TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bai jima ba ta shigo da sobo mai sanyi da ruwa ta ajiye masa tace “yanzu zai dawo” sai kuma ta zauna a gefe tana wasa da hannunta, ya zuba sobon data kawo masa ya daga yana sha yana kallon hannun da take wasa da shi, sai daya ajiye cup din sannan yace “fadi, ina jin ki” ta dan kalle shi kadan suka hada ido tamayar da kanta kasa tace “dama ina ta son in tuna maka maganar nan damukayi ranar nan, kuma bana so kaga kamar na dameka shi yasa na kasa yi maka maganar” ya gane maganar da take nufi amma sai ya nuna kamar bai gane ba yace “wacce maganar kenan?” Tace “maganar zuwa Kano, kace zamu je tare kuma har yau bamu je din ba, kuma ni ba za’a barni naje ni kadai ba. Na san Baba yana jin maganar ka dan Allah ka tambaye shi ko kai ba zaka samu damar zuwa ba ni sai inje” ya rungume hannunsa yana kallonta, a ransa yana jinjina soyayyar ta ga Adam, ina ma dai zai samu irin wannan soyayyar ta gaskiya, soyayyar da za’a yiwa mutum ko da a bayan idonsa ne. Sai kuma wata magana da Hussain ya taba gaya masa akan mata ta fado masa

“the way to a woman’s heart is through kyautata wa, tausayawa, nuna soyayya da kuma kyauta. In kayi mata haka you don’t need to say I love you, zata gane, itama kuma zata so ka”.

Yace “shine abinda kike so? In munje kano gidan su Adam mun nemi labarin sa zaki ji dadi?” Yadda yayi maganar ya sa ta dago kanta suka hada ido, amma hakan bai hanata gyada kai ba, yace “good, in dai haka kike so to haka za’a yi, zanyi wa Baba magana, in ya amince kuna gama exams sai muje” tace “yaya Hassan muje da weekend din nan mana” sai kuma ta sunkuyar da kanta tace “that’s if you are not busy” ya gyara zamansa yace “am not, amma kinga exams kuke yi, abinda zamuyi finding out a kano zai iya ya taba ki emotionally hakan kuma zai iya taba exams dinki, ni kuma ba zanso hakan ba. Shi yasa nace after kun gama exams sai muje. Kinji?” har cikin ranta taji maganar sa, sai ta gyada kai lokacin da taji tsayuwar sabuwar Napep din da Baba ya siyar da waccan ya cika ya siya kwanan nan, sai ta yashi da sauri ta shige gida, a ranta bata son Baba ya ganta tare da Hassan kar yayi tunanin wani abu.

A ranar Hassan yayi wa Baba maganar yana son zasu je kano da Sumayya su bincika labarin Adam, amma sai Baba ya nuna kin amincewar sa yace “ina so a ji labarin Adamu, amma me yasa lallai sai Sumayya taje? In zuwan za’a yi ai gwara kai din kaje tare da ni ko tare da Sulaiman, amma ita menene nata na zuwa?” Hassan yayi kokarin kare Sumayya, “Baba kasan dangantakar Sumayya da yaron nan, kasan kuma ita zuciya tafi yarda da abinda taji ko abinda ta gani ba wai abinda wani yaji ko ya gani ba, in ba ji tayi da kunnenta ko ta gani da idontaba ba lallai ta yarda ta cire yaron daga xuciyarta ba” Baba ya tsaya yana kallon Hassan yace “ita ce tayi maka maganar sa ko?” Hassan ya girgiza kai da sauri “kawai dai naga kamar hankalin ta har yanzu yana kansa, ina so ne ta samu nutsuwar zuciya” Baba ya fahimci boye laifin Sumayya Hassan yake son yi, kuma yaji dadin hakan dan wannan shine alaka ta gaskiya ba wai kayi ta kokarin kawo karar mutum kana nuna shine mai laifi a komai ba. Sai ya nuna ya amince, ba dan Sumayya ba sai dan Hassan.

Ranar Friday aka yi wa yara hutu sai Hassan ya dawo tare da ƴaƴan sa duk su ukun, ya kira Sumayya a waya yace tazo ta shiga dasu suna ta murna an kawo su gurin mommy, ya fahimci cewa basa banbance Sumayya da Ruqayyah kuma yaji dadin hakan dan baya so su gane Ruqayyah ce ta haife su, at least not now. Bayan ta gaishe shi tana ta murnar ganin yaran suma suna ta makalkale ta sai ya dauko wata yar karamar jaka irin ta computer ya mika mata “laptop, nasan zaki bukace ta saboda project” ta karba da murna, fuskarta tana nuna irin farin cikin da zuciyarta take ciki tace “you are are real life savior Yaya. Kamar kasan yadda nake ta fama da hada project a waya ina ta rigima da yan café. Thank you thank you” yayi dariya, “you are welcome, sai a dage aci jarabawa sosai”

Daga lokacin sai ya samu excuse din kiran wayar Sumayya sai ya nuna mata kamar yaran ya kira su gaisa, wani lokacin kuma sai ya fake da tambayar ta yaya exams, a haka har suka gama exams din, ranar da suka gama a ranar Sumayya ta kira shi da kanta ta gaya masa sun gama sannan ta tuna masa maganar tafiya Kano, sai yace ta fada a gida gobe zai zo ya dauke ta su je, gwara dai suje Kanon nan ko ya samu ta sakar masa mara yayi fitsari.

