TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Gwoggo Habibah ta kira Baba ta gaya masa abinda ya faru ta roke shi ida ya yarda su taho da Ruqayyah gida sai yace “itace tace zata taho? Ta amince da duk sharudda na? Idan ba haka ba ko kofar gida na ban amince ta zo ba”
Ruqayyah taji Abinda Baba yace, sai ta saki hannun gwoggo Habibah ta shige gidan da take kira da matsayin nata a ra ta tana mamakin karfin hali irin na Baba da har bayan wannan abinda yayi mata sannan yace wai ta koma gidan shi, ba san cewa ita a yanzu hanyar da ake bi aje gidansa ma ba zata bi ba. Lissafin da take yi na komawa gida in ta samu lafiya ma yanzu babu shi, sun gama nuna mata karshen kiyayya dan haka su rike soyayyar su ita kuma xata rike rayuwarta. Duk wani ragowar string da take ji yanarike da dangantakar da take tsakanin su yanzu ya tsinke.
Da ta shiga gidan ma bata iya ta hau sama basai tayi zamanta a kasa, kukan ma ta daina yi sai kunan zuciya, bata taba tunanin tana son Hassan ba sai yau, sai data ga shi a matsayin mijin wata, watan ma kuma twin sister dinta. She just can’t imagine, zuciyarta ba zata iya daukan tunanin Hassan da Sumayya a matsayin ma’aurata suna yin duk irin abubuwan da ita da Hassan din suka yi a da ba, the bedroom things, yanzu kuma sai yayi da Sumayya?
Da tace ba zata iya kisa ba, now she is not sure ………
Sumayya tana zaune har mutane suka yi ta mata sallama suna tafiya, yanzu duk wanda bai san dalilin rabuwar Hassan da Ruqayyah ba ya sani ko ma ba’a san complete dalilin ba amma an san ita ta zabi ya bata kudi ya sake ta. Hussain already yayi bacci a cinyar ta, sai ta dauke shi a kafadar ta ta tafi dashi sama ita da Zulaihat, sauran kawayensu duk sunyi musu sallama sun tafi musamman saboda ganin dan hargitsin da aka yi sji yasa basu tsaya siyan baki ba.
Sumayya ta saka Zulaihat ta nuna mata dakin yara a saman, ta nuna mata sannan ta nuna mata nata. Ta shiga tana kallon tsarin dakin, sam baiyi kama da na Ruqayyah ba, kayan Ruqayyah sunfi tsada amma ita a idonta sai taga nata kayan sunfi kyau kuma sun dace da ita sosai. Ta kwantar da Hussain akan gado ta sannan ta koma da niyyar tahowa da Aminu da Yusuf sai Zulaihat tace mata “a ina kike tunanin zasu kwana? Wannan din ma ba lallai Aunty ta bar miki shi ba. Sai kin gama cin amarci tukunna za’a kawo miki shi” ta fada da sigar tsokana.
Sumayya ta marairaice “dan Allah kinga yayi bacci, kar a tashe shi kansa yayi ciwo ki tafi dasu Aminu kawai, a barshi shi yayi baccin sa anan” Zulaihat tace “ni dai babu ruwana, zan tafi dasu amma in aunty ta lura baya can na san zata aiko a dauke shi” Sumayya tace “ba zata lura ba ma” a haka sukayi sallama Zulaihat ta kama hannun twins suna ta bacin rai su a gurin mommy zasu kwana, suka tafi.
Ta koma sama dakinta ta shiga ta zauna a kan gado ta saka Hussain a gaba tana kallon sa, amma ba wai shi take kalla ba zuciyar ta tana saka mata urin rayuwar da zata yi a gidan nan tare da Ruqayyah a matsayin makociyarta, da kuma rayuwar da zasu yi da Hassan a matsayin miji da mata.
Bata an kara ba taji an bude kodar dakin an shigo, ta dago kai tana kallon Hassan shima daya tsata yana kallon ta, ta sunkuyar da kanta kasa tana shafa kan Hussain daya sauke ajjiyar zuciya ya cigaba da baccin sa, Hassan yace “ina kawayen naki?” Tace “sun tafi. Kai ina abokan ka?” Yace “sun tafi” sai ya karaso ya zauna akan side drawer yana kallon ta, ita kuma bata kalle shi ba sai kirjinta da yake dukan tara tara.
Ya kalli Hussain yace “shi wannan me yake yi anan?” Ta kara jawo Hussain jikinta tace “yayi bacci ne, shine nace a bar min shi ya kwana anan” ya girgiza kai, “ki ce in koma in bude kofar gida kenan, dan na tabbatar Aunty sai ta aiko an dauke shi” Sumayya tace “ba zata lura ba, dan Allah ka barshi ya kwana anan dan Allah” ya bita da kallo, a tsorace take sosai, sai kara kankame Hussain take a jikinta kamar zata tsaga kirjinta ta saka shi a ciki.
