TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Hassan bai dauko hanyar gida ba sai da biyar na yamma ta wuce, saboda yasan masifar Ruqayyah zai je ya tarar a gidan. Sun gama komai yau da lawyers dinsa da kuma sell agents, anyi pricing komai kuma dama tun jiya daya sanar da muradin sa na siyar da kamfanonin already har labarin ya iske manyan yan kasuwar kasarnan kuma sun fara nuna interest din su akai. Shi dama ya fi son ya siyar wa da yan kasuwa yadda zasu cigaba da running business din ta yadda babu wanda zai rasa aikin sa a cikin ma’aikatan kamfanonin, in suna bukatar service dinsa shima zai cigaba da yi musu aiki yana karbar albashin sa kamar yadda ya saba, idan ma kuma basa bukatar sa zai nemi wani aikin kuma yasan insha Allah ba zai sha wahala ba kafin ya samu in akayi la’akari da experience dinsa da kuma links din da yake dashi a cikin masu hannu da shuni na kasar nan. Sannan kuma a account dinsa yana da kudin da yake tunanin zasu rike shi daga yanzu zuwa lokacin da zai samu aikin.
Gurin Aunty ya fara shiga kamar yadda ya saba, ya gaishe ta sai yaga fuskarta da damuwa, bata bashi abinci ba kamar kullum saboda ta san matarsa ta dawo, sai shi ya kira Zulaihat yace ta kawo masa, ya fara ci sai Aunty tace “Hassan ya akayi baka gaya min yau zaku tare a gidan Hussain ba? Ai da sai in tura wadannan yaran su taya ku shirya kayan ku ko? Ko ba haka ba ma fadar ai tana da dadi akan ace sai dai inji a gurin yan aiki” ya ji abincin bakinsa yana kokarin shake shi, da kyar ya hadiye shi ido a waje yace “tarewa kuma? Gidan Hussain kuma?” A take Aunty tabbatar da abinda take zargi, Hassan bai san abinda Ruqayyah tayi ba kuma dama tayi tunanin haka dan babu yadda za’a yi Hassan ya aikata haka ba tare da ta sani ba dan shi Hassan baya taba yin komai sai ya tuntube ta first.
Chokalin hannunsa ya ajiye sannan ba tare da yace komai ba ya mike da sauri ya fita daga gidan. Sai kuma Aunty taji babu dadi a ranta ta ji kamar ta hada shi da Ruqayyah ne.
Yana shiga gidan ya hango kofar part din Hussain a bude ga mutane suna ta kai komo, da sauri ya shiga ciki ransa a matukar bace, yaran da ya tarar a palon kasa suka fara matsawa suna bashi guri saboda ganin yana yin sa, yace “ina take?” Suka nuna masa sama da sauri, ya hau da sauri yana hada stairs guda bibbiyu a lokaci daya sannan ya doshi wing din Fatimah dan yasan na Hussain a rufe yake. Bai taba shiga ba saboda duk haduwar da suke yi da Fatima a part din Hussain ne ko kuma a palon kasa sai ranar daya ganta a gym, yayi sauri ya kawar da tunanin daga ransa dan bama ya son tuno abinda ya faru a ranar. A can kuryar Bedroom din Fatimah ya tarar da Ruqayyah tana zaune akan gadon da ba nata ba hannunta rike da wata yar karamar box din da ba tata ba tana jera wasu kaya a ciki, gefenta Hussain karami ne yana kwance so innocently yana tsotsar hannunsa.
