TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta dauko wayarta ta nemo number din Jabir da kyar saboda hawayen da ya lullube mata idanunta ya rage mata gani. Ta kira ta saka a handsfree, yana dauka tace “yaya Jabir ina kwana? Aunty ce take tambayar ko kuna tare da yaya Hassan, bai kwana gida ba” shirun da Jabir din yayi shi ya tabbatar musu da amsar sa, basa tare, Safiyyah ta fara kuka sosai, Aunty ta karbi wayar daga hannunta tace “Jabir ba kwa tare ko?” Ya danyi gyaran murya yana kokarin boye tashin hankalin sa yace “bama tare Aunty, tun jiya da safe dana raka shi yayi interviewing kananan ma’aikatan kamfanin su ban kuma ganin sa ba, na kira wayarsa dai da daddare bai dauka ba sai nayi tunanin ko har yayi bacci lokacin, da wacce motar ya fita?” Aunty ta gaya masa sai yace ” bara in zo gidan, amma ku kwantar da hankalin ku, bara in kira Khalid, maybe gidan su ya kwana kuma maybe bashi da charge” ya fada cikin kokarin sa na ganin ya kwantar musu da hankali amma tabbas shi nashi hankalin ya kai kololuwar tashi. Aunty tace “Khalid? In kwana yayi a gidan su Khalid din kuma bashi da charge mai yasa ba zai karbi wayar Khalid din ya kira mu ya gaya mana ba? Wannan ba halin Hassan ba ne ba. Hassan zaiyi tunanin cewa ya kamata ya kira ya fada. In Hussain ne ba zan damu ba” ta danyi shiru sannan ta dora da tambayar “waye ma Khalid din?”

Jabir yayi saurin kashe wayar,shima baisan wani Khalid ba kawai sunan ne ya fado masa kuma yana son kwantar mata da hankali ko da ta hanyar karya ne. Ya zauna a bakin gado yana dafe kai. Tabbas babu lafiya, Hassan ba zai taba tafiya wani gurin ya kwana ba sannan ya kwashe wayarsa. Ko wanka baiyi ba ya fita, duk inda yasan suna zuwa da Hassan ko wanda yasan suna harka da Hassan sai da ya nema amma babu wanda ya gan shi. A karshe dai ta tafi police station ya sanar wa yan sanda ya kuma basu description din Hassan da kuma motar da ya fita da ita. Anan ya bata lokaci da yawa, saboda police suna fahimtar waye Hassan din suka daukaki maganar kuma abinda suka fara kawowa shine kidnapping. Sai wajen azahar sannan yaje gidan Aunty ya same ta ita da yara sunyi kuka har gode Allah. Ya yi musu bayanin duk abinda yayi sannan yace “ku kwantar da hankalin ku dan Allah. Police sun riga sun shiga maganar nan kuma sun bazu gurin nemansa a lunguna da saƙunan jahar nan, an bada cigiya gidajen rediyo da talabijin duk an baza hotunan sa. An aika asibitoci suma da mortuary duk za’a duba” Zulaihat ta saka kuka tace “mortuary kuma Yaya Jabir?” Ya dafe kansa yace “baya can Zulaihat, dubawa kawai za’a yi amma baya can” tace “to in baya can me yasa za’a neme shi a can?”

Yayi kokarin kawar da maganar ta hanyar tambayar “ina Hussain. Aunty ta dago kai daga kallon charbin hannunta tace “Hussain ya tafi China Jabir. Har yanzu kuma bai kira mu yace mana ya sauka lfy ba, shima bamu san halin da yake ciki ba” ta karasa tana goge hawayen idanunta.

Da yamma a gidan Inna Ade. Inna Ade tana yiwa Ruqayyah kitso Sumayya kuma tana tsefe nata kan. Suleiman da Zunnur suna gefe suna dorawa wasu yara karatu sai ga Baba ya fito daga daki fuskarsa dauke da tashin hankali, hannunsa rike da radiyo. “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Maman biyu kinji wai an sace shi. Yanzu shikenan ya bata sai kace ba mutum ba? Sai kace wata jaka?” Inna Ade ta saki kitson da take yi tana dafe kirji tace “wa aka sace baban biyu? Waye ya bata?” yace “yaron nan da na ce miki na jishi a raina kamar Suleiman, yaron da muka je neman aiki gurin sa, mai sabon kamfanin nan, yan zu ake sanarwa a gidan radiyo wai tun jiya ba’a ganshi ba ana tunanin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa dashi”.

