TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai Baba ya aika Sulaiman ya kira Inna, ta zauna a kusa dashi idanuwan ta da alamar kuka sai yace “ki zama shaida, ko bayan raina in Hassan yazo neman auren husaina na bashi ita.” Ta gyada kai tace “Allah yasa haka shi yafi musu alkhairi” sai kuma ya mika mata takardar sakin Ruqayyah yace “ga wannan ku tafi tare da Sulaiman gurin Hassana ki kai mata, sannan ki gaya mata in ji ni ni ubanta Malam Yusuf mai gadi nace ta baro gidan nan a yanzu ta taho gidana, kuma ban amince ta dauko koda tsinke na daga abinda yake gidan ba tunda sanda ta shiga bata shiga da ko tsinke ba. Wannan shine umarni na, idan kuma taki bi ki gaya mata nace babu ni babu ita har abada, ke ma babu ke babu ita har abada, babu ita babu duk kan abinda muka haifa a duniya, har sai ranar da tayi abinda nace sannan kuma ta nemi dukkan wanda ta batawa ta nemi gafarar su suka yafe mata to a lokacin nima zan yafe mata”

Inna ta fara kuka tana son ta rokar wa Ruqayyah gafara a gurin mahaifinta amma sai ya daga mata hannu yace “wannan umarni ne na baki a matsayi na na mijinki, sai ki zaba ko ki bi umarni na kiyi abinda nace ko kuma ki biye wason da kike yiwa yarki ki bita gidan da take son kwata daga hannun masu shi ku zauna tare” wannan yasa inna ta mike dan tasan aljannar ta tana tattare da bin umarnin mijinta kuma tasan wannan wata sabuwar hanya ce daya biyo da ita dan ganin Ruqayyah ta dawo kan hanyar dai dai. Amma a ranta tana tunanin abinda Ruqayyah zata zaba, tsakanin su iyayenta da yanuwanta da kuma dukiya.

Kafin Inna ta kai bakin kofa Sumayya ta fito daga dakinta ta riga ta fita, duk tana jin maganganun da Baba yayi har maganar bada ita ga Hassan da yayi taji amma ba wannan ne a gaban ta ba yanzu, abinda yake gabanta shine tana so taga Ruqayyah, tana so ta gaya mata abinda yake zuciyarta face to face. A cikin Napep din Baba suka tafi, babu wanda yayi wa wani Magana a cikin su har suka je gidan, direct part din Hussain suka dosa dan sun san tana can kamar yadda Hassan ya fada. Ai kuwa a can din suka same ta rashe rashe a palon Fatima tana ta wasada yaranta kamar bata aikata komai ba. Sai dai ganin su da yanayin fuskokin su ya saka taji zuciyarta ta tsinke, wato Hassan karar ta ya kai gida ko? Zai zo ya same ta ne.

Tayi kokarin mikewa, “Inna sannu da zuwa. Ban san zaku zo ba ai. Ga guri zauna” Inna tace “a ina zan zauna Ruqayyah? Akan kujerar da ba taki ba? A cikin dakin da ba naki ba a kuma gidan da ba naki ba? Me kika mayar da rayuwar ki ne Ruqayyah? Yaushe lalacewar ki har ta zama haka ban sani ba?” Ruqayyah ta bude baki zata yi magana sai kuma ta rufe, bata jin ko ma menene zata gayawa Inna zata fahimta tunda ita duk bata san komai ba a game da jin dadin rayuwa ba.

Sai Inna Ade ta mika mata takardar da Hassan ya rubuta mata tace “gashi inji mijinki” ta karba amma bata bude ba, a zuciyarta taji ta san menene a ciki, sakinta Hassan yayi, wayo threats din ta baiyi ba kenan tunda har ya sake ta, wato taje ta fadi duk abinda zata fada kenan yake nufi ko? Lallai kuwa zaiyi nadama mai girma. A can kasan zuciyarta taji sunan bazawara ya karu akan sunan kurma kuma gurguwa. Duk sunayenta ne ita kadai. Sai kuma taji wata magana da tafi sauran zafi a gurinta. “Baban ku yace ki taso ki biyomu mu tafi gida tare, tunda can shine gidan uban ki ba nan ba. Yace kuma kar ki sake ki dauki ko chokali a cikin gidan nan tunda ba ubanki ne ya siya ba” Ruqayyah ta zaro ido waje tana girgiza kai, zuciyarta tana kaduwa, ba zata iya ba, after all what she went through ba zata iya yin asarar duk wannan dukiyar data samu bayan ta aikata abubuwa da yawa kafin ta same ta ba, biyu bau kenan, noo ba zata iya ba. She can’t imagine ta koma gidan su da zama, gurguwa, kurma, bazawara kuma talaka? Impossible.

Inna Ade ta maimaita “ki tashi ki dauko mayafin ki mu tafi Ruqayyah. Ki duba ki karanta ki gani saki uku mijinki yayi miki” Ruqayyah bata motsa ba, Inna tace “Baban ku yace in baki taso kin biyo mu gida a yanzu ba, babu shi babu ke har abada, babu ni babu ke har abada, babu ke babu yanuwanki har abada ko kuma har sai kinyi nadamar abinda kika yi kuma kin nemi yafiyar duk wadanda kika batawa sannan muma zamu yafe miki”.

