TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya muskuta a hankali har yaje jikin kofar sannan ya jingina jikinsa da kofar ya kasa kunnen sa yana so yaji abinda suke cewa amma har kansa ya fara ciwo saboda stressing kunnensa da yayi bai samu ya fahimci komai a maganganun nasu ba saboda can kasa suke maganar. Ya fara buga kansa a jikin kofar, yana jin kan yana kara yi masa ciwo amma yana so yayi calling attention din wadanda suke waje in mutanen kirki ne su taimaka masa in kuma holders dinsa ne ya nemi su kunce shi yayi sallah. Sukayi shiru da maganganun su a lokaci daya sannan suka taho bakin kofar da sauri suna gyara abinda suka rufe fuskokinsu dashi. Katon ne ya bude kofar da sauri yana auna Hassan da bakin bindigar da take hannunsa “Will you stop banging that door?” Ya fada murya can kasa kamar me rada. Hassan ya fara kokarin magana amma sai ya kasa saboda bakinsa yana rufe. Mutumin ya saka hannu daya ya cire abin bakin Hassan, Hassan yaji tamkar ya cire ne tare da fatar bakin gabaki daya saboda zafin da yaji amma babu hannun shafawa dan haka kawai ya runtse idonsa har zafin ya lafa, sannan yace “ina son zanyi Sallah dan Allah” mutumin ya sunkuyo fuskanta kusa data Hassan yace “kaga nayi kama da mai yin Sallah? Reserve your sallah kayi ta addu’a twin dinka ya biya mu kudin da muka nema and you will be out of here kaje kayi ta sallolinka”.

Dayan ya matso yana turawa Hussain robar abinci data ruwa gasansa, ya kunce masa daurin hannunsa sannan yaja baya, mai bindigar yace cikin gurbatacciyar hausarsa “mu na nan a bakin kofa, if you dare try to make any sound I will fill your brain with bullets” and Hassan knows he means it.

Sai da suka rufe kofar sannan ya dauke ganinsa daga kansu ya mayar kan hannunsa yana shashshafa shi, bringing back blood, sai da yaji hannun ya danyi masa dama dama sannan ya jawo kafarsa yana noticing yadda ta kumbura ya fara kokarin kunce ta, da kyar ya iya kuncewa saboda karfin daurin da suka yi masa da kuma kumburin da kafar tayi. Ya jawo ta yana shashshafa ta sannan yayi kokarin mikewa yayi alwala da ruwan da suka bashi, bai san inane gabas ba kuma ko ya tambaya ba zasu gaya masa ba dan haka sai ya zabi guri ɗaya yayi niyya ya tayar da sallah sa, saboda shi addini mai sauki ne, ubangiji masani ne kuma mai rahama ne.

Bayan ya idar, yayi dogayen adduoi sannan ya zauna ya runtse idanunsa yana kokarin tuno yana yin da ya hango cikin dakin da mutanen suke. Dakin bashi da girma kuma da alama ba’a kammala shi ba dan jikin bangon babu penti kuma tagogin babu frames. Yayi assessing yadda yaga situation din, mutane biyu ya gani amma yasan su uku suka dauko shi, ina dayan? Ya tuno da muryar da yaji a mota, muryar da yaji kamar ya sani. Shin mai muryar ne baya nan? Ya tuna da yadda yaga suna magana cikin rada, da kuma yadda suka buga masa warning din kar yayi making sound, hakan yana nufin cewa a cikin gari suke, a cikin mutane suke. Ya kalli window din da take saman toilet din, glass ne, yana fasawa zasu ji kara kuma kafin ya gudu zasu harbe shi, dan babu imani sam sam a cikin idanun wannan katon.

Yayi ajiyar zuciya ya jingina kansa da jikin bango yana shafa fuskarsa yana jiyo maganagun su kasa kasa a cikin dakin, his only option is to wait har Hussain ya basu abinda suke so su sake shi. Ba shi da ko digon kokwanto cewa Hussain zai biya kudin, ko da kuwa zasu nemi dukkan abinda ya mallaka zai basu, ko da zasu nemi ya bada kansa zai basu, ko da wani aka kama ba shi ba Hussain zai iya biyan kudin ransom ya ceto mutum. Shi mutum ne da dukiyarsa sam bata dame shi ba.

Hassan ya yanke shawarar zai jira, yasan jiran ba zai yi masa dadi ba amma bashi da wani option than that. Zai jira har sai Hussain ya biya kudin sannan su sallame shi ya koma gida sannan kuma ya yanke shawarar yana komawa gida zai yi aure.

