TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Tayi saurin bude idon nata taba numfashi sama sama, har wani duhu duhu take gani da wani jiri da yake fibanta duk da cewa a kwance take, ta mika hannu ta bude side drawers ta jawo sleeping pills dinta da kuma robar ruwan da tane ajiyewa permanently a nan saboda bata iya bacci in bata sha ba.

Ta mike zaune tare da bude robar maganin ta debo a hannunta, sai dai maimakon ta debo biyu kamar yadda take sha kullum sai ta devi guda biyar sannan ta watsa su a bakinta ta bisu da ruwa.

Ranar through out Hassan yana gida bai fita ko bakin gate ba, kawai duniyar ce take yi masa dadi duk da cewa ba wai angwancewa yayi da Sumayya ba amma shi gani yake ko haka ta barshi ta biya shi. Yana jin dadin yadda suke yi da yaran, da shima yadda take yi masa, duk da yasan bata sonsa amma ko a fuskarta ba zaka ga alama ba.

Yan uwansu na Gombe suka zo yi musu sallama zasu tafi, ta durkusa har kasa ta gaishe su tare da rufe fuskarta tana jin kunyar tsokanar ta da suke yi, sai ya tuna da aurensa da Ruqayyah rana irin ta yau yadda ta tari yanuwansa, sai yayi mamakin kansa ta yadda bai lura da komai ba a lokacin sai ynazu.

Da zasu tafi Sumayya ta hau samt ta bude lefenta ta debowa yammatan kayan kwalliya masu yawa a leda, manyan kuma ta basu turaruka, suka yi mata godiya kowa yana saka mata albarka sannan ta kama hannun twins dinta suka raka su har bakin gate. Suna ta tsokanar yaran da cewa sunga gidan amarya sun guji Aunty saboda ita tsohuwa ce, Hussain yana ta zuba musu surutu da iyayi har suka tafi.

A daren ranar Sumayya duk yara ukun ta jere akan gadonta tace duk anan zadu kwana, Aunty ta aiko a tafi dasu suka hada kai suka yi ta zunduma kuka su bazasu koma gidan aunty ba, Hussain har da bada sakon a gaya wa aunty ta aiko masa da kayan sakawarsa da kuma kayan wasan sa. Haka Hassan ya saka su a gaba ya zuba tagumi yana kallon yadda suka kankame Sumayya suka bacci, exhausted, saboda kiriniyar da suka yi tayi.

Ya gaji da tsaiwa ya kuma gaji da hamma, yana lura da Sumayya ba bacci take yi ba idonta biyu amma ta rufe ido sai yace “zan tafi in kwanta” ta dan bude ido kadan tace “sai da safe” ya tsaya yana kallon ta sai tayi sauri ta mayar da idonta ta rufe. Ya juya a hankali ya kashe musu fitila ya fita, ba zai taba takura mata ba, yasan tana bukatar lokaci kuma zai bata as much time as possible dan yafi son duk abinda zai faru a tsakanin su ya faru da son ranta ba wai bisa tursasawa ba.

Washegari ma suka tashi kamar jiya, sai dai yau yara suna da school dan haka da wuri Sumayya ta tashe su tayi mudu wanka tana tunanin yadda zata taso Hassan ya karbo musu uniform dinsu a gidan Aunty sai gashi Aunty ta aiko musu har da abinci a lunch boxes dinsu. Dan haka Sumayya ta saka musu kayan ta hada musu tea duk suka sha sannan sai ga Hassan ya sauko dakansa yace zai kaisu duk kuwa da cewa drivern su yazo already, but yafi so ya kai su da kansa dan yanzu fatherhood din yake ji sosai.

Sun tafiya ta koma saman da sauri ta shiga dakinsa, ta yaba da tsaftar dakin sosai dan ba zaka taba cewa dakin namiji bane ba ta gyara masa gadon ta share ta wanke toilet ta fitar da kayan wanki sannan ta koma bata dakin shima ta gyara. Kafin ya dawo har ta kusa gama gyaran gidan, sai ya dage wai lallai sai ya taya ta aikin ta hana shi yakinyarda sai ta bashi duster ya fara goge goge, tana tayi masa dariya, ita sai taga abin mamaki namiji da aiki, hannun sa kamar yayi wa duster din girma, sai shi kuma ya fara bata labarin yadda yake aikin gidansu sanda yana saurayi “Hussain baya komai sai bata guri, ninake yin kusan komai a gidan lokacin su Hassana basu girma ba aunty kuma bata da yan aiki. Har wanke wanke nayi wa aunty. A haka na saba, ni ina enjoying gyaran gida ma sosai sai inji kamar wani responsibility ne daya kamata inyi”