Hawaye suka fara bin fuskar Ruqayyah, ta kama hannun Inna “Inna dan Allah ki fahimce ni kije ki fahimtar da Baba, ni ba zan iya komawa waccan rayuwar ba saboda yanzu ba zan iya yin irinta ba, na saba da wannan rayuwar, ga kuma nakasa da ta same ni, inna da wanne zanji? Da nakasa ko da saki ko kuma da juya min baya da kuke kokarin yi? Dan Allah ki fahimce ni Inna, kudin nan da nake fafutukar samu ai ba wai dan ni kadai bane ba, dan kune gabaki daya, yadda muka sha wahala a baya nake so muji dadi a gaba, zuwa aikin hajji duk shekara, su Zunnur su tafi kasar waje suyi karatun su a can su zama likitoci, Sumayya sai mijin data zaba zata aura, mazan ma ai kudi suke bi kamar yadda matan suke bin kudi” Inna ta kwace hannunta tana kukan takaici tace “ban taba tunanin abinda na haifa a cikina zai yi wannan tunanin ba, kina son Sumayya ta samu miji kuma kika korar mata yaron da yake sonta? Kika yi sanadiyar da yanzu yana can a hannun ahlul kitabi suna kokarin mayar dashi addinin su? A hakan kike sonta, wannan ce taki soyayyar?” Ruqayyah tayi sauri ta kalli Sumayya,bita ta manta ma ta gaya wa Hassan wannan maganar, dan bata yi niyyar gaya masa ba saboda baya son abinda zai bata tsakanin ta da Sumayya dan tana ganin ko duk duniya zasu guje ta Sumayya ba zata taba guje mata ba. Amma yanayin data gani a fuskar Sumayya ya saka taji zuciyarta ta tsaya da bugun da take yi.

Inna tace “na tafi Ruqayyah kamar yadda babanki ya fada zabi ya rage naki. Ko ki biyo ni ko kuma ki cigaba da zama ki cigaba da rayuwa amma ba tare da mu ba. Kuma babanki ya bawa tsohon mijinki damar yayi miki duk abinda yayi niyyar yi miki babu ruwansa, ko da kuwa abinda zaiyi mikin yana nufin ya hada ki da police ne” ta juya zata tafi sai Ruqayyah ta kuma kamo hannunta tace “dan Allah inna kiyi hakuri, ki rokar min Baba ya bani lokaci muyi magana da Hassan komai zai dai dai ta. Dan Allah Inna baku san wahalar da nasha ba kafin in samu kudin nan baku san irin abinda nayi ba kafin in samu kudin nan bazan iya hakura dasu ba tare da nayi iyakar kokari na ba” Inna ta kuma kwace hannunta tana goge hawayen ta tace “abinda kika yi ai duk tsohon mijinki ya gaya mana, lokaci kuma mun baki lokaci daga yanzu zuwa sanda zamu bar gidan nan ki dauko mayafin ki mu tafi tare, in baki yi haka ba kuwa to na gaya miki abinda zai biyo baya kuma da gaske muke” ganin Ruqayyah bata da niyyar tahowa ya saka Inna ta kama hannunta tana janta zata fitar da ita da karfi amma Ruqayyah taki fita, ganin Inna tana kokarin jin ciwo ya saka Sulaiman ya kama hannunsu ya raba su sannan ya ja Inna ya fita da ita tana ta kuka, aka bar Ruqayyah itama da take kukan tana kiran Inna da kuma Sumayya da tun da suka shigo take tsaye tana kallon su. Sai bayan fitar su sannan Sumayya ta matso gaban Ruqayyah, Ruqayyah tayi sauri ta rike hannunta tace “Sumayya kibi bayan Inna kije kiyi musu bayani yadda zasu fahimta, kudin nan fa har dasu za’a ji dadinsa, su bani lokaci in samu in yi Magana da Hassan ni na san abinda zan gaya masa komai zai dawo dai dai” Sumayya tace “kin tuna da ranar nan? Ranar da na yi miki warning cewa ki fita daga harkar Adam?” Ruqayyah tace “zamuyi wannan maganar daga baya, yanzu maganar Inna da Baba sunyi fushi dani akeyi akan maganar da Hassan ya gaya musu ba tare ma da sun tsaya sunji nawa side din ba. Kije ki basu hakuri kice zanzo gidan zamuyi magana sosai” Sumayya tace “kin tuna warning din da nayi miki ko baki tuna ba?” Ruqayyah ta ce ” ta tuna kince kar in kara, na daina yanzu ba shikenan ba?” Sumayya tace “da nace kar ki kara dai kika ce in kin kara mai zanyi miki? To yanzu zan baki amsa” Ruqayyah tana tsaye tan kallon t da mamaki tace “me zaki yi min?” Sumayya tace “babu ni babu ke har abada. Shine abinda zanyi miki” daga nan ba tare da ta kara cewa komai ba ta juya ta bar palon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button