TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Kusan a tare suka je gidan, sai dai da yake shi namiji ne yafi ta doguwar kafa sai ya wuce ta zuwa saman, sanda taje already yana kokarin balla kofar amma being kofar da Hussain ya saka sai taki balluwa. Da sauri ya fita, a lokacin Sumayya ta gama rikicewa kuka kawai take yi tana buga kofar amma babu ko alamun Ruqayyah a ciki, a hargitse ya shiga dakinsa ya binciko key din part din Hussain da ya ajiye sannan ya dawo ya shiga part din Hussain ya nemo spare keys din gidan gabakidaya sannan kuma suka fara neman key din dakin da Ruqayyah take ciki.

A ransa yana cewa gidan da Ruqayyah take so fiye da shi shine zai zama ajalinta in tayi wasa, da kyar suka samu wanda ya bude kofar dakin sannan suka shiga.

Tana kwance a kan gado, idanunta a rufe, a gefenta da robar ruwa da sleeping pills. Da sauri Sumayya ta tafi kanta tana jijjiga ta, sai taga kamar ba Ruqayyan ta ba, kamar wata ramammiya mai kama da Ruqayyah. Hassan ya karaso yana janye Sumayya daga jikin Ruqayyah sannan a hankali ya dora hannunsa a gefen wuyanta yana so yaji heartbeat. Can ya jiyo shi da nisa, she is alive but barely.

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020

Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800
bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa
Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin AllahUnstable

Sorry for the typos

Ya mike tsaye tare da ja da baya, sannan ya dauko wayarsa yayi dialing number din doctor dinsu, ya fita yana waya dashi, wannan ya sa Sumayya ta koma da sauri gaban Ruqayyah ta saka hannun ta a inda Hassan ya dauke nasa tare da kara dan yatsanta na daya hannun a kofar hancin Ruqayyah, ta jiyo heart beat din sannan taji hucin numfashin ta a hannunta amma bayan wannan babu alamar rai a tare da ita.

“Ruqayyah! Ruqayyah ki tashi dan Allah, ki tashi muyi magana dan Allah” tana jim Hassan ya dawo dakin yace “doctor yana zuwa yanxu” bata ce komai ba sai ya karaso ya dauki robar maganin yana karanta wa yace “maganin bacci ne, overdose tayi maybe” Sumayya ta gyada kai tana share hawaye tace “na gane shi, tun sanda ina jinyar ta a asibiti shi take sha kafin tayi bacci, bata iya bacci tsorata take yi duk dare” sai kuma ta fashe da kuka, tausayin halin da Ruqayyah take ciki take yi sosai, wannan wacce irin rayiwa ce yar uwarta ta dora wa kanta.

Tana tuno yarintar su da irin burikan Ruqayyah amma bata taba tsammanin cewa zata kai ta ga haka ba, bata taba tsammanin kaddarar su zata zama haka ba. Ta fara kallon fuskarta tana shafa kanta a hankali tana kiran sunan ta, ga dai kaya masu kyau a jikinta amma shi jikin bashi da kyau, ta rame fiye da tunanin Sumayya, dama kuma ita Ruqayyah bata da jiki sosai. Ta mayar da idonta kan kafarta marar lafiya taga yadda kafar ta kara motse wa ta yamushe kamar ma jini baya zuwa kafar.

Sai kawai ta fara karanto mata adduoi tana tofa mata a haka har doctor din ya karaso suka shigo tare da Hassan, suna shigowa Hassan ya dauki robar maganin ya mika wa doctor din suka yi maganganu sannan Hassan yazo ya kama hannun Sumayya ya daga ta tsaye sannan ya jata suka fito waje. Sai da suka fito palo sannan ya saki hannun, tayi sauri ta saka hannun a cikin hijab tana mummurza shi tana sunkuyar da kanta kasa, ya jingina da jikin bango yana kallon ta yace “wai dan na rike hannunki shine kike wannan abin?” Ta girgiza kai da sauri, amma a ranta tasan haka ne, ita wani namiji bai taba kama hannun ta ba kuma bata taba zaton cewa Hassan mijin twin sister dinta shine zai zama na farko ba.

