TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Aunty ta kalli Hassan ta daga kafada tace “a gurin su mommy ce, ba step mom ba, duk matar da zaka aura will be their step mom not their mom. Kamar yadda nake a matsayin uwa a gare ku not a matsayin kushiyar uwa Sai kayi lissafin abinda zai iya faruwa da ku idan da ace iyayen mu basu yi tunanin hada aure na dana mahaifin ku ba. Maybe da bamu samu kan mu a matsayin da muke kai a yanzu ba. Wannan kadai ya ishe ka misali” ya sake cewa “aunty, this is a different case, na gaya miki yarinyar nan bata sona, in anyi abin nan zai zamanto kamar an tilasta mata ne” Aunty tace “nima sanda aka aura min babanku bana yi masa soyayyar aure, amma a yanzu da za’a dawo min da rayuwata baya ace in sake zabar miji da shi zan sake zaba over and over again”

Sai ya kama kofa ya bude zai fita ba tare da yace mata komai ba, tace “Hassan” ya juyo yanab kallon ta amma bai amsa ba sai tace “misali idan Sumayya ta yarda zata aure ka, zaka amince?” Yace “bata so na Aunty, ba zata yarda ta aure ni ba” ta sake cewa “misali nace ai, in ta yarda, zaka yarda kaima?” A rufe idonsa ya bude, sai kuma ya gyada kai yace “yes, zan yarda, but only in ta yarda, in ba tilasta mata akayi ba”.

Wannan kenan………

Bara mu leka muga yadda rayuwa ta kasancewa Ruqayyah a cikin wannan shekarar………..

A ranar data farka ta tarar ana katange gidan da take ciki, a ranar ne kuma yan aikin gidan kaf dinsu, wadanda suka yi aiki a karkashin fatima suka hada kayan su kaf suka zo yi mata sallama “zamu tafi, Allah ya sada mu da alkharinsa” Ruqayyah ta bude baki “ba gane zasu tafi ba, ni na sallame ku ne? Ni da iya kacin saninaba sallami kowa a cikin ku ba, ko akwai wata matsala ne wadda ban san daita ba?” Babbar cikinsu tace “babu wata matsala, kawai da bazamu iya cigaba da aiki a gidan nan ba alhalin masu gidan basa cikinsa” Ruqayyah tafara kufula, “ban gane masu gida basa ciki ba, ni nice mai gidan, wadanne masu gidan kumakuke magana akai?” Tace “gimbiya Fatima itace uwargidan mu, mutuniyar kirki da sanin ya kamata, tunda akayi auren ku ita muke yiwa aiki da haka yanzu lokaci daya ba zamu iya cigaba da aiki a cikin gidan nan sannan kuma ba a karkashin taba. Gwara mu tafi mu nemi wani aikin a wani gurin daban” Ruqayyah mamaki ya kamata, me suke nufi? Zasu iya yiwa Fatima aiki ammaita ba zasu iya yi mata ba? Dame Fatima ta fita?

Ta fara lallashin su da nuna musu cewa duk abinda Fatima take musu itama zata dora akai amma suka tubure suka ki zama. Har sun mike tace “zanyi muku doubling salaries dinku in kuka zauna” ita tana ganin wannan wani abu ne da ba zasu taba iya turning down ba amma sai taji daga daga cikin su tace “it is not about the money, it is about loyalty” daga nan suka fita suka barta a zaune.

Takaicin duniya ya ishe ta, ita bata san inda ake samo yan aiki ba dan tunda akayi bikin su Aunty ce take samo mata yan aiki har da mai girki duk ita take samo mata ita da Fatima, gashi yanzu na Fatima sun gudu saura nata kuma aikin yayi wa nata yawa dan gidan ba irin nata bane ba, duk kuwa da cewa bangaren Hussain a rufe yake.

Sai taji gida yayi mata shiru sosai, taji wani irin kadaici kamar ita kadai ta rage a duniya, wannan yasa ta kira zuwaira a waya, kawarta ce da Minal ta hada su kuma tana cikin kawayen ta da suka tsaya mata a wajen bikin su ta gaya mata problem dinta “ban sani ba ko kin san yadda zanyi in samo yan aiki? Kamar gida biyu haka masu hankali” babu bata lokaci zuwaira tace zata samo mata sannan kuma suka jajanta labarin batan Minal, zuwaira tace “ance man ke ce mutum ta karshe da kika ganta ko?” Ruqayyah tace “inji wanne munafikin? Inji wanne makaryacin?” Zuwaira tace “a’a, ni da mijinta ne yake gayamin kuma yace mijinki ne yagaya masa, ba san waye munafikin ba a cikin su ba kuma san wate makaryacin ba” Ruqayyah tayi kokarin chanja maganar “okay ban san sunyi maganar ba ai. Ki gayyato duk kawaye ku zo kuga sabon gidana” sai ta bata labarin tarewar da tayi a gida Hussain. Tun a wayar taji excitement a muryar ta, kafin a jima kuwa wajan mutum biyar a kawayen su sun kira ta aka maganar, shi kenan aka bar maganar batan Minal aka cigaba da lissafa yadda za’a ci duniya.

