TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800
bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa
Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin AllahLife Afresh
Bayan Hassan ya rufe kofar gidan sai ya jingina da jikin kofar yana mayar da numfashi, tabbas shi kansa yasan zuciyarsa tana son Ruqayyah amma dole ya barta saboda shi dai bai taba haduwa da shaidanin mutum irinta ba, ba zai cigaba da zama da ita ba kuma ba zai bar yayansa a hannunta ba for his sake and for the sake of his children. Har cikin ransa yasan wannan hukuncin da ya yanke shine dai dai duk da wani bari na zuciyarsa yana nuna masa kamar bai yi wa yayansa adalci ba daya raba su da mahaifiyar su, sai kuma ya gaya wa kansa “ita ta zabi haka, ita ta zabar musu haka”.
Gidan Aunty ya shiga dasu, wani yaro ya daukar masa akwatin da aka zubo musu kayansu. Aunty tana zaune palo tana kallon wa’azi taji sallamar sa, ta daga kai da sauri tana kallonsa rabe rabe da yara, cikin kwanakin da bata ganshi ba sai taga fuskarsa ta fada ciki, manyan idanuwan sa sun kara fitowa waje sannan fatarsa ta kara duhu. Tabbas bayan rashin Hussain akwai wani bakon al’amari da yake damunsa. “Allah ga dan marayan nan Allah ka tausaya masa” ta fada a ranta lokacin da yake zama a gabanta yana mika mata Hussain, Yusuf da Aminu kuma suka fara rige rigen hawa jikinta. Hassan ya gaishe ta ta amsa tana shafa kan tagwayen da tun da aka haife su take jin soyayyar su a zuciyarta tamkar irin son da tayi wasu Hassan sanda suna kanana.
Ta kalli akwatin kayan da aka ajiye a can gefe tace “gidan Sa’adatu zaka kai su ne? Ba kwanan nan suka dawo ba?” Yace “ba can zan kai su ba, nan na kawo su, anan zasu cigaba da zama” sai tayi shiru bata ce komai ba amma tana ji a jikinta cewa wani abin ya faru da ma’auratan. Sai tasa baki ta kira Zulaihat tace “dauki yaran nan ki tafi dasu sama zamu yi magana da yayan ku” Zulaihat ta amsa mata sannan ta gaishe da Hassan, itama tana lura da lalacewar daya sake yi. Sai da suka tafi sannan Aunty tace masa “ina jin ka, wanne dalili ne ya saka zaka raba uwa da yayanta ka kawo min su har da jariri?” Ya gyara zamansa yace “Aunty abubuwa da yawa sun faru wadanda baki san su ba, akwai abubuwa da yawa wadanda ban fada miki ba, kuma nayi haka ne saboda ina gudun bacin ranki musamman a yanzu da lafiya bata ishe ki sosai ba, kuma a yanxun ma ina so ki yi hakuri kar ki tashi hankalin ki akan duk wani abi da xan gaya miki, ki sani, tashin hankalin ki ba zai chanza komai ba tunda hannun agogo baya taba dawowa baya, da yana dawowa dana dawo dashi na chanja abubuwa da dama, da na chanja wasu choices da nayi a rayuwata. Amma kwantar da hankalin ki zai taimaka sosai wajen kwantar min da nawa hankalin, zai taimaka mana wajen hada kai mu samar da matsaya a lamarin mu”
“Abu na farko da bamu gaya miki ba shine tun lokacin da Hussain ya a da rai, tun lokacin da aka sanar dashi surgery din sa was not successful sai ya raba H and H biyu ya bani rabi, tunanin sa a lokacin shine kar in ya mutu Fatima ta haifi namiji ya kasance bamu da komai a cikin dukiyar sa, ban fada miki ba tun a lokacin saboda bana son ki san cewa Hussain bai warke ba”
“Abu na biyu da ban fada miki ba shine na siyar da rabin H and H, share din da Hussain ya bani tun yana da rai”
Aunty ta bude ido “ka siyar? Saboda me? Wa ka siyar wa? Me zaka yi da kudin?” Bai ce komai ba har tayi shiru tana mayar da numfashi sai ya kuma cewa “Aunty dan Allah kar ki tayar da hankalin ki, zan miki bayanin komai” sai data jera ajjiyar zuciya sannan tace “ina jinka” ya cigaba..