Yana kokarin saita numfashin sa yace mata “me kike tunanin kina yi?” Ta juyo tana kallon sa sannan ta mike tsaye tace “sannu da zuwa mijina” yace “me kike tunanin kina yi? Wa ya baki izinin shigowa nan har da kwaso kaya? Ki zo ki fita daga gidan nan” tace “na shigo ne saboda gidan mijina ne, kuma fita ta ba yanzu ba, am here to stay. Idan kai baka so mu muna so ni da yayanka, zaka iya cigaba da zama a can gidan duk sanda kake bukatar ganin mu sai kazo ka ganmu anan. Amma mu anan zamu zauna” yace “ni nine mai gidan, kuma ni nace ki fita, ba’a nan nayi niyyar ki zauna ba kuma ba’a nan zaki zauna ba, ki fita ko kuma in saka a fitar dake. Na gama magana” ya fada dead serious, ya juya zai fita daga dakin sai tace “ni kuma ban gama magana ba, in fact, ban ma fara magana ba tukuna, in har kana ganin zaka iya sakawa a zo a fitar da matarka da yayanka daga cikin gidan ka bismillah. Amma ni ba zan fita ba kuma ba zan barka ka bayar da ko kwandala daga cikin kudin nan ba” ya juyo yana kallonta yace “and how are you going to stop me? Taya zaki hana ni yin abinda na yi niyya?” Itama ta juyo tana kallon sa tace “da ace kasan abinda nayi kafin in samu kudin nan da baka tambaye ni yadda zanyi in hana ka rabar da su ba” ya kara matsowa cikin mamaki yace “kika samu? Yaushe kika samu? Me kuma kika yi? What have you done?” Ta danyi murmushi tace “komai, from the beginning to the end” sai ya dakata a tafiyar da yake yi, a lokaci daya yana realising truth, tun farko ba shi ta aura ba dukiyar da tayi tunanin tasa ce ta aura, daga baya kuma da ta san ba tasa bace ba ta zauna dashi ne saboda tana tunanin zai samu, tana burin ya samu. Zuciyarsa tayi sinking a cikin kirjinsa, ji yayi kamar ta koma cikinsa ta bar kirjinsa. Cikin muryar da yaji kamar ba tashi bace ba Yace “me yasa kika taimaka min ranar nan? Me yasa kika yi saving rayuwata?” Sai ta sake wani murmushin, she hates breaking his heart amma yau ranar gaskiya ce, dole ta fada masa dan ya san dalilin da yasa zata aikata abinda ta riga tayi niyyar yi.
Tace “Baba yaje neman aiki gurinka, sanda aka sace ka sai ya bamu labari, shi ya dauka kaine mai kamfanin dan haka ce mana yayi kai ne mai H and H. Muna ta following labarin batanka saboda Baba ya damu da kai sosai, and then sai gaka a toilet din mu, daga yanayin ka da kayan jikinka nayi tunanin kai ne shi yasa na saka rayuwata a hadari na taimaka maka dan inaso ka rike taimakon da nayi maka a ranka kar ka manta, dan ina so ka biya ni. Na dauka wasu kudi zaka bani wanda zai fitardani daga talauci sai kai kuma ka yi Maganar aure na and I thought auren mais even better dan maybe abinda zaka bani din zai iya karewa amma in na aureka komai naka ya zama nawa. That’s why I married you”
Ya dafe kirjinsa yana jingina da jikin bango dan ji yake yi kafafuwan sa kamar ba zasu iya daukarsa ba. Yana girgiza kansa yace “kina nufin ba kya sona Hassana? Kudina Kika aura bani ba Hassana?” Ta bata rai tace “I can’t say gaskiya, ban sani ba ko zaman da muka yi da kai na fara sonka amma ban sani ba but abinda na sani shine bana son wannan sunan da kake gaya min, I hate it, kullum kuma ka gaya min raina baci yake yi” ya bude baki zaiyi magana amma sai ya kasa, his heart breaking into pieces, bleeding, kunnuwan sa har kara suke yi masa dan suna so su daina jin maganganun Ruqayyah amma sai ta cigaba da cewa “nasan heart dinka zata yi breaking kaima kamar yadda tawa tayi breaking lokacin da aka kawo ni gidan nan na fahimci cewa ba kai ne mai kudin ba, na fahimci cewa you are just your brother’s puppet. But I thought zan iya juya ra’ayin ka tunda naga kana sona, I thought zan iya hada ka da brother din naka yadda zaka kwasar mana wani abu daga cikin dukiyar sa da muma mu kafa kanmu amma kaki bani hadin kai, saying wai kafi son sa akan kowa”.
Hassan ya tuna da maganganun da Ruqayyah tayi ta gaya masa akan Hussain, akan Fatima, wato duk karya ce kenan, duk da ta hada su ne, wato duk dan taci dukiyar Hussain ne. Ya tuno maganar Baba, ya tuno maganar Hussain kamar yanzu yake gaya masa “me yasa bata je ta kira iyayenta sun taimaka maka ba sai ta zabi ta kama katanga ta haura?” Sai yau Hassan ya samu amsar sa.. yace “bayan wannan kuma sai me kika yi?” Tayi shiru tana kallonsa, yace “kina da hannu a gurin batan Adam?” Ta juya hannu “what does it matter? Sai me? Ni ba zan bari yaruwata ta auri wannan inyamurin drivern ba” yace “ke kika aikawa iyayensa suka zo suka tafi dashi” ta juya idonta, me za’a yi mata in an sani? Karkarinta Sumayya tayi fushi na wani lokaci da zarar kudi sun zauna kamar yadda take saka rai shikenan komai zai dawo normal tsakanin su tace “eh ni na aika musu, me za’a yi min?” Yace “you are not human being Ruqayyah ke shaidaniya ce. A devil in human form”.