TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
A yanzu plan dinta shine zata ke biyan mai duba rabin kudin da ya nema a cikin kudin da za’a ke kawo mata na ribar share din da Hassan ya bata a H and H, sauran kudin kuma bayan ta fitar da abin bukatun ta na yau da gobe zata ke tarawa a hankali sannan sai ta fara neman maganin ciwon ta, zata gwada na hausa dana islamic chemist har in Allah ya taimake ta ta samu kafin nan kuma ta san yadda tayi tayi maganin malamin duba sannan sai ta koma gida, at least dai taji da talaucin ba tare da nakasar ba.
A ranar sai ga mai aikin Aunty ta shigo mata da su Aminu wai inji Aunty tace suzo su gaisheta, murna a gurin Ruqayyah harda hawayenta, ta jawo su jikin ta ta rungume tana kallon yadda suke fes fes dasu babu alamun wata matsala a tattare dasu, at least tana da kwanciyar hankali ta wannan bangaren, tasan ƴaƴan ta suna hannun tiko na gari duk da tasan albarkacin Hassan suke ci .
Haka rayuwa ta tafiyar wa Ruqayya tsahon wannan shekarar, kudi suna shigo mata daga kamdani ita kuma tana bawa malamin dubanta sannan tana tarawa, bayan ya taru kuma ta fara neman magani dashi, duk inda taji mai magani daya danganci kafa ko kunne sai taje amma shiru babu sauki sai a wurin Allah, kafa kullum kara motsewa take yi har ta kai cast din ma yayi mata girma ta koma amfani da crutches, kuma har yanzu bata iya ji da kunnenta sai ta saka hearing aid, har yanzu kuma bata iya bacci sai ta sha sleeping pill, har yanzu kuma bata samu hanyar da zata bi ta rabu da wancan karfen kafar ba.
Rayuwar Ruqayyah kenan……
Sorry guys…. bacci….ina typing ina bacci……ayi hakuri da wannan duk da kankantarsa.
Tomorrow zamu dan fara rushing things up yadda zamuyi covering shekarun da wuri.
Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020
Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800
bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa
Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin AllahDestiny
Tun ranar da Aunty tayi wa Hassan maganar Sumayya bai kuma yi mata maganar ba ita ma kuma haka, amma ya dukufa da addu’a, duk sallah sai ya gaya wa Allah ya kuma roki yayi masa zabin mace ta gari wadda kuma zata zama uwa ta gari a gurin yayansa, waɗanda yake dasu da kuma wadanda zai samu nan gaba. Sai kuma ya mayar da hankalinsa kan business dinsa. Sai dai lokaci zuwa lokaci maganar tana fado masa amma sai ya kawar da ita dan shi bai san da wacce fuskar zaije yayi sallama da Sumayya yace mata yana sonta, shi kansa sai da yadafe kansa daya aiyana abin, wannan ai abin kunya ne kuma zubar da girman sa ne a gurin yarinyar da yake gani kamar kanwarsa. In ma za’a yi to yana ganin sai dai manya su shiga maganar in yaso in anyi auren sai yasan yadda zaiyi. Even at that ma bai san ta yadda zaiyi din ba. To shi ma kenan da yake namiji kna gaita da take mace? Ta yaya zata so shi irin soyayyar aure? Ta ya kuma zata iya muamalar aure da shi? Musamman in yayi la’akari da yadda take girmama shi sosai. Amma ta ko’ina im ya duba sai yaga ita din ce dai a sama a cikin zabin sa. Dan yayansa, dan farin cikin iyayensu, dan nutsuwar zuciyarsa, dan abubuwa da yawa.
Tunanin abin ya sa ya kara kaimi gurin addu’ar sa, yana kuma rokon Allah ya bashi kwarin guiwar tunkarar ta da maganar indai har ita ce alkhairi a gare shi. Daga nan sai maganar ta fara damun shi sosai har ta kan hanashi bacci sometimes, ya saka ya warware, har mafarki yake yaje ya gaya mata yana son auren ta ita kuma tayi mishi masifa tace masa maci amana, a wani mafarkin kuma sai ta karbi tayinsa ta ce Allah yasa hakan shima nafi alkhairi, ya san dole a cikin biyun nan daya ne zai faru amma bai san wanne ne ba, ba zai kuma sani ba har sai ya gwada, Sumayya kamar wani unopened page ce a littafin rayuwarsa, ba zai san menene a ciki ba har sai ya bude, courage din budewa ne kuma ya rasa.