Tare suka gama komai har kitchen ta gyara ta hada wa Aunty kayan abincin da ta aiko musu dashi jiya, kamar hadin baki tana fitiwa dashi ana aiko musu da wani sai ta bayar da na jiya aka tafi dashi sannan ta dauko musu plates suka zauna a kasa akan carpet ta zuba masa zata zuba nata yace sai dai su ci tare, sai taji wani iri dan jiya ma da daddare haka ya dage ta hada musu abinci gabaki daya har yara a tray suka ci gabaki daya, but wancan da yara, wannan kuwa su biyu ne kawai.

Amma bata son yi masa musu, tayi wa kanta alkawarin ba zata ke yi masa musu ba dan haka ta saka chokali a nasa suke ci tare, ya lura a takure take sai ya fara yi mata hira, a lokacin ta lura da wani abu a tare dashi, da wahala yayi dogon sentence ba tare daya ambaci sunan Hussain ba, sai ta tuna da tata twin din, ko a wanne hali take ciki? Ta dauka zata dawo da safe amma shiru har gari ya sake wayewa.

Bayan sun gama ne ya hau sama ita kuma ta gyara gurin da suka bata. Bai jima ba ya sauko yace mata zaije gidan Aunty “zanje gurin Hussain”. She was confused sai daga baya ta tuna a gidan aka binne Hussain, kabarin sa zaije kenan. Sai takara jin tausayin sa sosai, lallai shi din ya hadu da jarabawowi da yawa a rayuwa, lallai shi din abin a tausaya masa ne, lallai yana bukatar mai faranta masa rai a yanzu.

Bayan ya tafi ta koma dakinta tayi wanka ta shirya tsaf da ita ta bade kanta da turare, sannan ta hada kayan wankinsa data dauko da nata dana yara da suka cire da towels din da suka yi amfani dasu duk ta je toilet din yara inda taga washing machine sabo a ciki, ta dauki manual dinsa taga yadda ake amfani dashi sannan ta dauko detergent din da ta gani a toilet dinsa ta wanke kayan tsaf ta matse su, ta zagaya baya ta backdoor inda tasan akwai igiyar shanya tun Ruqayyah tana gidan ta shaya kayan ta dawo palo tadauki wayarta tana duba messages din da kawayenta da kuma yan uwan da basu samu damar zuwa bikin ba suka turo mata.

A lokacin ne aisha ta shigo, tsohuwar yar aikin Ruqayyah ce tun tana tare da Hassan, Sumayya ta tashi zaune tana kallon ta ganin tashin hankali a rubuce a fuskarta. “Aisha lafiya? Aisha ta fara hawaye “Aunty Sumayya dan Allah ki zo, Aunty Ruqayyah tunda ta kwanta jiya da safe har yanzu bata tashi ba. Kofar dakin arufe munyi ta bugawa bata bude ba”

Wani abu ya dunkule a kirjin Sumayya, ya tokare mata hanyar da numfashi yake shiga hunhun ta. Ta mike tsaye tana kallon Aisha “tun jiya? Tun jiya da safe fa kika ce? Kuma ku baku yi tunanin ya kamata ku fada ba?” Tace “dama ita kadai taje zama, mun dauka idonta biyu ko dan bata son a dame tane ya sa ta rufe kofa, sai da muka ga duk abincin da muke kai mata bata tabawa sannan muka fara buga kofar kuma bata bude ba” ta share hawaye, “muna tsoron tayi mana fada ne shi yasa muke gudun damunta”

Cikin karkarwar hannu Sumayya ta dauki wayarta ta fara neman number din Hassan, shine a kusa shine namiji shi ya kamata ta fara kira, kuma shine zai bata izinin fita taga halin da yaruwarta take ciki. Sai dai tasan yana gurin kabarin Hussain ko zai iya daukan waya?

Bugu daya ya dauka “hello Noorie” bata kula da sunan daya kirata dashi ba tace “dan Allah kazo ka taimaka min” yadda yaji tashin hankali a muryar ta haka shima nashi hankalin ya tashi. “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Me ya faru?” Cikin rawar murya ta fada masa abinda Aisha ta gaya mata, bai jira komai ba yace ta fita ta shiga gidan, ta kira mai gadi ko duk wani namijin da yake gidan tace inji shi yace su balla kofar dakin, shima gashi nan tahowa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button