TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Tunda ya fito daga gidan Hussain yake tambayar kansa dalilin da yasa haka ta faru dashi, ina carefulness dinsa ya tafi lokacin da ya zabi Ruqayyah a matsayin matar aure, ina smartness dinsa da dabarar sa da hangen nesan sa suka tafi, me yasa yayi failing akan abinda yafi komai muhimmanci a rayuwarsa? Ya ninke takardar a hankali ya ajiye a tsakiyar su shida Baba, ya kasa mikawa baban, sai Baba ya saka hannu ya dauka ya warware yana kallonta duk da cewa ba gane rubutun yake yi ba, dai kuma ya mikawa Sulaiman yace “karanta muji” sai Sulaiman ya karanta a fili, Hassan ya sunkuyar da kansa yana jin nauyin Baba amma ko kadan baya jin wani abu mai kama da regret na saki ukun da ya yiwa Ruqayyah.

Inna Ade ta fara kuka, Baba ya dago kai yace “ina rokon ka ka gaya min abinda tayi maka, saboda ina son insan muma iyayenta abinda ya kamata muyi mata” Hassan yana girgiza kansa yace “zuciyar ku ba zata iya dauka ba Baba, nima tawa zuciyar yanzu kuka take yi, Ruqayyah ta riga tayi mata mikin da ba zai taba goguwa ba” Baba yace “tunda har kana numfashi hakan yana nufin zuciyarka ta dauka, kai da ba dolen ta ba ballantana mu da muka haife ta, mu da ba zamu taba iya chanjata ba, ka gaya mana dan Allah dan musam ta yadda zamu taimaka mata”.

Sai Hassan ya basu labari, labarin duk abinda Ruqayyah ta gaya msa da bakinta cewa tayi he told them everything har labarin abinda tayi wa Adam da kuma zargin da yake na cewa abinda tayi shine sanadiyyar batan Adam din. But duk wannan ba shine dalilin da ya saka ya sake ta ba, dalilin da ya saka ya sake ta shine abinda tace zata yi, sharrin da tayi ikirarin zata yi wa brother dinsa duk kuwa da cewa yana cikin kabarinsa a kwance, zata bata masa suna ta kuma bata nasabar dan ta data haifa da kanta duk dan saboda kudi. Yana tsoron cewa babu abinda ba zata iya yi ba saboda kudi.

Inna ta kasa juye labarin sai ta tashi ta shiga daki tana kuka, Sumayya da take tsaye a kofar dakinta tun shigowar su tana jin abinda suke cewa ta juya ta koma daki ta turo kofa, sai ta zauna akan gado blindly tana kallon bango sannan sai ta dauko wayarta ta nemo number din Ruqayyah ta saka ta a blacklist sannan ta goge ta daga cikin wayar ta, sai kuma ta ajiye wayar ta kwanta tana tunanin hanyarda zata bi ta tafi imo…

