TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta jima a zaune a gurin tanajin hawayen ta yana zuba akan rigarta, sannan ta saka hannu ta dauki takardar tana karanta amount din kudin daya rubuta sannan ta girgiza kanta da sauri, inaa, ba zai yiwu ba, wato kura da shan bugu gardi da kwace kudi? In dai har zata ke bashi wannan kudin duk wata sannan zata ke biyan maaikatan data dauka a gida albashi plus kayan abinci da sauran house maintenance to babu abinda zata tsira dashi ita din. Tunda ta fara ganin alert daga H and H lissafin ta shine ta tara kudi ta nemi hanyar da zata bi ta dauko likita daga waje yazo ya duba mata kunnen ta yadda zata iya hawa jirgi ta tafi neman lafiyar kafar. Yanzu kuma gashi wannan yallaban yace shi zata ke bawa kudin, wato ita kuma ta cigaba da zamanta a matsayin musaka har karshen hargitstsiyar rayuwarta? Gaskiya da sake wai an bawa mai kaza kai.

Ta dauki takardar ta saka a jakarta ta koma mota suka fita daga gidan, a zuciyarta tana tambayar kanta dalilin daya dawo da ita zuwa gurin dan duban, duk dadai tasan in yaso blackmailing din nata zai iya binta har gida ya gindaya mata sharadin sa. Amma wannan sharadin sam ba zata iya binsa ba ba zata iya zama baiwar sa ba. Ita da zunubin, ita da rashin iyaye, ita da nakasa, ita da rashin miji sannan kuma shi da samun kudi? Wannan sam ba zata yiwu ba.

Tana zuwa gida ta wuce cikin bedroom ta jawo akwati ta fara zuba kayan sakawarta, gida zata koma ta zauna, gwara ta mayar wa da Hassan dukiyar sa kamar yadda Baba ya bukata, gwara ta bi sharadin Baba wanda ya haife ta ya kula da ita har girmanta akan ta bi sharadin wani kazamin mutum da yake kiran kansa da Malami. Ai dai tasan Baba ba zai hana ta daukan kayan sakawarta ba tunda dai ya’ya uku maza ta haifawa Hassan ai kuwa ta ci lefenta. Gwara taje ta zauna a matsayin musaka, bazawara, talaka amma kuma tare da iyayenta akan ta zauna anan a dukkan wadancan matsayin amma kuma babu iyayen. Sai data cika akwayi biyu da kayan sannan ta fita da niyyar kiran nai aikinta ta fitar mata da kayan bakin gate sai kuma wani tunani yazo mata, yanzu in ta mayar wa da Hassan dukiyar sa ba zata ke biyan mai duba ba, in kuma ba ta biya shi ba zai iya aikata abinda yace zai aikata.

Ta tuno da Fatima da matsayin ta da matsayin mahaifinta da irin tarin son da yake yi mata, me zaiyi idan yaji labarin cewa gawar daya binne ba ta Fatima bace ba, in yaji cewa Fatimah tana raye amma ba’a san a inda take ba, sannan kuma danta, jikansa an jefar dashi cikin kaskanci a gidan marasa gata? Tasan in ya fara daure ta har sai igiya tayi saura kuma babu wanda zai taimaka mata tunda ita a yanzu bata da kowa. Ta tuno irin zuciyar Hassan kuma da irin son da yake wa Hussain, idan yaji abinda ta aikata ga da daya tilo na Hussain in ya shake ta tabbas sai ta dangana da lahira. Idan haka ta faru sunayenta zasu karu daga kurma gurguwa bazawara talaka zuwa yar prison, ko kuma worst, matacciya. Ita kuwa bata shirya tafiya lahira yanzu ba dan tasan bata aikata abinda can din zata yi mata kyau ba.

Ta zauna akan kujera tana dafe kanta, ita kanta tasan cewa rayuwar ta ta kare tun kafin ma ta soma. Ita da kanta ta dauko biro da takarda tayi signing contract da shaidan shi kuma ya zuga ta ta haka rami da kanta ta shiga sannan malamin duba ya binne ta da ranta. Menene kuma yayi mata saura?

Babu abinda ba zata iya bayarwa ba a yanzu dan ta dawo da hannun agogo baya. Dan ta dawo da rayuwarta ta baya, dan ta dawo da alakar ta da Hassan. Ta tuno da irin son da Hassan yake yi mata da yadda yake tsayuwa akan dukkan al’amuran ta, da ace suna tare ne da wannan mai duban bai isa yayi blackmailing dinta ba Hassan sai ya kwato mata yancin ta. Ta tuno Sumayya, da irin yadda suke open to each other, babu abinda ba zata bayar ba a yanzu dan ta samu Sumayya ta gaya mata halin da take ciki ko zata bata shawarar yadda zasu bullowa lamarin. Ta dauki wayar ta for the nth time ta kira number din Sumayya amma ko ringing ba tayi ba ta katse kamar yadda take yi kullum alamar an yi blocking layinta kenan. Wai Sumayya ce tayi blocking dinta, kuma tasan akan Adam ne. Ita a ganinta taimakon Sumayya tayi data rabata da Adam bata sam cewa zata dauki zafi haka ba.

