har wani murna taga suna yi cewa an sallame ta daga asibiti duk da cewa ko kama hanyar warkewa bata yi ba. Sai ta dauko handbag dinta ta dauko hearing aid dinta ta saka dan taji abinda suke cewa sosai. Sai kuma taji sun daina maganar sai dai taga chanji a yanayin Sumayya kamar tana murna da wani abu, sai kuma ta lura da cewa motar ce take guiding Hassan zuwa inda zasu je. A haka har suka je kofar wani gida suka tsaya, yayi horn sai ga mai gadi ya fito ya tsaya yana kallon motar da alamar rashin sani a fuskarsa, sai Hassan ya fita ya tafi gurin sa, Sumayya tana hango su suna maganganu amma bata jin mai suke cewa sai ta tashi ta fita itama dan zuciyarta ba zata bari ta zauna a mota tana jira ba bayan zata iya samun labarin daya shafi Adam idan ta fita. Tana zuwa taji Hassan yana yiwa mai gadin kwatancen Adam yana cewa shi suke nema, friends dinsa ne. Sai taji mai gadin yace “Joseph?” Da sauri tace “eh shi” sai ya girgiza kansa yace “about five years kenan rabo na da in ga Joseph. Tun daya musulunta ya gudu ya bar gida ban kuma ganin sa ba” Hassan yace “kuma baka da ko labarin inda yake? Ba ka ji masu gidan suna fadar wani abu daya shafe shi ba?” Yace “banji suna fada ba. Amma kusan wata hudu da suka wuce a guy came here yana gaya min wai yasan inda Joseph yake a Kaduna, nace zan shigar dashi gurin mai gida amma sai ya ce shi ba zai shiga ba, yace wata ta turo shi ya fada anonymously, kamar tana son helping parents din ne su same shi” Hassan ya kalli Sumayya wadda itama shi take kallo sai yace “ko zaka iya gaya mana address din daya gaya maka please? Maybe ko zamu same shi acan din? Neman da muke yi masa mai muhimmanci ne sosai” sai mai gadin ya tsaya yana kallon su da alamar rashin yarda, sai Hassan ya zaro kudi masu yawa ya bashi yace yayi cefane, kamar ba zai fada ba kuma sai ya fada, address din gidan su Hassan. “mutumin yace wai aikin driver yake yi a gidan” Hassan yaji kansa ya dau zafi, yana iyakacin kokarin ganin bai nuna tashin hankalin sa a fili ba yace “kuma ka gayawa parents dinsa?” Mai gadin ya gyada kai “sosai. Sun jima suna nemansa, suna sonsa sosai” Hassan yace “yanzu masu gidan suna ina?” Mai gadin yace “mai gidan watansa biyu rabonsa da nan, Madam kuma da yara three weeks ago suma suka bishi, sun tafi state din su, imo”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button