Sai ranar nan dai da sukayi magana da Zulaihat ta gaya masa cewa suna exam din first semester ta final year dinsu, ma’ana semester daya ta rage musu a karatun su na jami’a, sai ya fahimci cewa time yana kure masa, lokacin da Baba ya bashi ya kusa karewa tunda cewa yayi alƙawarin yana nan daga lokacin zuwa sanda zata gama jami’a, yasan kuma Baba jira yake kawai ta gama jami’a ya aurar da ita ko gare shi ko ga wani, wanin kuma yasan ba Adam bane ba tunda dai Adam har yanzu babu labarin sa, dan shi kansa yasan Baba yayi kokarin barin ta har ta gama jami’a ba tare da miji ko kuma wani tsayayyen mane mi ba dan iyaye irin Baba musamman wadanda ba yan boko ba da wahala suke barin haka ta kasance ga ƴaƴan su, maybe ma Baban ya barta har yanzu ne saboda shi, saboda ko zai zo yace ya karbi tayinsa.
Dan haka a ranar sai ya shirya da yamma ya tafi gidan nasu a fili da niyyar gaishe da Baba amma a ransa so yake ya ga ko zai samu wata kafa da zai fake da ita. Sai dai cikin rashin Sa’a sai ya tarar Baban bayanan, duk gidan ma babu kowa duk suna makaranta dan Sulaiman shima ya shiga jami’a last year Zunnur ne dai yake kokarin kammala secondary school dinsa, sai Inna kadai ya tarar a gidan, ya shiga ya gaishe da ita tana ta tambayarsa mazajenta tana korafin cewaya kwana biyu bai kawo mata suba “ko da yake ba laifin ka bane ba laifin Sumayya ne, dama ita ceai zuwa ta dauko su kuma yanzu ta daina wai dan taji muna maganar ku kai da ita ranar nan da Amina a waya. Shine ta daina zuwa gidan dan kar Amina tayi mata maganar” sai ya sunkuyar da kansa kasa shima yana jin kunya, wato har maganar suke yia tsakanin su tun kafin su wadanda za’a yiwa auren su amince. Kuma daga yanayin da Inna tayi maganar itama sai ya fahimci tana son hadin, Aunty ma tana so, Baba shi yayi initiating, saura su kadai ya rage.
Ya tashi yayi mata sallama tare da alkawarin kawo mata maxan ta ranar Friday idan anyi hutu tunda sun fara zuwa school yanzu. Sai dai kuma yana fita kofar gida suka kusa yin karo da Sumayya tana kokarin shigowa gidan a gajiye, kallo daya yayi mata sai ya rike baki yana boye dariyarsa. Ga jaka ga lecture notes a hannunta, ga uban hijabi har kasa wanda daga dukkan alama zafi take sha a cikinsa, fuskarta kadai zaka kalla kasan tsabar gajiyar da tayi da kuma irin yunwar da take kwakwular cikinta. Ta bata rai “dariya kake min ko?” Yayi saurin girgiza kai dan yasan yana bude baki dariyar zata fito, tayi kwafa, “dan ma dai kaima kayi karatun kasan wahalar da ake sha” sai ya bude bakin yayi dariyar sannan yace “ni sanda ina zuwa makaranta da ace kin sanni a lokacin da ba zaki damu dan na yi miki dariya ba, dan kin fini kyan gani, ni kamar skeleton nake komawa baƙi na kuwa ko bayan tukunya nan ya ganni ya bari” tace “ni ma ai kamar skeleton din nake yanzu, hijabi ne ya biye ramar” Yace “an kusa gamawa ai, wahalar ta kusa karewa” ta langwabe kai tace “ameen. Bismillah ko har ka shiga ka fito?” Ya girgiza kai pretending as if bai shiga ba yace “ashe Baban baya nan” ta dan duba wayarta tace “ya kusa dawowa ai, bara in bude maka dakin soro sai ka zauna ka jira shi” ta shiga gidan da sauri bata jima ba ta dawo da key ta bude masa dakin ya shiga ya zauna yana kallon dakin kamar yay ya fara gani, sai yake jin memories na da suma dawo masa, memories din sanda yake zuwa gurin Ruqayyah suke zama a dakin. Yayi sauri ya ture tunanin a gefe dan baya son ya bata mood dinsa, yaji dadin yadda Sumayya ta tarye shi bata bata rai tayi mishi kallon wanda yake forcing kansa a gurinta ba.