TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Kar ka manta, tabbas Hussain ne yake biya musu kudin makaranta amma kai kaine kake tsaye a kansu a matsayin babansu, tun daga sec sch dinsu har jami’ar su kai kace fafutukar samar musu kuma duk wani abu da ake bukata na uba kai kake yi musu, wadanda suka yi aurea cikin su kai ka tsaya musu a matsayin uba Hussain kudin kawai yake fitarwa. Kar kuma ka manta cewa Hassana da Safiyya yanzu duk aiki suke yi, aiyukan kuma da kai ne kayi fafutukar samar musu, nan zuwa karshen shekarar nan muke saka ran Khadijah zata karbi certificate dinta a matsayin cikakkiyar likita, Nafisa tana shekarar ta ta karshe, Zulaihat tana shekara ta biyun karshe, to menene kuma ya rage wanda suke bukata? Allah yayi mana komai Hassan, mun gode masa kuma mun gode maka kai da danuwanka, ko Hassana kadai a yanzu zata iya kula damu kafin business dinka ya kafu, tunda mijin da kai ka zabar mata bai rage ta da komai ba kuma salaryn ta mai kyau ne. Maganar house maintenance kuma bana jin muna bukata, motocin nan da Hussain ya tara mana duk ka hada kansu ka siyar ka kara jari, ka bar mana guda daya ta ishe mu kaga an rage kudin maintenance da kudin mai, an kuma rage drivers, driver guda daya ya ishe mu mai gadi guda daya. Ina da kudade a account dina da kuke bani kai da danuwanka a matsayin kudin kashewa, babu abinda nake yi dasu sai ajjiya, suma zasu yi mana wani amfanin, yaran nan gaba ki daya babu wadda bata da personal kudi a account dinta, mai muke bukata kuma? Wacce daga cikin niimar ubangijin mu muka raina?”

Sai ta mike ta hau sama, Hassan ya bita da kallo sai gata ta kuma saukowa dawani karamin box a hannunta ta ajiye a gabansa tace “gwala gwala-gwalai nane da Hussain yake siya min duk sanda yayi tafiya, yasan yadda nake son gold shi yasa yake siya min a matsayin toshiyar baki dan kar inyi masa fada. Ka bawa Jabir naga yana harkar gold ya siyar maka ka kara dasu” ya girgiza kansa yace “Aunty ai kina son kayanki ko?” Tace “eh ina son su mana, shi yasa na baka ai saboda nafi son ka akansu. Kuma nasan in kayi kafuwar da nake so kayi zaka siya min abinda yafi gold ma ba gold ba. A yanzu so nake kayi kafuwar da Ruqayyah in ta kalle ka sai ta sake kallonka. Allah ya sa maka albarka a cikin duk abinda zaka yi, na yarda dakai Hassan, na tabbatar nan da shekara mai zuwa sai ka kai gurin da kai kanka sai kayi mamaki ba mu ba”.

Yayi shiru yana mamakin Aunty da irin tarin kyautatawar ta gare su shi da Hussain, ko uwar data durkusa ta haife su iyakacin soyayyar da zata nuna musu kenan. Ya dauki takardun da box din ya mike zai tafi sai tace “Hassan, abinda Ruqayyah bata fahimta ba shine da family da kuɗi akwai banbanci mai girma a tsakanin su, in kana tare da family dinka babu irin matsayin da ba zasu tallafa maka taje ba, shi kuma kudi baya taba siyawa mutum family, amma nan gaba kadan zata gane” ya gyada kai yace “insha Allah Aunty. Nagode sosai. Thank you for your understanding, thank you for believing in me”.

