TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

A cikin shekara gudar nan Hassan went through a lot a zuciyarsa, yayi fighting sosai da soyayyar Ruqayyah, yayi fighting da impulse din da yake gaya masa ya shiga gidan da take ya duba jikinta, ya dai taba ganinta a bakin gate kamar tana so ta shiga gidan, tana jan kafa tana bin katanga, a take ya kira maigadi yace kar ya barta ta shiga, sai dai ganin nata ya taba zuciyarsa kuma ya gaya wa Aunty, tun daga nan dai yasan Aunty ta kan aika mata da yaran lokaci zuwa lokaci su ganta, bai taba tambayarsu ya take ba, bai kuma taba shiga shi ya ganta din ba.

Wannan kenan……

Sumayya, in ka ganta a cikin shekarar nan zaka kasa tantance wanene yafi shiga damuwa tsakanin ta da Hassan. Ta rame ta lalace ta fita daga hayyacinta, rashin Adam, tunanin halin da yake ciki shine yake hanata bacci, yake hanata karatu, yake hanata cin abinci, yake kuma hanata fara’a. Kowa ya santa ya san ta chanja. Tun a watannin farkon bayyanar gaskiya ta samu Inna Ade, wadda itama a lokacin duk ba’a cikin nutsuwar ta take ba saboda tunanin Ruqayyah. Ta zauna a kusa da ita tace “Inna magana nazo da ita dan Allah, ki daure ki dan saurare ni ko kadan ne” Inna ta juyo tana kallonta, bata jin dadin yadda yar tata take rauzayewa a guri daya tace “Sumayya wani abun kike so?” Sumayya tace “dama Inna akan maganar Adam ne, nace ko zaki dan yiwa Baba magana muji ko da akwai yadda zamu iya zuwa nemansa” Inna ta bude ido tace “nemansa Sumayya? A ina zamu neme shi? Kina ji dai Hassan yace yana tare da mahaifansa a can garin inyamurai, ta yaya zamu iya zuwa can mu neme shi?” Sumayya ta fara sharar hawaye, “ni zan iya zuwa Inna in kun barni, ko ku hada ni da Sulaiman, Inna dan Allah” Inna tana girgiza kai tace “Sumayya! Sumayya munsan kin damu da Adam kuma muma mun damu dashi, mun damu da musan halin da yake ciki, amma ba zamu barki ki tafi nemansa ba Sumayya, ko da a kusa yake damu ba zamu barki ki fita nemansa ba ballantana yayi nisa sosai, yana cikin mutanen da ba irin mu ba wadanda shiga cikin su zaiyi mana wahala” sai Sumayya ta kara sautin kukan ta, inna ta jawo ta jikinta tana lallashin ta “ba zan iya yiwa babanku maganar nan ba, ransa a bace yake har yanzu akan maganar yaruwarki, ga kuma alkawarin da yayi wa Hassan a kanki….” Sumayyan ta kwace jikinta, bata so ko zancen hadin su da Hassan ayi mata dan kullum so take ta gaya wa kanta cewa hakan ba gaskiya bane ba, in aka fada kuma sai taji yana so ya zama gaskiya. Tace “Inna Adam fa? Shikenan mun bar shi? Shikenan ba zamu taimaka masa ba?” Inna tace “Sumayya Adam jarumi ne, kuma islam ya zauna a zuciyarsa, bani da shakku a kansa, kuma indai har da gaske yana son ki yana kuma son auren ki zai samu hanyar da zai dawo zuwa gare ki. Shi yasan inda kike, ke kuma baki san inda yake ba dan haka shine ya kamata yazo gare ki ba ke zaki je gare shi ba”.

Wannan maganar bata saka Sumayya ta hakura ba, ta cigaba da yiwa Inna Ade maganar Adam lokaci zuwa lokaci amma kuma ga mamakin Inna Ade ko sau daya Sumayya bata taba ambatar sunan Ruqayyah ba duk kuwa da yawan zancenta da Inna Aden take yi kullum. Ko ranar da Ruqayyah tazo gidan Baba yayi mata korar kare ma Sumayya bata fito daga daki ba balle taga ramammiyar fuskar Ruqayyah.

