TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020

Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800
bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa
*Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin Allah
*Home Coming*

Amira ta gode da adduoin ku, ni kuma na gode da fahimtar ku. Allah ya bar kauna ya kuma bar zumunci. Nagode sosai

Washegari Ruqayyah ta fara ganin therapist din da aka hada ta dashi. Dr Mahmud. Shi yazo har gidan ta suka zauna a kasa, he talked to her, trying to get her to talk amma babu abinda tace masa mai amfani har awa dayan da yayi scheduling for her ta kare sai yayi mata sallama ya tafi.

Daga lokacin kuma ya cigaba da zuwa duk sati suna zama suna hirata awa daya,a lokacin ya fahimci abubuwa da yawa a tare da ita, na farko akwai abinda da take boyewa a ranta, abinda ba zata bata iya fadawa kowa ba kuma yana tunanin wannan abin shine sanadiyyar shigar ta halin da take ciki, na biyu tana halucination, ma’ana tana gani tana kuma jin abubuwan da basa guri a lokacin, sai dai bai sam yaushe ne ta fara gani da kuma jin haka ba.

Ya kuma fahimci tana da high spirit, a never giving up spirit wanda baya jin zata yi giving up akan abinda ta saka a gaban ta kuma a yanzu abinda ta saka a gabanta shine business, sai ya bata shawarwaro tare da kara mata karfin guiwa akan hakan, dan yana ganin hakan sai kara mata mental health dinta wanda a gurinsa shine top priority dan aikinsa kenan.

Ita kuma sai ta kara kaimi, ta sake neman Umar akan maganar da suka yi kuma ya nemi su hadu a cikin kamfanin sak ta shirya taje, with crutches and all, for the first time taji bata damu da kallon da mutane zasu yi mata ba cos tana da missing, ta san abinda take so and she is going to get it. So take ta saka duk wadanda suka guje ta su fahimci irin mistake din da suka yi sannan su dawo gareta.

Umar ya amince mata a game da harkar H and H, ya bata office dimda zata ke zuwa kullum ko kuma duk sanda tasamu dama, sannan kuma za’a ke briefing dinta na duk abinda yake faruwa a kamfanin. She accepted that, sannan ta karbi copy din duk takardun da suka shafi harkokin H and H ta tafi dasu gida, daga nan ta mayar da hankali sosai wajen karantawa da fahimtar duk yadda al’amurran kamfanin suke tafiya, and then she got enrolled in online business classes, giving it her all, and within a year sai gata ta san komai da yake shiga kuma yae fita daga H and H.

A shekara ta biyu sai ya kasance Sau dayawa ma Umar yana bar mata ragamar kafanin tacigaba da juyawa saboda shi yafi mayar da hankali akan sarauta da ita yake so, business kawai yana yi ne dan ya cika aljihun sa but not because yana da interest akai. Ita kuma ta cigaba da investing, sai ga kudi suna ta multiplying kamar an saka musu yeast. A yanzu har bata damuwa da kudin da take biyan mai duba dashi dan bashi da wani yawa a cikin kudin da take samu.

Yes, wannan ua taimaka mata sosai gurin rage mata damuwa da yawan tunani, amma har yanzu yaki ya yalwata mata zuciyarta, ga kudi dai har kudi tana samu, ga yalwataccen gida ga kuma yalwataccen account amma zuciyarta kullum a kuntace take jinta. Sai tayi tunanin kadai ci ne, dan haka ta gayyato all her friends, duk wanda take buƙatar gurin zama ta taho ta zauna, wasu ma daga gidan iyayensu suka fandare suka dawo gidan Ruqayyah da zama ita ce cinsu ita ce shansu ita ce komai nasu wai dan kawai tana so su cike wani rami da take ji a zuciyarta amma sai taji ramin yaki cika.

