TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Ta zauna akan kujera, rnata yana son kifin nan data gani, kuma tana son tayi masa maganar Ruqayyah ta gaya masa abinda nurse ta gaya mata akan case din Ruqayyah, tana so ta gaya masa abinda nurse ta tsegunta mata na cewa doctor yana tunanin Ruqayyah ta hadu da mental related disorder. Amma kuma ta lura tun da aka fara zancen aurensu har akayi har yau kuma bai taba yi mata maganar Ruqayyah ba, bai ma taba ambaton sunan Ruqayyah ba.
Shin ita tayi masa ko ta barshi kawai tunda baya so……..? Amma mental health din Ruqayyah ai abu ne muhimmanci ko?
Amma sai ta kasa samun courage din yi masa maganar.
Ta mike zata fita yace “ina zaki? Ki zauna inyi wanka in fito sai in sammiki nama ki ci, dan naga kina ta hadiyar yawu” ta dan bata rai “ni na koshi, ni bana cin nama dama, baka sani bane ba” ya fara cire kayansa, ta rufe idonta, yace “amma ai kina cin kifi ko?” Ta girgiza kai “shima bana ci” ya zo gabanta ya tsaya “to me kike so ki ci?” Idonta yana rufe tace “bana son cin komai, bacci kawai nake so inyi”
Numfashin sa taji a fuskarta, tayi saurin jan fuskarta baya sai taji yayi dariya, sautinsa dai dai fuskarta amma ta kasa bude idonta sai da taji takunsa ya matsa sannan ta dan bude idon kadan sannan taga ashe babu komai a jikinsa sai dan karamim towel na kugu, tayi sauri ta mayar da idon ta rufe kirjinta yana lugude, bata taba ganin namiji a haka ba, ko a hoto ko a zahiri.
Wasu abs data gani a kafadun sa su suka saka yayan hanjinta suka kada, yana shiga toilet ta mike da sauri tana jin kifin duk ya fita daga kanta ta fice ta a hardewa kamar zata fadi. Dakinta ta shiga ta rufe kofa ta kashe fitila sannan ta zauna a kasa ta saka kanta a tsakanin cinyoyinta, nasihohin da akayi ta yi mata na hakkokin miji akan matarsa da kuma hakkokin mata akan mijinta.
Bata san tsahon lokacin da ta dauka a gurin ba, ga cikin ta yana kugin yinwa dan abincin rana bata samu ta ci ba tana asibiti gurin Ruqayyah. Kamar daga sama taji an bude kofar dakin sannan aka kunna fitila, ta sake rufe idonta, bata son ta kuma ganinsa babu kaya kamar dazu, sai taji kamshin turarensa sannan ta ji motsin sa ya zo gabanta sannan ta kuma jin hucin numfashin sa a fuskarta, ta sake rintse ido tana cije lebe, sai taji sautin murmushin sa.
“Shine kika gudu ko? Ba zaki ci abincin ba?” Ta gyada kai da sauri yace “to ki zo muyi sallah, ai dai ita sallah ba’a koshi da ita ko?” Bata ce komai ba sai ya hura mata iska a fiskarta, ta kara runtse idon, ya mike tsaye yace “ki bude idon ki, na saka kaya ai” ta bude a hankali sai taga ya saka jallabiya, ta danyi ajjiyar zuciya sannan ta tashi ta bishi suka koma dakinsa suka gabatar da sallar sunna ta ma’aurata, suka gabatar da adduoin samun dacewa a cikin zamantakewar su tare da neman zuri’a mai albarka sannan suka shafa.
Da kyar ya matsa mata ta ci abincin kadan ta sha lemo, duk da cewa shi kansa yasan bata koshi ba amma tsoro da fargaba sun hana ta ci, daga kwashe kayan abincin kuwa ta makale taki dawowa sai da ya bita ya kuma dawo da ita dakin yayi ta fama da ita akan ko hijab din jikinta ta cire amma taki, sai ta saka masa kuka. Ya sake ta ya hau kan gado ya kwanta tare da cewa “good night”
Da sauri ta fita daga dakin ta kuma shiga nata dakin tare da rufe kofa ta jingina da jikin kofar hawate suna bin idonta tana girgiza kanta. Wani bari na zuciyarta yana jaddada mata cewa ba zata iya ba wani barin kuma yana tuna mata da hukuncin laifin da take aikatawa. Tasan ba a son ransa ya kyale taba, kuma da yanayin da yayi maganar kamar wanda yayi fushi, sai ta tuna da abinda ta riga ta sani “duk matar da mijintaya kwana yana fushi da ita akan kin bashi hakkinsa da tayi to Mala’iku zasu kwana suna tsine mata” idan ta mutu a cikin daren nan kuma fa? Menene makomarta?