Sai ya mike tsaye yana kallonta yace “shikenan, in kwanan nasa anan zai faranta miki” ya danyi faking hamma yace “sai da safe”
Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020The Sixth Wave
Kanta yana kasa tace “Allah ya bamu alkhairi” tana jin sa har ya fita ya rufo mata kofa sannan ta dago kai tare da sauke ajjiyar zuciyar da take ta rikewa. Ta tashi tayi locking kofar sannan ta dawo ta dauki Hussain ta kaishi toilet sannan ta dawo dashi ta kwantar dashi itama tayi shirin kwanciya duk da tasan ba bacci zata iya yi ba, kukan Ruqayyah dazu ya taba ta, ta tina rabon da ta ganta tun ranar da Hassan ya sake ta and she ca only imagine abinda Ruqayyah take ji a zuciyarta yanzu. Duk da tasan ba son Hassan Ruqayyah taje yi da gaske ba amma still dole auren su da Hassan sai ta taba zuciyarta sosai.
Ta kwanta tana tuna Adam, sai kuma ta daina tausayin Ruqayyah dan ita ta jawo komai, idan da Adam yana nan da babu yadda za’a yi Baba ya hana shi ita ya bawa Hassan dan tasan Baba yana son Adam kamar yadda yake son Hassan. Ruqayyah ce tayi sanadiyar rabuwarsu dan haka this will be her price to pay.
Ta dauko wayarta tana going through hotunan su kamar yadda take yi kullum, sai data gama gani sai kuma ta koma farko tayi marking all sannan ta danne delete tana jin zafin abin a ranta amma tasan hakan shine dai dai hakan shine zai kara taimaka mata gurin cire shi daga zuciyarta. Bayan ta gama gode hotunan sai ta koma kan messages dinsa da take ta ajjiyar su suma ta goge su sannan ta shiga contact ta goge number dinsa, tasan ko zai dawo ma he won’t be using that same number again.
Sai data gama sannan ta tashi tahe ta dauro alwala tazo ta tayar da sallah, tana gayawa ubangijin ta bukatar ta, and for the first time tun bayan rabuwar su da Ruqayyah sai ta samu kanta da yi mata addu’a tana neman Allah ya shiga lamarin ta ya huce zuciyarta ya daidaita tsakanin su.
Sai da taji bacci yayi mata nauyi har bata iya bude idonta sannan ta kwanta, saboda bata son ta kwanta tayi ta tunani, tana kwanciya kuwa tayi bacci abinta.
Da assuba ta tashi tayi sallah sannan tayi wanka sai ta koma ta cigaba da baccin ta dan sai yanzu gajiyar bikin ta ke sauko mata, duk da dai ba wani dogon biki tayi ba. Motsin Hussain ne ya tashe ta, ta farka ta ganshi ya kafe ta da ido yana ta murna wai yau sun kwana tare, daga nan sai ya saka ta a gaba da zance a dole ta mike duk da baccin ba isarta yayi ba ta ja shi xuwa toilet tayi masa wanka yana tayi mata hira “mommy wai yanzu kim dawo gidan daddyn mu ne? Anan zaki ringa kwana ko? Kin daina kwana a gidan Inna?” Tace “eh” yayi tsalle yana bata toilet din da kumfa “nima na daina kwana a gidan Aunty ko? Tare zamu ke kwana anan da su Aminu ko? To ina suke? Ko a dakin mu suka kwana? Daddy ya kawo mu jibi ya nuna mana dakin mu ya saka mana gado a ciki kowa da nasa yace banda fada. Kinga Daddy shi fada yake yi mana idan munyi fitina, Aunty kuma sai ta bamu sweet tace mu fita backyard muyi ball. Ni ban iya ball ba faduwa nake yi……”
Haka yayi ta zuba kamar fanfon daya lalace ita dai tana tayi masa dariya har ta gama masa wankan tayi masa brush da alwala ya fito ita kuma ta tsaya ta gyara toilet din sannan ta biyo bayansa ta tarar ya jawo drawers din dakin wai yana neman kayansa. Ta goge masa jikinsa sannan ta mayar masa da kayan da ta cire masa saboda bashi da wasu sannan ta saka shi yayi sallah, ya duddungura abarsa duk rabi wasa, ita kuma ta shirya cikin riga da skirt na atamfa da suka karbi jikinta sosai, ta gyara fuskarta dai dai gwargwado sannan ta gyara dakin shima ta dauki Hussain suka fito yana ta yi mata complain din yunwa yake ji “a gidan Aunty ina tashi aunty take bani tea nake sha ba ta yi min wanka sai nasha tea” suka fito tana lakuce masa hanci “ninkuma a gidana sai mutum yayi sallah yayi wanka sannan zai sha tea, in luma mutum bainyi abinda nace ba to zan mayar dashi gidan Aunty” ya kankame ta yana kwabe fuska “ni nafi son gidan nan, nafi son mommy na da Daddy na” ta rike fuskarsa a hannunta tana murmushi tace “nima ina sonka sosai sweetie pie”