Shikenan kowa ya guje ta, kowa banda mutum uku, mutum ukun da take ganin har abada ba zasu taba gudun ta ba, ƴaƴan ta, suma kuma Hassan ya raba ta da su. Sai ta mike ta saka hijab dinta ta sauka kasa sannan ta fita, ta fita gate ta tsaya tana kallon gidan Aunty, ta san can ya kai su, tasan bashi da inda zai kai su idan ba can din ba. A fara bin katanga a hankali tana jan kafarta har taje bakin gate din gidan Aunty a dai dai lokacin ne kuma taga motar Hassan tazo gurin, ta dauke kanta gefe dan bata son su hada ido, not now. Tana kallon sa ya sauke glass daga alama kare mata kallo yake yi, tai expecting ya rufe ta da bala’i amma sai taga an bude masa gate ya cusa motar sa ciki, ta lura da yadda ya tsaya yayi magana da mai gadi tare da nuna ta sannan ya shiga gidan, duk da vata ji su ba amma tasan cewa maganar ta suka yi kuma tasan Hassan cewa yayi kar a barta ta shiga gidan, kar a barta taga ƴaƴan ta. How cruel!

Duk da haka bata hakura ba dan tana ganin ai itama ƴaƴan ta ne, amma kafin ta shiga sai maigadi ya tare ta yace “kiyi hakuri hajiya, yallabai yace kar in barki ki shiga, kiyi hakuri dan Allah kar ki matsa, bana son inyi miki abinda ba zamuyi dadi ba gabaki daya” ta tsaya tana kallon katon mai gadin, to in ma bata hakura mai zata yi masa? Ita dai ba zata kama shi da kokawa ba kuma ba zata iya kama katangar ta haura ta shiga gidan ba. Time din da take haura katanga ya riga ya wuce, those good old days!

Ta juya a hankali kamar wadda kwai ya fashe wa a ciki ta sake bin katangata koma cikin tangamemen gate din tafkeken empty gidan da yake matsayin nata, gidan da tunda ta dora idonta a kansa take son ta mallake shi amma yanzu data mallake shin take jinsa kamar wani prison. A ranar tayi kukan da rabon da tayi irinsa ita kanta ba zata iya tunawa ba. A daren ranar kuma bata yi bacci ba duk da maganin baccin da tayi ta bunkawa kanta, ba wai kukan jariri da idon Minal ne kadai suka hana ta bacci ba a’a abubuwan da suka cunkushe mata a ranta ba zasu kirgu ba.

Zuwa safiya ta yanke shawara. Tana idar da sallah ta dauko takardar da mai duban ya bata ta saka number din wayarsa data gani a ciki ta kira, ya dauka tare da sallama, bata amsa masa ba dan tana ganin bai cancanta ba tace “na amince zanke baka kudi kamar yadda ka bukata, amma ba amount din da ka nema ba, zanke baka rabi” yace “baki so a daidaita ba kenan. In rabi ne ki rike kayan ki ni kuma in fara tunanin inda zan fara aikawa da sako na, gidan su Minal? Kano? Ko kuma ofishin tsohon mijinki?” Ta lumshe ido ta bude tace “in nace zan baka duk abinda ka nema, ni zan tashi bani da komai kenan, in haka ya kasance ko zan gwammace in mayar wa da Hassan kudinsa in koma gidan mu, kaga dani da kai munyi two zero kenan. Ka karbi rabin dana baka ko kuma ni da kai duk mu rasa” ya danyi shiru sannan yace “na rage miki, ki bada kashi uku cikin hudu” ta girgiza kai kamar yana ganinta tace “rabi ko nothing. Karkari ta kashe zaka tona min asiri, ni kuwa a yanzu na kuna bana jin tsoron wuta, to waye ya rage min wanda zai guje ni in an san abinda nayi?” Yace “in ma bau wanda zai guje ki ai zaki tafi gidan yari ko? Kinsan…..” Ta dakatar dashi tace “zan tafi prison ko kuma zamu tafi prison? Inajin a duban naka baka duba sosai ka ga wacece Ruqayyah ba, if I am going down I will surely take you down with me, zan ce tare da kai muka shirya komai kuma za’a yarda saboda in ba haka ba ya akayi kasani? Wannan takardar da ka bani da sunanka da account details dinka da kuma adadin kudin dazan baka ita ce shaidata, zan bayar daita a matsayin shaidar payment din da nayi maka na taimaka min da kayi gurin duk abinda nayi. Dan haka kayi tunani kafin ka yanke shawara” yayi shiru, tabbas sai yau ya tabbatar cewa yarinyar nan shaidaniya ce. Yayi gyaran murya yace “shikenan, ki ringa turo rabin” bata ce komai ba ta kashe wayar ta ajiye. Ta kama shi a inda ba zai iya kwacewa bakuma wannan kamun na farko ne, nan gaba sai yayi nadamar hada hanya da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button