Sai ta juya ta fita, ta koma dakin nasa ta bude kofar ta tsaya a bakin kofa tana kallonsa hasken security light din daya shigo ta taga. Yana kwance ya lullube har kansa da abin rufa, amma tasan ba bacci yake yi ba kuma tasan yaji shigowar ta, sai ta tsaya a gurin bata ce komai ba, sai taga ya bude fuskar sa yana kallonta sai kuma ya bude abin rufar tasa sosai sannan ya miko mata hannu, ta tafi a hankali ta saka hannun ta a cikin nasa sai ya jawo ta kan gadon da hannu daya sannan ya cire hijab din jikinta da daya hannun, sai kuma ya saka hannayensa duk biyun ya rike fuskarta yana kallon cikin idonta a hankali yace “may I?” Ta rufe idonta tare da gyada kanta a hankali, and she felt his lips on hers together with some kind of feeling da bata taba jin irinsa ba a rayuwarta.
**. ***. *
Washegari da Hussain yazo neman mommyn sa Hassan cewa yayi mommy tayi tafiya sai next week zata dawo, haka ya zauna yaci amarcin sa son ransa su rayan duk sun dauka da gaske tafiyar tayi, sai da sati yayi sannan yaje ya dauko su yace mommy ta dawo, har da tsaraba ya raba musu yace inji ta, su kuwa sai murna. A ranar aunty ta hado musu kayansu gabaki daya suka dawo gidan iyayensu. A ranar ne kuma aka sallamo Ruqayyah daga asibiti ta dawo gidanta bayan gwaje gwaje da akayi mata a karshe likita yayi concluding “mentally unstable”.
Ya rubuta mata magunguna kuma ya bata shawarwari sannan ya hada ta da therapist din da zata ke gani duk sati. Abubuwan da suke damunta sune rashin bacci, halucination, rashin abokin magana, damuwa da kuma shan sleeping pills din da take yi. Yayi suggesting therapist din ne saboda yana tunanin at least zata samu wanda zata ke yiwa magana tana fitar da abinda yake ranta tana rage damuwarta. Ya bata shawarwarin ta koma gida cikin yanuwanta sai tace masa ita bata da yanuwa duk sun mutu.
Sai kuma ya bata shawarar ta nemi abinyi, something to keep her busy yadda kullum in ta tashi she will be looking forward to doing something kuma kafin dare zsta gaji yadda zata fi saurin yin bacci. And she already decided on abinda zata yi, she is going to make money. In mutane ba zasu so ta ba dan Allah to zata siye su da kudi. Tana zuwa gida abinda ta fara yi shine neman number din Umar, yayan Fatima wanda suke partny a H and H sai ta gaya masa tana son shiga business din sosai, tana son ta zama involved a duk al’amuran kamfanin kuma tana son ribar da take samu da share dinta a daina turo mata gabaki daya, ake bata rabi rabin kuma ana sake re investing.
Bayan sun gama wayar ta bude kofar valcony tashiga tana kallon duk saura gidajen unguwar a kasanta dan duk unguwar babu gidan da ya kai na Hussain tsaho. Ta danyi murmushi tana lumshe idonta, hayaniyar da taji a barin gidan Hassan ya saka ta juya tana kallon side din, Hassan ta gani hannunsa rike dana Sumayya suna dariya, sannan ga yayanta suna zagaye su da ball a hannun Aminu, bata jin abinda suke cewa amma duk a cikin farin ciki suke.
Sai taga Hassan ya cire rigarsa ya bawa Sumayya riko sannan sun fita a guje shida yaran suna ball, Sumayya kuma tana kallon su tana cheering dinsu, duk wanda ya buga yaci zai je Sumayya tayi masa kiss, yaran sai rige rigen ci suke yi amma uban yafi zakewa har sai da yaci ya tafi da gudu gaban Sumayya ya durkusa yana dariya ita kuma tayi kissing dinsa a both cheeks.
Ta juya tana barin gurin, ta koma palo sannan ta saka key ta rufe kofar valcony din ta tafi toilet ta jefa key din a cikin toilet tayi flushing.