TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai taji gyaran muryar Hassan a bayanta, suka juya da sauri, Hussain ya zame daga jikinta ya ruga gurinsa “daddy yau akan gadon mommy na kwana kuma banyi mata fitsarin kwance ba kuma tace a nan gidan zata ke kwana kuma bata bani tea nasha ba sai tayi min wanka” Hassan yayi dariya yana shafa kansa yace “kai, da kai da parrot ban san wanda yafibwani surutu ba. To gaya min gadon mommy da dadi?” Hussain yace “da dadi mana, wankan ta ma da dadi, dama tana yi min wanka in naje gidan Inna shi kuma Baba ya siyo min Mango”

Sumayya tace “Hussain baka gaishe da Daddy ba fa kake masa zance haka” Hussain yace “lah na manta, daddy good morning. Zaka bani tea insha?” Hassan ya dauke shi yace “zan baka, amma sai kayi shiru ka barni mun gaisa da mommyn ka tukunna”

Ya juya yana kallon Sumayya sai taji babu dadi, sai taji Kamar bata kyauta ba data fito babu hijab dan bata jin ta taba tsayawa a gabansa babu hijab. Ta dan rage tsaho ta gaishe shi ya amsa yana studying fuskarta “anya kuwa kinyi bacci sosai? Ko bakunta ce?” Ta danyi murmushi tace “nayi bacci fa” yace “amma ba sosai ba ko?” Tayi shiru, yace “kar ki damu, babu dodo a gidan nan” Hussain daya kwantar da kansa a kafadar Hassan yace “Daddy akwai dodo a gidan aunty, yana nan acikin closet aunty Zulaihat tace duk wanda ya kuma shiga ciki ya buya sai dodon ya kama shi kuma tace yana da manyan hakora da zai cinye mutum dasu kamar haka” ya fada yana kokarin demonstrating a wuyan Hassan, Hassan ya sauke shi yana cewa “a’a kar a fara cinyewa ta kaina a cuci amarya ta” Sumayya ta danyi dariya tace “ban san lokacin da bakin yaron nan ya bude haka ba, maganar sa tafi shekarun sa yawa, biyu da rabi yake yanzu fa” Hassan yace “sai next month ma zai yi two and a half years. Yawo be dashi da surutu da kirinki irin na mai sunan shi. Dama kamar su daya” Sumayya tabi Hussain daua fara tsalle tsallen sa a corridor din da suke tsaye tana tuno late Hussain tace “Allah yasa yayi halinsa” Hassan yace “banda iyayin” tayi dariya, sai ya bi ta da kallo yana jingina da jikin bango, ta hadiye sauran dariyarta tana kokarin kamo hannun Hussain yace “kinyi kyau sosai” Hussain ya juyo yace “yes mommy kinyi kyau, amma na jiki kyau” ta juyo tana kallon Hassan sai ya girgiza kansa yace “too late, har iyayin ya dauko”.

Tana kokarin hada wa Hussain tea sai ga breakfast an kawo musu daga gidan Aunty, a tare da breakfast din akwai Aminu da Yusuf hannayensu ruke da kayan su wai sun taho ana gidan zasuyi wanka. “Mommy ce zata yi mana wanka yau, bama son wankan Aunty Zulaihat” Zulaihat ta dungure musu kai, “kar Allah yasa ku so din, kafin dai ayi daran akayi kwande” Sumayya tayi murmushi “tuba suke yi auntyn yara” sai ta jasu suma zuwa dakinta tayi musu wanka ta shirya su sannan suka dawo suka tarar Hussain ya saka Hassan a gaba da surutu shi kuma sai loda masa abinci yake yi yana ci yana kara wani zancen.

Suka hadu sukayi breakfast tare as a family, sai Hassan yaji bai taba jinsa complete ba irin na yau dan tun da yaran suka fara tashi basu taba samun sun zauna sunci abinci da iyayen su ba. Ko kafin su rabu da Ruqayyah ma mostly kafin ya tashi ta tura su gidan aunty. Suma kuma yaga abin yayi musu dadi sosai musamman yadda Sumayya take tarairayar su kowa yana zuba shagwabarshi son ranshi.

Tare suka gyara gurin da suka ci abincin, har da Hassan shima a dauke plate Sumayya tana tayi masa dariya sannan ya bisu kitchen yana kallon ta tana wanke kayan da suka bata yaran kuma suna tayata kifewa, har layi suke hawa in aka bawa wannan yayi drying plate ya kai cikin drawer sai a bawa wannan cup shima yayi drying ya kai, a haka har suka gama ita bata san Hassan video yake tayi musu ba sai data lura sannan ta rufe fuska tana dariya, sai ya dawo bayan ta ya tsaya sannan ya jera yaran a gabansu yayi musu selfie, Hussain yana ta gyara riga yana dago kai wai dan yayi kyau kuma kar a yanke shi.