A palo Baba da Sulaiman suna zaune har Hassan ya gama basu labarin duk abinda Ruqayyah tayi. Da kyar yake magana amma bai yi shiru ba sai da ya kai aya sannan yace “kayi hakuri Baba, zaman da nayi ma da Ruqayyah a baya da ace zan iya dawo da hannun agogo baya da banyi shi ba har na hada zuri’a da ita ba, da ace zan mayar da rayuwata baya da nabi zabi irin na Hussain, na zabi mace kamar Fatima ba kamar Hassana ba, na zabi wayayyiya mai zurfin ilimin boko yar gidan masu kudi mai budadden ido irin Fatima ba irin Ruqayyah ba, wata kila da nayi haka da yanzu ban samu kaina a halin da nake ciki yanzu ba” Baba ya girgiza kansa yace “tabbas kayi kuskure a gurin zaben matar aure, amma ba wannan ne kuskuren ka ba. Arzikin mutum, zurfin ilimin bokon sa, yanayin al’ummar daya taso a cikin ta, shekarunsa ko kuma wayewar sa basu suke nuna halayyar sa ba. Ita halayyar mutum da ita ake haifar sa, su duk wadannan abubuwan dana lissafa suna taimakawa ne gurin kara wa ko rage karfin halayyar mutum. Ana samun nagari a cikin kowanne kaso na al’umma kamar yadda ake samun bata gari a cikin kowanne kaso da al’umma. Ana samun shaidanin mutum a cikin malamai kamar yadda ake iya samun salihin mutum a cikin shaidanu. Dan mun kasance malamai hakan baya nufin cewa yayan da zamu haifa lallai zasu kasance na gari ba, mu dai iyakacin mu mu bada ilimi mu bada tarbiyya amma ita shiriya ta Allah ce, Allah ne kadai zai iya shiryar da bawansa a lokacin da yaso. Kamar kuma yadda na gaya maka cewa yana yin guri da yanayin al’ummar da mutum ya samu kansa a ciki yana karawa ko rage halayyar mutum, wannan shine abinda ya faru da Hassana. Tun farko Hassana halinta ba mai kyau bane ba, ni da mahaifiyar ta mun sani kuma kamar yadda mahaifiyar ta take yawan fada ita Hassana kamar harabawa ce ubangiji yayi mana dn yaga yadda zamu yi da ita, kuma munyi iyakacin kokarin mu, a inda muka yi kuskure shine da muka biye mata muka hada auren ku kai da ita, komawar ta cikin ku da shiga irin rayuwar ku da bude idon da t kara yi da duniya shi ya kara lalata mata halayyar ta, shi yasa har ta zama abinda ta zama. Wata kila da mun barta a gabanmu, ko kuma mun samu wani mijin wanda ba irin ka ba, mai rufin asiri dai dai gwargwado mun aura masa ita da ba zata ga dukiya irin taku ba har ta saka a ranta sai ta mallake ta. Wannan shine abinda naso in nunawa mahaifiyar ta a lokacin da kake neman aurenta, amm ita kuma sai tayi tunanin idan bamu bawa Ruqayyah abinda take so ba shine zata kara lalacewa. Wannan shine kuskuren mu, wannan shine inda muka fadi jarabawar mu. Amma hakan ba wai yana nufin shikenan mun hakura ba, zamu cigaba da kokarin ganin mun gyara kuskuren mu, abinda zamuyi kuma a yanzu shine zamu barta da duniya, zamu barta ota da kanta ta gane cewa abinda take yi ba dai dai bane ba muyi fatan kuma komai ba jima komai ba daɗe zata yi nadama za kuma ta nemi yafiyar wadanda ta zalunta. Ta haka ne kadai zata samu rahamar ubangiji. Ni ba zance kayi wa Hassana komai ko ince kar kayi mata komai ba, in ka ga dama zaka iya hada ta yan sanda kace ga ikirarin da tayi na cewa zata yiwa dan uwanka kazafi akan dukiyar sa, in kafa dama zaka iya duba ya’yan da suke tsakanin ku ka barta da duniya kamar yadda muma zamu barta din. Duk zabin ka ne.”

“Ina so ka sani, a yanzu ima tsananin jin kunyarka saboda abinda yata ta cikina tayi maka duk kuwa da irin kyautatawar ka a garemu. Sannan kuma ina so in tabbatar maka da cewa Ruqayyah ta aikata abinda ta aikata ne kawai saboda halin ta ne haka. Bawai saboda ta fito daga gidan talakawa ba. Ina rokon ka idan ka amince ina son ka auri SUMAYYA a madadin Ruqayyah. A lokacin ne zaka gane abinda na fada maka ranar nan, a lokacin ne kuma zaka gane abinda nake gaya maka yau”

Hassan ya bude ido yana kallon Baba da mamaki yace “Sumayya kuma Baba? Sumayya ai ƴar uwar Ruqayyah ce ciki daya ta yaya zan iya aurenta bayan ita Ruqayyan tana da rai?” Baba yayi murmushi yace “ni dai iya kacin sani na babu wata aya ko wani hadisi daya haramta aure a tsakanin ku a irin wannan yanayin. Abinda aka haramta shine hada yan uwa a aure su a lokaci daya, sai dai alkunya tana sakawa sau da yawa a ki yin irin wannan auren dan shi musulunci addinin zaman lafiya ne, amma mu a yanzu babu wata alkunya wadda zamuyi wa Hassana. Na baka auren husaina”

Hassan ya cigaba da girgiza kansa, abubuwan sunyi masa yawa, zuciyarsa ba zata iya dauka ba, kansa ya toshe a yanzu ba zai iya yin tunanin komai ba. Sai Baba yace “na sani, na san yanzu ba zaka iya bani amsa ba kuma nima bana son ka bani amsar a yanzun, kaje kayi tunani, ka nemi zabin Allah kayi addu’a, na baka daga nan har zuwa shekarar da Sumayya zata gama karatun ta na jami’a, idan har zuwa lokacin ba kaji zaka iya auren ta ba shikenan, idan kuma kaji zaka iya to alkawarin da nayi maka yana nan na baka ita ko bayan raina”. Still Hassan bai ce komai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button