Five days later……………

Tunda Hussain ya dawo Nigeria yake jiran barayin Hassan su sake kiransa amma shiru, ba kira babu message babu komai, shima kuma in ya kira number din Hassan din bata tafiya. Hankalin sa in yayi dubu ya tashi kuma commissioner of police ya gaya masa abinda suke so kenan, so suke su gama tsorata shi yadda duk abinda suka ce yayi zaiyi.

Hussain ya girgiza kansa yace “then they don’t know me as they claimed they do. I will give up anything for Hassan. One billion naira suka ce masa suna so in dollar bills kuma gata nan na hada na zuba a irin jakar da suka ce in zuba su kawai naje jira su gayamin yadda zanyi da ita” ya karasa maganar yana mikewa yana zagaye dakin. Haka yake tun sanda ya dawo daga China, baya taba zama na minti biyar a guri daya zai mike kamar wanda ake mintsinin sa, fuskarsa tayi baki, idonsa yayi ja kuma ya fada ciki saboda rashin cin abinci, rashin bacci da kuma rashin kwanciyar hankali.

A ranar da aka sace Hassan, Hussain Yana sauka a Beijing ya kira Hassan da niyyar ya gaya masa ya sauka, a lokacin kidnappers din suka dauka kuma direct suka gaya masa cewa yana hannunsu, suka bashi umarnin ya dawo Nigeria sannan suka gaya masa adadin kudin da suke bukata. Sai kuma suka turo masa hoto, hoton Hassan a daddaure a yashe a bandaki, hoton da har yau shine yake yawo a kwakwalwar Hussain, shine yake hana shi bacci.

Ranar da ya dawo Nigeria gidan su ya cika da police da yanuwansu na Gombe da sauran abokan arziki da abokan aiki, kusan duk uncles dinsu da aunties da cousins dinsu sun zo. Yana shiga gidan zai gansu duk a zazzaune da charbi suna ja kamar gidan makoki, sai gidan yake nuna masa kamar Hassan ya mutu ne, sai yake tunawa da mutuwar Abban su.

Wannan ya saka ya tattara kayansa ya bar gidan ya kama daki a hotel duk kuwa da nuna wa da Aunty tayi cewa bata yarda da hakan ba, tana jin tsoron kar wani abu shima ya same shi. A hotel din ne commissioner of police ya same shi kuma ya hada shi da SS dan suke tsaron lafiyar sa “bamu san menene nufin su na yin shiru haka ba, maybe tarko suka dana, maybe kai suke nema mistakingly suka kama Hassan”.

Bayan kwana biyar da kama Hassan ne kidnappers din suka sake contacting Hussain da wayar Hassan din. Message suka tura masa

“Kana so ka sake ganin twin dinka? Ka cire police daga gidan ka sannan su daina zuwa hotel din da kake zaune, SS din da suke gadin ka ma ka sallame su idan ba haka ba zamu dawo maka da Hassan, but in PIECES”

Ya ajiye wayar a gefe ya mike ya fara pacing dakin da yake ciki yana yarfar da hannayen da, sai kuma ya shiga toilet ya yo alwala ya dawo ya gaya wa Allah sannan ya dauki wayar sa yayi wa commissioner forwarding message din na su. Jima wa kadan kira ya shigo daga commissioner din ya dauka baice komai ba. Commissioner yace “barazana ce suke yi maka kar hankalin ka ya tashi ba zasu iya yi masa komai ba tunda suna bukatar kudin ka” Hussain ya lumshe idonsa ya bude, he is not going to take that risk, yace “ku janye mutanen ku. I will do this thing alone, zan iya” commissioner yayi ajiyar zuciya yace “I understand, zamu matsa, but Please keep us updated, daga an karbe shi kuma zamu yi moving in mu kama su mu dawo maka da kudin ka” Hussain yace “alright. Nagode” ya ajiye wayar tare da saka hannayen sa ya rufe fuskarsa.

A lokacin wayar Gimbiya Fatima ta shigo, she had been very supportive dan sau biyu tana zuwa Kaduna gurin sa tare da brother dinta. Mai martaba ma ya aiko takanas anyi masa jaje kuma yayi alƙawarin saka Hassan a cikin adduoin sa da kuma umartar malamai suyi ta addu’a akan lamarin. Ya dauka wayar ya gaya mata duk halin da ake ciki. Cikin shigar lallashi tayi ta bashi baki tare da bashi shawarwari har sai da taji alamun ya dan daidaita sannan suka yi sallama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button