Da tago kai suka hada ido taga har yanzu ita yake kallo yana murmushi, sai taja hijab dinta ta rufe fuskarta, ita bata san ya akayi yake tsokanar ta har yake murmushi ba bayan ga halin da Ruqayyah take ciki, yana nufin wai shi yanzu bashi da wani concern akan Ruqayyah? Ko babu komai ai sister dinta ce kuma uwar yayan sa. Tace “me Doctor din yace?” Ya dan daga kafada yace “yace zata warke, zai dai duba ta yanzu amma yana tunanin sai an kai ta asibiti sunyi flushing system dinta, in akwai sauran maganin duk zasu fitar mata sannan su saka naya drip sabida ta samu nourishment tunda ta kwana ta wuni bata ci abinci ba sannan kuma a jira sanda zata farka”

Sumayya ta gyada kai hawaye yana tarar mata a idonta tace “me yasa zata yi overdose?” Ya daga kafada yace “Allah masani, maybe ta gaji da duniyar ne” Sumayya ta girgiza kanta da sauri tace “no! She will never do that. Ni nasan Ruqayyah fiye da kowa” yace “really? I don’t think so” ya mika mata hannu “ki zo mu tafi gida” sai ta girgiza kai “ina so in zauna a gurinta, in za’a kaita asibitin ma ina son in bisu can din” ganin kallon da yake mata ya saka ta sunkuyar da kanta tace “in ka amince”.

Yayi ajjiyar zuciya, tabbas yasan akwai soyayya da shakuwa sosai a tsakanin Sumayya da Ruqayyah, amma shi yanzu Ruqayyah tsoro take bashi, yana gudun kar ta cutar masa da matarsa akan kishin da take iƙrarin tana yi duk da yasan cewa na karya ne, ita da bakinta ta gaya masa bata sonsa, ta aure shine saboda tana tunanin mai kudi ne shi. But, ba zai raba hanta da jini ba sai ya tafi ya zauna akan kujera yace “we will wait together then. Bazan taba barin ku tare daga ke sai ita ba” ta biyo shi itama ta zauna tana kallon sa tace “wai kana tunanin Ruqayyah zata iya cutar dani? She is my twin sister, she will never hurt me” yace “she already did hurt you, not once not twice, wanda na sani ma kenan, Allah ne kadai yasan sau nawa ta cutar da ke, bana fatan ta sake wani. I won’t wait har sai ta sake kafin in raba ku”

Tace “nasan akan Adam kake wannan maganar, ita a nata juyayyen tunanin tana ganin kamar taumako na tayi data raba ni da Adam” ya daga mata hannu yace “mu bar maganar Adam please” tayi mamakin yadda ya hade rai, wato kishi yake yi kenan ko mene ne? Amma sai tayi shiru ta bar maganar kamar yadda ya bukata.

Suna zaune sai ta dauko wayarta zata kira Inna ta sanar da ita sai ya hana ta “menene amfanin gaya mata? Hankalin ta ne zai tashi kuma Baba ba zai barta tazo ta ganta ba, ki bari kawai in kin tabbatar ta warke sai ki gaya mata daga baya yadda hankalin ta ba zai tashi ba” ta gyada kai cikin fahimta, tabbas Hassan ya san halin baba kuma yasan cewa in dai har Ruqayyah bata yi abinda yace ba to ba zata shiga gidan sa ba kuma Inna ma ba zata shiga nata gidan ba ballantana shi.

Suna nan zaune doctor din ya fito ya sauka kasa sai gashi ya dawo da kujerar marasa lafiya, Sumayya ta tashi tataimak masa suka dora Ruqayyah akai sannan suka kama shida Hassan suka sauka da ita kasa, doctor din yana cewa “akwai problem gaskiya, I tot zan iya farkar da ita tun anan amma abin ya gagara, dole zamu tafi da ita za’a yi mata some tests.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button