Gabaki daya suka dauki salati. Inna Ade tace ” wannan wacce irin rayuwa ce muke ciki a yanzu? Dan adam ba’a bakin komai yake ba, talaka bai tsira ba mai kudin ma bai tsira ba. Ubangiji Allah ka bayyanar dashi, Allah ka hana azzalumai yin zaluncin su a kansa, Allah ka kare shi ka kare mu baki daya. Allah sarki iyayensa, har naji tausayin su wallahi. Allah ka bayyanar musu dashi in kuma ya mutu Allah ka sa su ga gawarsa” gabaki daya suka ce ameen.

Ruqayyah tace “at least dai ya dana jin dadin rayuwa ko yaya ne, bai zo a bati ya koma a alakoro ba” duk suka juya suna kallonta

A ranar da daddare sai Inna Ade ta samu kanta da saka Hassan a cikin addu’ar ta duk kuwa da cewa bata san shi ba amma tayi masa adduoi sosai da fatan alkhairi duniya da lahira.

A gidan Aunty ma daren ranar basu yi bacci ba, gabaki daya suka hadu a bedroom din aunty suna kai wa ubangiji kukansu. Daga mai sallah sai mai karatu sai mai zikiri a haka har assuba da cimmusu, suka yi sallar assuba sannan suka zauna Aunty tana jero Adduoi su kuma suna amsa mata da ameen har ta gama suka shafa. Suna shafawa ana turo kofar dakin da sauri, suka waiga kusan a tare suna kallonsa kamar yadda yake binsu shima da kallo daya bayan daya yana haki tamkar wanda ya taho a guje tun daga China. Aunty ta mike “Hussain?” Yace “Aunty kidnappers ne suka dauki Hassan, sun kira ni da wayarsa sun kuma turo min hotonsa a daddaure, kudi suke nema, 1billion naira suke nema”.

Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.

Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only

Please duk wadda ta turo min kudi tayi min magana, in baki yi min magana ba ba zan san number din da zanyi adding ba.

Notice
Saura episodes uku mu gama free…….
Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only???????? TAGWAYE ????????

By

Maman Maama

Episode eight : Kidnapped

Hasken da ya shigo ta window ne ya sauka a dai dai fuskarsa. Ya kikkifta idon sannan yayi kokarin amfani da hannunsa gurin tare hasken amma sai yaji ya kasa motsa hannun nasa. Wani irin ciwo jikinsa yake yi masa tamkar wanda aka kwana ana duka da ƙulki. Ya bude idonsa da kyar, su kansu eyelids dinsa sunyi masa nauri kamar an dora wani abu akan su. Idonsa ya sauka akan window din da take kallonsa ta inda hasken ranar yake shigowa. Ya sake rufe idon da sauri saboda hasken daya kashe masa ido amma already yaga tagar kuma a ransa ya fahimci cewa bai san ta ba. A ina yake? Ya sake kokarin motsa hannunsa amma yaji ya kasa, wannan ya tabbatar masa da cewa hannayen sa a daddaure suke sannan ya fahimci ƙafafuwan sa ma haka. Bakinsa ma a like yake ta hancin sa kawai yake numfashi. Ya juya fuskarsa gefe sannan ya bude idonsa yana numfashi sama sama cikin tsoro, a hankali ya zagaye gurin da yake da idanunsa sannan ya fahimci cewa toilet ne, ya kuma fahimci shi kadai ne a gurin. Sai a lokacin tunanin abinda ya faru dashi ya dawo masa.

Farkon abinda ya fara fahimta shine har ya kwana ya hantse kenan, tashin hankalin sa shine wanne hali yan’uwansa suke ciki? Wanne hali Hussain yake ciki? Shin kidnappers din sunyi contacting dinsu ko kuwa? Abu na biyu daya tuna kuma shine bai yi Sallah ba, bai yi magrib ba bai yi isha ba baiyi assuba ba.

Ya ja ƙafafuwan sa ya lankwasa su yana jin tamkar zasu karye saboda sandarewa da suka yi ga kuma azabar ciwo da suke yi masa, ya yi kokari ya jingina bayansa da jikin bango sannan yabi bangon ya mike zaune yana jin jikinsa gabaki daya yana amsawa saboda ciwo, ciwon tafiyar da akayi dashi a booth din mota, daure shin da akayi for hours da kuma kwana da yayi akan tantagaryar sumunti. Ya sake karewa ban dakin kallo yaga bashi da wani girma sosai daga kofar da take a rufe sai yar karamar tagar da take can sama a rufe itama da glass. Kasa kasa yake jin muryoyin mutane yana shigowa ta kofar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button