Data sanarda Baba sai yace “a dawo lafiya. Amma ki sani, ko kun samu Adamu ba zan bashi aurenki ba sai dai in Hassan ne da kansa yace ya janye ya bar masa”

Da sassafe Hassan yazo suka dauki hanyar kano, yana ta kokarin yi mata hira a hanya amma ita hankalin ta yana kan abinda zasu tarar a kanon, wannan shine last chance dinta na samun labarin Adam dan tasan Baba ba zai kara barin ta ta dawo ba kamar yadda ta san ba zai cigaba da kallon ta a gida ba dole zai yi mata aure ko da Hassan ko ma da waye amma dole zaiyi mata aure, ita kuma a yanzu batada wani saurayi dan babu wanda take kula wa duk kuwa da cewa babu ranar da wani a school ko a unguwa ba zai yi mata magana ba amma ita sam bata da interest, bata jin zata iya soyayya da wani idan ba Adam ba.

Ta fahimci duk wannan kame kamen da Hassan yake yi a kanta, tana kuma sane da alkawarin da Baba yayi wa Hassan din kuma tasan babu yadda za’a yi ta ketare maganar Baba musamman im tayi la’akari da abinda ya faru da Ruqayyah, bata so tayi breaking heart din iyayenta ta fama musu ciwon da Ruqayyah ta riga taji musu a zuciyoyin su, dan haka chnace dinta na gujewa auren Hassan guda daya ne shine samun Adam, idan suka sami Adam tana da tabbacin Hassan zai hakura ya bar masa ita wannan kuma zai saka Baba ya hakura da maganar. Amma idan ba Adam ba,bata jin Hassan zai barwa wani.

Hassan bai manta da address din gidan su Adam ba, tiryan tiryan suka tafi har bakin gate din gidan sukayi packing, zuciyarsa cike da abubuwa da dama itama tata zuciyar haka. Kamar yadda yayi tsammani gidan looks deserted kamar babu mutane a ciki, ya dudduba ko zai ga mai gadin da suka gani ranar nan amma bai gashi ba sai ya fita zai he yayi knocking ko yana ciki, a lokacin aka bude gata din gidan sannan wata mota ta fito. Macece a cikin motar, tayi packing kusa da su Hassan sannan ta fito ta koma tana locking gidan. Daga Sumayya har Hassan sai da suka yi mamakin ganin yarinyar, kamar an tsaga kara ita da Adam, ko ba’a fada ba kana gani kasan ciki daya suka fito.

Sumayya ta bude kofar motar da sauri ta fito, a lokacin da yarinyar take kokarin komawa cikin motar ta, Sumayya tace “Assalamu…….. excuse me” yarinyar ta tsaya, hannunta daya rike da handle din mota tana kallon Sumayya sama da kasa tace “hi” Sumayya tace “dan Allah muna tambaya ne, Adam…..amm Joseph muke nema” tana kallon yadda expression din fuskarta ya chanja tace “and who are you if I may ask” Sumayya tace “am his friend, munyi secondary school tare, naji labarin ya bar gida kuma sai naji kamar ance ya dawo shine nake son in ji ko gaskiya ne” yarinyar ta kalli Hassan sannan ta kalli plate number din motar tace “Kaduna. Ba a Kaduna yayi secondary school dinsa ba ai” Sumayya ta rasa me zata ce sai tace “dan Allah……please, just tell me idan yana nan. Is he okay?” Yarinyar tace “he is fine alright, amma ba zaki ganshi ba. Cos baya North and he is never coming back to North, haka Daddy yace, duk family sun koma can nima dan ina karasa school ne shi yasa nake nan” Sumayya ta hadiye wani abu da bata san yaa makogwaronta ba sai yanzu tace “can you at least give me number wayar da zan same shi? Am worried about him” yarinyar ta girgiza kai tace “kune fa, irin kune kuka makala masa addinin ku kuka asirce shi ya bar mu, gashi nan har yau ana ta fama dashi har yanzu bai dawo dai dai ba, how can I just get you together again? If you are truly worried about him ai na gaya miki he is Okay, har an karba masa transfer dinsa ma ya koma school, they are both okay shi da girlfriend dinsa daya tafi da ita” Sumayya ta daskare “girlfriend?” Tace “yes, that beautiful lady daya tafi da ita” sai kuma ta lura da yanayin Sumayya sannan tace “ohhh, ko kema wata girlfriend din tasa ce?” Ta danyi dariya tana girgiza kai tace “he was double dating kenan, amma daga dukkan alama yafi son waccan tunda ya tafi da ita ke ya barki without even a phone number to call him with” daga nan ta bude motarta ta shige ta ci taya tayi tafiyarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button