TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sumayya ta jima a gurin a tsaye har sai da Hassan yazo yace mata “lets go” sannan ta dago fuskar tadata jike da hawaye tana kallonsa, bata ce komai ba ta bude mota ta shiga shina ya zagaya ya shiga suka juya.

Tun da suka shiga mota ta rufe fuskar ta da hijab ta cigaba da kukanta, bai kulata ba shi kuma ya cigaba da driving dinsa. A hanya ya samu bakery ya siya musu snacks da lemo da ruwa ya ajiye mata a kusa da ita ya cigaba da tukin motarsa. Taci kukan ta ta koshi sannan bacci ya dauke ta. A haka har suka kusa shiga Kaduna sannan ta farka ta rarrashi kanta ta goge hawayenta sannan yace “he is fine, alhamdulillah, he is still a muslim, alhamdulillah” ta gyada kai tace “yes, alhamdulillah” sai yace “zancen girlfriend din nan zata iya kirkira ta gaya miki dan kiji haushi” ta sake gyada kai tace “karya take yi, na sani, bashi da wata budurwa karya take yi. But still it hurts me that yana nan lafiya kalau har ya koma school amma be neme ni ya gaya min cewa yana lafiya ba, ni ban damu da wai wani abu da yake tsakanin mu ba, abinda nafi damuwa dashi shine lafiyar sa at least dan hankali na ya kwanta kuma…..” Yace “yanzu kin sani ai, hankalin ki ya fara kwanciya?” Sai tayi shiru bata bashi amsa ba.

Yace “Sumayya shi aure rubutacciyar kaddara ce, matar mutum kaddarar sa ce, idan Adam mijin ki ne dole sai ya zo daga duk inda ya tafi ya aure ki, idan kuma babu aure a tsakanin ku duk kukan da zakiyi duk neman da zakiyi masa ba ba zai aure ki ba ko da kuwa kun hadu din. Idan kuma shine kaddarar ki sai kin aure shi kamar yadda na auri twin sister dinki. Allah ya riga ya rubuta sai munyi aure kuma sai mun haifi yaya har uku da ita. Haka zalika idan da rabon ke ma sai na aure ki, maybe har da zuri’a a tsakanin mu, to babu yadda zamuyi sai hakan ta kasance tunda wani baya auren matar wani kamar yadda wani baya haihuwar yayan wani”

Jin yayi shiru yasa tace “Baba ne yake son wannan hadin” yace “Baba, da Inna da Aunty” ya kalle ta yace “da ni” tayi sauri ta dago jajayen idonta tana kallonsa sai ya daga kafada yace “yes, nima ina so, ke kadai kika rage yanzu, amsar ki kadai muke jira” tana girgiza kanta tace “nayi wa Ruqayyah alkawarin ba zan taba auren ka ba” da mamaki yace “Ruqayyah kuma? Yaushe kuka yi wannan maganar da ita?” Tace “ba yanzu bane ba, tun lokacin kana neman auren ta ta ji Baba yana baka shawarar ka aure ni ka rabu da ita, ranta ya baci a lokacin, and I promised her ba zan aure ka ba saboda in kwantar mata da hankali” Hassan yayi mamakin halin Ruqayyah, wato har labewa tayi taji maganar su da Baba, wato wannan shine dalilin rufa rufar hali da tayi tayi masa tana nuna masa ita ta kirki ce, ya tuno da lokutan da tayi kokarin bata Sumayya a gurinsa, yace “I don’t think a yanzu dai akwai wani alkawari da yake kanki tsakanin ki da Ruqayyah. Mai yasa ba zaki bamu chance ba? Idan ninba mijinki bane ba babu yadda zanyi in aure ki ko da kuwa duk duniya suna son hakan. Just give us a chance muga inda Allah zai kaimu akan wannan maganar.