Sai kuma ta yi tunanin ko dan nakasar da take da ita ne, sai ta dukufa gurin ganin ta nemo likitan da zai taho daga kasar waje yazo har gidaya duba ta amma ta rasa, ta samu guda biyu sunzo baya ta kashe musu uba kudi amma sai da suka zo suka ganta sannan suka gaya mata ba zasu iya duba ta ba sai da kayan aiki, kayan aiki kuma suna can kasar waje ba zasu iya dauko su su taho dasu ba. Sai dai kawai suyi mata prescribing magani wanda har yau babu abinda yake kara mata.

Ita kuma har yau ta kasa taking risk din sake shiga jirgi balle tabi su can. And she misses fita kasashen duniya musamman ida kadaici yayi mata yawa kuma ta gakudi account dinta sai taji babu abinda take so irin ta keta hazo zuwa wata kasar kamar yadda Hussain yake yi a duk lokacin da yayi niyya.

A duk tsahon wannan shekaru ukun da auren Hassan, shekaru biyar da mutuwar Hussain, babu moment guda daya da Ruqayyah ta daina jin kikan jariri a kunnen ta, babu kuma lokacin data rufe idonta ba tare da taga fuskar Minal ba, duk kuwa da magungunan da take sha wadanda likitan ta yake ganin zasu taimaka mata but it is getting worst everyday. Sai ya zamanto zuciyarta ta kara bushewa ma yanzu bata jin tsoron abubuwan da take gani da ji.

Kullum tana sak ran Fatima zata dawo, tunda akwai chances na cewa she is alive duk da dai rashin ji daga gareta na tsahon shekaru biyar ya saka ta fara kwantar da hankalin ta da tunanin maybe ta mutu da gaske. Ita bacewar Fatima is a mystery agurin ta, dan ita har ga Allah sanda Fatima ta bata baby bayan ta haihu data ta bata bata ji alamar rai a tare da ita ba, wannan shi ya kara mata karfin guiwar yar da jaririn. Amma duk da haka ta yanke wani hukunci a ranta.

Duk ranar da Fatima ta dawo, that’s in zata dawo din, zata tubure tace ita Fatima bata bata jariri ba, it will be her word against hers tunda babu shaida, babu wanda akayi a gabansa dan haka da wahala alkali yayi convicting dinta. Zargi ne kawai, mutane zasu zarge ta yan uwa zasu kara nisanta kansu da ita amma sai dai suyi tayi, ba zata yi asara goma da ashirin ba, ba zata taba furta abinda tayi ba ballantana ta rasa dukiya da kuma freedom dinta. Yes, wannan shine abinda zata yi.

Kanenta maza ne kawai suke kai mata ziyara sometimes, duk da cewa ta fahimci Inna Ade ne take turo su su duba lafiyar ta ba da sanin Baba ba. Tana jin dadin zuwansu sosai duk da bata nunawa amma tana jin dadin yadda taje jin labarin gida a gurinsu, ta fahimci kowa yana lafiya, sannan a gurin su ta ji labarin haihuwar Sumayya, amma duk da yadda suka so su jata ta shiga gidan taga baby sai taki zuwa. Bata jin akwai tsautsayin da zai kaita gidan Sumayya ballantana har taga abinda zai saka zuciyarta ta buga. Wanda ta riga ta gani ma is enough.

. . **

Shekaru uku sun wuce bayan auren Hassan da Sumayya, rayuwa mai kyau suke shimfidawa abinsu tamkar basu da sauran wani problem a duniya. Sumayya ta gama karantar Hassan kuma ta taya yar uwarta bakin cikin rasa miji irin Hassan ta kuma yiwa kanta murnar samun miji irin Hassan. Hassan irin namijin nanne da in suka samu abinda suke so a gurin mace su kan iya zama tamkar bayi a gun matansu. Ta fahimci abinda yake so din kuma, na farko yana son respect, baya son raini ko kadan duk kuwa da cewa yana da wasa da dariya amma yana so a girmama shi, yana son other room sosai da sosai dan baya taba bari ya wuce shi indai ba da wani kwakwkwaran dalili ba, ita ma kuma sai ta fahimci ashe tana so din, dan haka sai suka kara makalewa da manne wa juna ta wannan bangaren.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button