Wannan hoton shi ya dora a dpn sa kuma shine abinda Ruqayyah ta tashi dashi a yau. Dama jiya a palo bacci ya dauke ta akan carpet, shima kuma dan ance bacci barawo ne amma da babu yadda za’a yi ta iya yin bacci a yadda take jin zuciyarta. Bata taba shiga bacin rai irin na wannan karon ba, bata jin ko rashin kafarta ya yi affecting dinta kamar yadda auren Hassan to her twin sister yayi affecting dinta. Taji duniyar gabaki daya ta fitar mata a kai, taji tana son mutuwa ko zata huta da ganin wannan bakin cikin amma kuma bata san abinda zata tarar in taje can din ba, a lokacin ta fahimci frustration na matan da suke kashe mazajen su idan sunyi musu kishiya, kishiyar ma da babu dangin iya balle na Baba ballantana ita d mijinta ya auri twin sister dinta, anya kuwa an taba yi wa wata irin cin mutuncin da akayi mata? Kuma iyayenta? Wadanda suka haife ta?

Ta tabbatar cewa Baba ne ya hada wannan kwamachalar saboda dalilin shi baya son aurenta da Hassan dama tun farko, Inna kuma ta zabi tabi bayansa akan ta goyi bayanta ita yarta, ita kuma munafukar Sumayya ta amince, tasan kuma dalilin da yasa Sumayyan ta amince va dan komai bane ba sai dan ta rama rabatan da tayi da Adam.

Sai taji nadamar abinda tayi wa Adam yazo mata, da ta sani ta barshi yayi ta auren Sumayya tunda ita Sumayya bata fahimci gata tayi mata ba, ita tana so ta hana ta auren wanda nan gaba zata zo tayi nadama shine ita kuma ta huce by auren mijinta? Uban yayanta?

Tabbas da ace zata iya kama Sumayya a yanzu da sai tayi mata abinda duk su biyun sai sunji a jikinsu. Tabbas sai tace ina ma ta zabi ta bata ran Baba taki auren Hassan akan auren Hassan da ta zabi yi a yanzu. Sai taji tsanar family dinta a ranta, tsana mai tsanani kamar irin tsanar da take tunanin suna yi mata, tunda zasu iya hada auren Hassan da Sumayya.

Yan aikinta babu wanda ya zauna ya tattashe ta, sannan dama ita babu wanda yake zuwa gurinta ballantana ya rarrrashe ta. Tabbas a ranar tunanin lahirar ta ne kawai ya hanata kashe iamta cikin dare. Sai da assuba sannan ta ja jiki ta hau sama tayi sallah ta kuma kwamta akan sallayar bacci ya dauke ta.

Tana farkawa kuma ta farka da wannan mugun hoton da Hassan ya saka a dp dinsa. Yayanta data haifa da cikinta, mijinta, data sha wahala kafin ta samu, wai duk sun zama na twin sister dinta bayan gata nan da ranta a duniya.

Wannan hoto yafi saran maciji dafi a zuciyar Ruqayyah, yafi kuma kibiya tsini saboda sukar da yayi mata. Kamar yadda ta kwanta da kuka haka ta tashi da kuka tana neman Allah ya dauki ranta ta huta, to me zata yi musu ne ita yanzu? In ma tace zata yi musu wani abu dan ta rama abinda suka yi mata ta yaya zata yi musu bayan ita yanzu sauka kasa ma daga dakin da tayi wa kanta a sama ba karamin tashin hankali bane ba. Sharrin data saba yi wa mutane kuma yanzu ta yaya zata yi musu bayan babu wanda yake sonta hatta iyayen da suka haife ta.

Sai ta tashi ta ja kofar dakin ta rufe, locking herself in, dan bata son ganin kowa bata son kuma jin maganar kowa yau, duk da cewa ma tasan babu wanda zai zo gurinta sai yna aikinta, sai kuwa kawayen ta da sukan dan leko su gnta musamman in rashin kudi ya motsa musu.

Sai dai kuma tana kwanciya taji kukan jaririn nan ya cika gidan gabaki daya, har amsa kuwwa gidan yake yi da kukan nasa. Ta saka hannayenta ta toshe kunnuwan nata tare da rufe idonta”dan Allah kayi hakuri ka rabu dani, kayi hakuri dan girman Allah” amma rufe idon yasa ga ganin gawar Minal a idon nata, kamar kullum ta zuba mat ido tana kallon ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button