Tayi shiru tana tunani. Me yasa ne mutanen da tayi trusting the most sune sukayi hurting dinta the most, Ruqayyah, yanzu kuma ga Adam. Few months ya rage mata ta kammala karatun ta, ta san kuma tana gamawa Baba zaiyi mata aure ko da Hassan ko kuma da wani daban maybe ma wanda bata sani ba, kuma ance the devil you know is better than the angle you don’t know, ballantana kuma Hassan is not a devil dan tun lokacin da yana neman Ruqayyah har zuwa auren su da zaman auren nasu ita dai a iyakacin abinda ta sani bata san yana da wani babban aibu ba, duk da dai ance kowanne mutum tara yake bai cika goma ba. Besides, tana son ta farantawa iyayenta rai.

Yayi packing a kofar gidan su ya juyo yana kallonta yace “me kika ce? Zaki bamu dama ko kuma in hakura” ta sunkuyar da kanta tana jin wani iri a zuciyarta, wannan wani decision ne da zaiyi affecting rest of her life, amma kuma kamar yadda yace in ita ba matar sa bace ba bazai taba auren taba. Tace “na amince, zan bamu dama muga inda Allah zai kaimu”.

And so it happened….

Ba wai soyayya ce Hassan sukayi da Sumayya ba amma akwai kulawa da mutum ta juna da aminci sosai a tsakanin su, duk wani abu daya shafe ta yana tsaye akai haka ita ma take yi a nasa affairs din. A hankali suka fara zama abokan shawarar juna musamman a harkar business dinsa wanda yanzu yake kokarin kammala ginin estate dinsa na biyu yayinda ita kuma take final exams dinta. A lokacin ne ya nemi permission dinta na turowa neman aurenta kuma ta amince masa. A take yayi wa Aunty magana wadda ba zaka iya tantance wanda yafi murna tsakanin ta da inna ba, ita ma nan take ta aika Gombe magabatansa suka zo suka tafi Zariya neman auren Sumayya, sai dai a nan ne aka fara samun matsala inda yan uwa da abokan arziki suke ganin rashin dacewar auren nasu musamman wadanda basu san abindaya raba Hassan da Ruqayyah ba. “Ta yaya zai auri Hassana ya sake ta bayan ta haifa masa yaya ta samu nakasa sannan kuma ya auri hussainar ta? Wannan wanne irin cin amana ne?”

Yan gari kuma sai suka dauka da gulma “dan ta samu nakasa shine yayi mata saki uku ya bata gida da kudi a matsayin cin hanci, sannan kuma ya koma zai auri yar uwarta sunkuma iyayen saboda kwadayin kudi suka bashi ita”

Yes, haka rumour din mutane yake, abinda kaji most of the times ba shine abinda yake gaskiya ba. There is more to it than you know.

But wannan bai hana komai faruwa ba saboda su immediate family dinsu sunsan ainahin abind ya faru kuma su suka fi kowa son wannan hadin musamman iyayen su da suke ta saka musu albarka tate da fatan alkhairi duniya da lahira.

Ba’a saka wani dogon lokaci ba kamar yadda Hassan ya buƙata, watanni uku aka saka bayan kammala jarabawar su Sumayya, wannan ma kuma dan Hassan yana bukatar lokacin gyare gyare-gyaren gida ne. Yana son yayi renovating gidansa completely dan ya cire duk wani traces na memory din Ruqayyah. Duk abinda yake gidan sai da aka fitar dashi sannan aka chanjawa gidan fasali yadda komai sanin da kayiwa gidan ba lallai ne ka gane shi ba yanzu idan ka ganshi. Dakunan kasa duk an rushe su sai aka mayar da palukan guda biyu, da nasa da nata, kowa kuma sai aka yi masa stairs din sa a palonsa zuwa samansa, a saman kuma sai aka hade palon sannan aka yi dakin yara a saman. Ta yadda in yayi baki babu ruwanta dasu ita ma inta yi baki ba zasu hadu bama.

Wannan karon Baba ya dage shi zaiyi kayan daki, wannan yasa Hassan ya bude hannu sosai a wajen kudin aure da kudin sadaki dan ya taimakawa Baban ba tare da ya nuna hakan a bayyane ba.

Aunty ce ta siyo lefe kamar yadda tayi lokacin auren Ruqayyah, dai dai gwargwado kamar yadda akayi na Ruqayyah. With that, komai ya gama kammaluwa ranar daurin auren kawai ake jira.

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020

Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800
bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa
Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin AllahNeighbors

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button