“Umar ne ya siya, yayan Fatima. Dalilin dabyasa na siyar kuma saboda tun a lokacin da Hussain ya bani nayi alkawarin in har ya kasance bai rayu ba to ni kuma ba zanci wannan kudin ba, zanyi masa sadaka dasu ne”
“Abu na uku da nayi ban gaya miki ba shine an raba gadon Hussain. Bana so in gaya miki dalilin da yasa na sa ayi rabon da gaggawa saboda bana so ki tashi hankalin ki har sai nayi solving problem din. Problem din kuma shine Ruqayyah” ta bude ido “Ruqayyah kuma? Menene hadin Ruqayyah da rabon gadon Hussain?” Sai kuma ta tuno da tarewar da Ruqayyah tayi a gidan Hussain, sai tayi shiru, sai ya dauko mata labari a nutse cikin hankali ya gaya mata duk abinda Ruqayyah tayi da wanda tace zata yi, da kuma shi abinda yayi. Aunty tayi mamaki kwarai da gaske, maganar kuma ta taba ta sosai musamman iƙrarin da Ruqayyah tayi na tarwatsa sunan Hussain, Hussain din da baiyi mata komai ba a rayuwarta dai alkhairi, amma yadda Hassan ya bi da maganar da matakin daya dauka ya saka tashin hankalin nata bai tsananta ba. Tace “tabbas Ruqayyah tayi asara Babba, tabbas rabata da yaran nan shine abinda yafi dacewa dan kamar yadda kace ita din guba ce, ita kuma halayya naso take yi sai wanda Allah ya tsare” Hassan yace “haka ne, wannan yasa na datse igiyoyin aure na da ita, duk ukun” Aunty ta dafe kai tana salati, yace “kiyi hakuri Aunty, bana jin zan bar duk wata alaka tsakani na da wadda zata iya yiwa Hussain wannan sharrin. Yaya Allah ya riga ya bani tare da ita, amma zanyi iya kacin kokari na wajen nesanta su da ita duk da cewa ba zan iya chanja musu uwa ba” Aunty ta jimanta abin, ita iyayen Ruqayyah take ji, mutanen kirki sai dai sunyi asarar haihuwar Ruqayyah. Amma kuma ta fahimci dalilin da yasa Hassan ya bar mata kudin daya gada daga Hussain tare da gidan Hussain din da take haƙo, wannan kadai zai koya mata darasin rayuwa, ko da badan ita ba ko dan ƴaƴanta dole zasuyi fatan Allah ya shiryeta.
Sai kuma Hassan ya mika mata wasu takardu daya fito dasu daga aljihunsa yace “ga wannan, kason su Hassana ne na daga gadon Hussain, ban siyar ba yana nan a matsayin share a kamfanin H and H wanda a yanzu yake a ƙarƙashin Umar da Ruqayyah. Zabin sune suyi duk abinda suke so suyi dashi” ta daga tana kallon rubuce rubucen jikin takardar, maganganu irin na lauyoyi da tasan ko ta karanta ba gane wa zata yi ba sai ta ajiye tana kallon Hassan tace
“kai kuma fa? What are you going to do?”
Ya rufe idonsa ya bude, wannan tambayar ta Aunty is a one million dollar question, me zaiyi shi kuma? Ina ya dosa a rayuwa? Ya girgiza kansa, “ban sani ba Aunty, a yanzu haka ban san menene matsayi na ba, ban san me zanyi next ba. Ki bani shawara dan Allah” sai tayi shiru tana tunani sannan tace “you need to start afresh, ka tattara duk tabbunan baya ka tura su bayanka ka manta dasu ka kuma rungumi gaban ka. Ba zaka iya mantawa da baya ba na sani amma ina so ka saka ta a wani bangare na zuciyarka wanda ba ko da yaushe kake bude gurin ba. You need to be strong for your children sake, for our sake gabaki dayan mu” sai ta mika masa takardar ta ya bata tace “ka karbi wannan ka kafa naka business din, forget about H and H, ka siyar da share din su Hassana suma, mun rasa Hussain da iyalinsa baki daya mun hakura babu abinda zai same mu dan mun rasa H and H” yace “Aunty wannan kudin yaran nan ne, in kuma suna da bukata fa? Besides, kuma kuma bukatar abubuwan amfani da yau da gobe, gidan nan yana bukatar maintenance, yara suna bukatar kudin makaranta, wannan kudin shine future din kowa, in na dauka na fara business dasu suka lalace yaya zamuyi kenan?” Sai tayi murmushi, wannan maganar daya fada exactly irin wadda ya fada ce shekaru goma sha uku da suka wuce lokacin da Hussain yake rokonta ta bashi gadon su ya shiga kasuwanci dashi, tace “Hassan kenan. Always the smart one. Muka bawa Hussain kudi ya kafa kasuwanci ma ballantana kai? Hussain din da yake kashe kudi tamkar wanda yake saka musu wuta ballantana kai da nake da tabbacin zaka adana su? Maganar yanuwanka kuma ina tuna maka cewa suma yanuwan Hussain ne kuma suna sonsa kamar yadda kake sonsa dan haka in suka ji abinda kayi da kudin daya bar maka murna zasuyi suji dadi, in kuma suka ji abinda ni kuma nayi da nasu kudin sai su kara jin dadi saboda kai ma dan’uwan su ne kuma suna son ka sosai”