Wannan yasa Ruqayyah taji kadaicin taya dan ragu, sai dai tayi ta kiran wayar Sumayya amma bata shiga, taso ko ma menene zata yi Sumayya takasance a hannun damanta kamar yadda suka shirya tun suna yara amma abin ya gagara, daga dukkan alamu Sumayya tayi fushidaita amma tasan zata sauko tunda ita ba iya fushi tayi ba, dawani ma ballantana da ita yaruwarta Ruqayyah.

Sai ta bata lokaci da niyyar ta huce, kafin nan suma su Inna da Baba sun huce sai taje har gida tayi musu bayanin cewa Hassan da kansa ya dauki kudin nan ya bata ba takura masa tayi ba, wata kila ma daga nan su yarda su biyo tasu dawo gidan da zama gabaki daya. Wata kila idan sunzo ta samu nutsuwar zuciya har ta iya bacci, dan yanzu sam bata bacci sai ta sha maganin bacci shima idan ta sha a wahale take yin baccin. Wannan kukan jaririn ne yake damunta a kunnuwan ta, ko ta cire hearing aid dinta bata daina jin sa dan kamar a cikin kanta yake ba wai ta kunnen ta kukan yake shiga ba. Da zarar ta rufe idonta kuma gawar Minal take gani, bata yo mata magana sai idanuwa da take tsare ta dasu, idanuwa masu ban tsoro, in kuma ta samu tayi baccin to kuwa sai Hussain ya ziyarce ta a cikin baccin ta, kullum mafarkin kusan guda daya ne cewa jaririn data ajiye a kofar orphanage ya girma ya rikide ya zama Hussain ita kuma ta koma jaririn, so defenseless so vulnerable and so scared, shi kuma sai yazo yasa kafa ya tatsile ta, kullum mafarkin iri daya ne amma kuma kullum sai ya bata tsoro tamkar ranar ta fara yinsa.

A haka har tayi sati daya agidan ita kadai kamar mayya, wanda zata yi magana dashi ma babu sai yan aikin da ba wata sabawa sukayi ba balle suyi hira, a lokacin ne kuma kawayenta suka kawo mata ziyara ta zagaya dasu duk suka ga gida suna ta yabawa. A ranar ne kuma alert ya shigo wayarta na ribar data samu a kamfani a cikin wannan satin. Ta rike baki tana mamaki hade da murna, da gaske Hassan yake kenan, da gaske wannan kudin duk nata ne. Lokaci yayi da zata je gida ta yiwa su baba bayani ta kuma lallabasu su dawo gidan ta da zama ko ta danji dadi a ranta, dan ita har yanzu data ga alert din kuɗin bata ji dadin da take tunanin zata ji ba. Zuciyarta a kuntace take, maybe in suka zo zata ji dama dama.

Ta shirya ta ja kafa ta sauka kasa ta aika aka kira mata drivern data bari a matsayin nata ya jata zuwa gida, ta ja kafa cikin murna ta shiga gida amma tun a soro Baba ya dakatar da ita “me kika zo yi gidan nan?” Tace “Baba ina wuni? Nazo muyi magana ne” yace “maganar me? Innar ki bata gaya miki sharadin dana kafa ba? Amma na ganki da mota? Cewa nayi ki ajiye duk abinda kika san a gidan Hassan kika same shi ki taho ke kadai kamar yadda aka kai ki ke kadai, idan ba haka kika yi ba kar ki shigo min gida na” ta fara girgiza kanta “Baba shi ya bani da kansa matsa masa nayi ba, kaso ya bani a cikin kamfanin su, da kuma gidan daya gada na danuwansa, yanzu duk nawa ne, zuwa nayi ku binimu tafi can zai fi nan dadin zama sai……” Ya daga mata hannu “duk ya gaya min abinda kika yi wanda yasa har ya baki wadannan kudade, bama son ko kwandala a cikin su, ke kadai muke so, in kina son mu ki jiye masa kudinsa ki dawo gare mu, in kuma kinfi son kudi ki koma ga kudi mu ki barmu”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button