A ranar yayi waya ya bayar da kwangilar yin katanga tsakanin gidansa da gidan Hussain inda Ruqayyah take ciki. Washegari da sassafe suka fara aikin, shi kuma ya fita ya kaiwa Jabir akwatin gold din Aunty yace ya siyar masa, daga nan kuma sai ya tattara hankalin sa kachokan ya mayar kan harkar sadakar da yayi niyyar yi. Ba wai mutane ya tara ya rarrabawa kudin ba a’a sakawa yayi aka bincika masa ƙauyuka da unguwannin da suke fama da matsala ko ta rashin ruwa ko masallaci ko makarantar islamiyya ko harkar lafiya, wannan yayi tayi, abinda yasan zai zaman to sadakatul jariya ga Hussain. Boreholes an haka babu adadi, masallatai an gina an saka alquranai a ciki, an kuma gina islamiyyoyi da yawa an zuba duk littattafan addini an kuma dauki malamai, sai kuma ya koma asibitoci yana neman marasa lafiyan da ba zasu iya biyan kudin aiki ko siyan magani ba, duk da sunan Hussain, da fatan Allah ya kai rahama kabarin Hussain. Wannan abin da yake yi shi ya taimaka masa sosai wajan mantawa da Ruqayyah and all what she did, dan baya ma tunawa da ita sai yazo kwanciya bacci tukunna zaiyi ta juyi a gadonsa zuciyarsa tana kuna da kalaman ta wadanda har yau yake jin su tamkar mashi ne a kafe a cikin kirjinsa, tabbas ta riga tayi masa illar da ba zai taba warkewa ba. Yayi mata so iyakacin so ita kuma ta zalince shi iyakar zalinta.

Sai da abubuwa suka lafa sannan ya waiwayi Jabir da maganar gold, nan take ya dauko kudi da takardar lissafi tsaf na yadda ya siyar da kowanne, Hassan bai karbi lissafin ba kudin kawai ya karba yana jinjina yawan su, tabbas gwalagwalan masu matukar tsada ne, tabbas Hussain ne ya siye su.

Wannan kudin su ya hada da kudin gadon kannensa da suka bar masa, ya kuma hada da kudin da ya dade yana tarawa a banki inda yake ajiye rabin albashinsa na kowanne wata, jimillar abinda ya samu sai data bashi mamaki, amma sai dai har yanzu bai yanke shawarar abinda zai yi ba, shi ba Hussain bane ba, shi bai iya shiga abu sama ta ka ba, shi yafi gane ya zauna yayi tunani akan abu yayi bincike sannan yayi. Dan haka wannan karon ma haka yayi, yayi tunani yayi bincike yayi shawara sannan yayi addu’a. A karshe ya yanke shawara. Real Estate management.

Ya yanke wannan shawarar ne saboda fahimta da yayi cewar risk na asarar kudi a real estate market is very low, ko mutum bai ci riba ba to ba zaiyi asara ba in dai ba disaster ya hadu da ita ba kamar gobara, flooding da ire-iren su, ya gaya wa Aunty shawarar sa kuma ta amince da hakan ta saka masa albarka sai yaje ya sayi land babba, ya zagaye shi sannan ya fara gini, blocks guda shiga kowanne kuma sama da kasa, kowanne gida kuma three bedrooms da palo, tsarin gidajen kuma irin na zamani masu kyau da akayi da kayayyakin aiki masu nagarta, a cikin watanni shida ya gama komai, ya zuba duk abinda ake bukata a gidajen. Wannan itace estate dinsa ta farko wadda ya sakawa “Hussain Aminu Abdullahi Memorial Estate”.

Ginin estate din nan sai daya lamushe duk tarin kudin da yake ganin ya tara dan har sai daya fara tunanin ya daga gidan sa ya siyar amma Aunty da sauran yanuwansa suka hana shi, suka sake tallafa masa sosai, daga mai siyar da sarkar ta sai mai siyar da motar ta a haka gini ya kammala. Suka shirya walima ta taya shi murna wadda aka hada tare da addu’ar shekara ta rasuwar Hussain, aka gayyaci yanuwa da abokan arziki aka hadu anan cikin Estate din aka gabatar da adduoi aka kuma ci aka sha aka gode Allah sannan aka zazzaga aka ga gidajen, a take aka fara kama hayar su, abin mamaki sati bai rufa ba duk an kame gidajen guda goma sha biyu. A ranar ne bayan an tashi Aunty ta saka shi ya mayar da Sumayya gida.

Babban kuma abinda ya jawo hankalin mutane kan gidajen bayan kyawun shine sunan da aka saka wa Estate din, kowa yasan Hussain Aminu kuma yasan taste dinsa bana banza bane ba.

Kudin da aka hada wa Hassan a matsayin kudin hayar gidajen sai yaga sun ishe shi siyan wani land din har da kafa foundation din wasu gidajen suma irin wadancan, dan ma dai abin ya hadu da bikin Khadijah wadda shi yayi mata komai da ya kamata uba yayi wa yarsa, sai kadan daga kayan kitchen wadanda ta siya da kanta tunda ta fara daukan albashi sannan kuma yanuwanta ma suka siya mata wasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button