A hankali Sumayya ta cigaba da zuwa makaranta, ta cigaba da karatu duk da dai ba kamar da ba. Sukan hadu da Zulaihat lokaci zuwa lokaci kuma a hankali sai suka fara kawance, basu taba haduwa sunyi zancen Ruqayyah ba, sai dai sukan yi hirar Aminu da Yusuf da kuma little Hussain. Wani lokacin kuma Sumayyan ta kan je har gida taga yaran wani lokacin har ma ta tafi dasu gida su kwana biyu tare da ita kafin ta dawo dasu. Wannan ya saka basu manta da ita ba, suka saba da ita sosai. A haka shekara ta zagayo, Sumayya da Zulaihat suka shiga shekarar su ta karshe a jami’a. A lokacin ne akayi addu’ar shekarar Hussain da mutuwa, a lokacin ne kuma aka gabatar da walimar bude estate din farko da Hassan yayi, a lokacin ne kuma Zulaihat ta gayyaci Sumayya.

Tare suka tafi da Inna da Baba da Zunnur, saboda Hassan yazo har gida ya gayyace su suma. Anyi addu’a, anci ansha kuma an zagaya anga gida. Ita da Sumayya taga Inna tare da Aunty suna hira, sai ta basu guri ta tafi gurin su Zulaihat suna admiring flowers din gidan. Bata ankara ba sai waiga wa tayi ta nemi su Inna ta rasa, data nemi ba’asi sai aka ce mata ai sun tafi. Hankalin ta ya tashi dan bata da ko kwandala a jakarta, me yasa su inna zasu tafi su barta? Tana cikin tunanin Aunty ta kira ta, sai ta tarar dasu tare da Hassan suna magana sai taji tace masa “Hassan in ka gama sai ka sauke Sumayya a gida, su Sa’adatu sun tafi sun barta”.

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020

Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800
bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa
Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin AllahThe Fortune Teller

Ya juyo yana kallonta, suna hada ido tayi sauri ta sauke kanta kasa tana kokarin barin gurin sai Aunty tace “Sumayya ki jira shi ya karasa dai ya kaiki gida” ta gyada kai, amma sai aunty tace “kinji?” A dole tace “eh naji aunty, zan jira shi” Aunty tace “good” sannan ta juya tana harhada kan yayanta da jikokinta. Sumayya tana kallon su suka shiga motocin su suka fara fita daga gurin, tana son tace su rage mata hanya amma babu dama dan haka ta ja bakinta tayi shiru ta bisu da kallo har suka fita sannan ta samu kujera can gefe ta zauna da waya a hannunta tana kallon tsofaffin pictures dinsu da Adam, in ta kai karshe sai ta dawo farko ta kuma maimaitawa sannan ta koma kan chats dinsu tana bi tana karantawa tana murmushi, ta karanta message dinsa na karshe “you know I love you, right?” sai taji hawaye yana diga akan wayar, tayi sauri ta dauke su a hankali tace “and I love you too” sai ta kife screen din wayar tana jin zuciyarta tana zafi. Me yasa ba zai zo ba? In dai har yana tare da iyayensa kuma yana cikin koshin lafiya ai ya kamata ya nemeta ko dan ya gaya mata cewa yana lafiya tunda yasan zata shiga damuwa saboda jin shiru daga gare shi. Sai taji tana jin haushin sa, To ko dai wani abun ya same shi ne?

Ta daga kai tana kallon mutanen da suke ta hada hada a gurin, kusan duk yan uwa sun tafi sai abokan Hassan suma da yake ta sallama dasu suna shiga motocin su suna fita, tasan da Adam yana nan maybe shima da yana gurin nan, da dashi za’a yi wannan hidimar, duk da babu Hussain tasan da Hassan zai cigaba da rikon sa in ma ba zai rike shi ba tasan Baba zai iya rike shi a gidan su. Da yanzu yana nan yana karatunsa, da yanzu sun shiga level four tare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button