TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai kuma ta fahimci baya son rainuwa kuma ya tsani mita, and she wondered yadda har suka iya rayuwar aure ta tsahon shekara biyu shida Ruqayyah dan ita a rayuwarta bata taba ganin mutum mai mita mai kuma rashin godiya ba irin Ruqayyah. Lallai Hassan ba karamin hakuri ne dashi ba, kuma tabbas ba karamin so yayi wa Ruqayyah ba.

Basu jima da aure ba aka yi posting din ta a service, aka tura ta bayelsa, amma haka Hassan ya shige mata gaba har sai da aka dawo da ita nan Kaduna musamman saboda a lokacin tana fama da laulayin ciki. Sai ta fahimci cewa shi din tsayayyen mutum ne irin wanda zaka iya gayawa problem dinka ya tsaya maka har sai kun samu solution. And she wondered yadda akayi Ruqayyah take kiran sa da matsolo. A gurin Sumayya sam Hassan bashi da maƙon kudi kawai dai baya son almubazzaranci, baya son unnecessary spendings, irin mutum ya sayi abu ba tare da yana bukatar saba, ko ka sayi abu kawai dan kaga wani ya siya kai ma sai ka siya dan ace kana da shi, amma kuma duk abinda yake da amfani Hassan zai siya in abundance, dan kayan abinci drinks fruits kala kalan nama har sai tace sunyi yawa kar su lalace. Musamman duk abinda ya fahimci cewa tana so ko kuma yaran suna so to ya ringa siyowa kenan. Kuma ta lura haka yake yiwa su Aunty ma, kafin su nemi abu ya kai musu shi indai yasan suna bukatar sa. Baya sai ya Aunty gwala-gwalai, baya chanja wa kannensa waya duk wata irin yadda Hussain yayi musu but yana kula da dukkanin bukatun su yana tsayawa a duk kanin al’amuran su kamar yadda ya tsaya a auren Nafisa bayan ya tabbatar yayi mata securing aikin da zata mori ilimin ta dashi, babu wanda zai ce marainiya ce dan Hassan ya cike gurbin uba a gurin ta kuma a yanzu yana kan cike wa a wajen Zulaihat dan ya matsa mata number akan ta fito da miji haka nan tunda har sun gama service dinsu.

A bangaren Hassan kuma bayan abinda ya faru tsakanin sa da Ruqayyah bai taba tsammanin zai samu farin ciki a rayuwar aure ba amma sai gashi ya samu more than abinda yayi tunani ma. Sumayya ta kawo haske sosai cikin rayuwarsa shi yasa ya makala mata suna “Noorie”. A yanzu ne kuma ya gaskata maganar Baba, a yanxu ne kuma ya fahimci mistake dinsa na danganta wani category na mutane da munanan halayya.

Tabbas auren sa da Ruqayyah tamkar lesson ne ubangiji ya koya masa kuma ya dauki darasi sosai, sannan kuma aurensa da Sumayya shi kuma sakayya ce Allah yayi masa saboda yadda ya bude hannayensa duk biyun ya karbi kaddarorin rayuwarsa tare da gode Allah a bisa niimomin sa.

Gasu dai Sumayya da Ruqayyah tagwaye ne, uwa daya uba daya, ciki daya mahaifa daya, sun kuma sha nono daya a lokaci daya, sun rayu a guri daya, an yi musu tarbiyya iri daya sun kuma samu ilimi iri daya, hatta cup da plate din da suka ci abinci sanda suna tasowa iri daya ne gashi kuma kamannin su daya amma banbancin halayyar tamkar banbancin dake tsakanin annabi da kafiri ne. Kamar ace positive and negative sides of a battery ne.

Shine zai bada wannan shaidar sama da kowa tunda shine wanda yasan in and out of them, shi yayi zaman aure da duk su biyun a mabanbanta lokuta.

Shekarar farko ta bayan aurensu Allah ya azurta su da haihuwar da namiji wanda suka saka wa Abdullahi.

Tabbas, a farkon auren su har zuwa yanzu ma da suke shekara uku da yin aure sukan fuskanci financial problems, saboda Hassan yanzu ba ya aikin da zai ke samun albashi duk wata, sannan auren da yayi da kuma auren da yayi wa kanensa har biyu Khadijah da Nafisa ya dakatar da harkar gine ginen sa, estate din nan ta farko dai har yanzu ita ce, har yanzu bai samu ya kammala ta biyun ba, kuma gidajen yearly suke biyan sa rent ba monthly ba dan haka dan ma dai shi mai kulawa ne da lissafi a komai shi yasa har suke samun condition din da suke ciki a yanzu.

Akwai lokacin da har sai da ya siyar da motar sa yake hawa ta haya saboda rashin kuɗi, amma fa iyalinsa basu taba zamada yunwa ba. Sai Sumayya ta bashi shawarar kafin ya kammala wannan ginin ya yi shaguna a gaban estate din sai ya saka musu monthly rents yadda duk wata zai ke karbar wani abu, sannan itama kuma ta nemi ya amince mata ya nema mata aiki amma sai yaki yadda da maganar aikin duk da cewa ya ji dadin waccan shawarar data bashi ta shaguna, dan haka sai yace mata ya bata aiki a karkashin sa a matsayin personal adviser dinsa, zai ke bata salary duk wata, ita kuma taki yarda tunda already yana bata kudin da suke isarta yin duk bukatun ta.

Shi kuma sai yaji babu dadi, dan yasan yadda Baba yasha wahala akan karatun ta ya kamata ace iyayenta sun mori ilimin ta amma sai dai shi baya son ace matarsa kullum sai ta fita gurin aiki, baya son abar tarbiyyar yayansa a hannun yan aikin gidadan haka sai ya mayar mata da matsayin ta zuwa secretary dinsa sannan yayi mata office dinta anan cikin gidan su inda anan ne suke ajjiyar duk wasu takardu da duk wasu bayanai da suka shafi business dinsa, ta ce mai kula da komai. Sai ta karba saboda tana ganin aikin zata yi ai ba wai bada shawara kadai ba, kuma tasan idan ma bata karba ba dole zai dauki wani ko wata a wannan matsayin.

Kiri kiri Hassan ya hana ake kai su Aminu gidan Ruqayyah, yace “I don’t want them getting confused su kasa gane wacece mommy din a cikin ku. In sun girma sun fahimta da kansu zasu je but not now” a dole Sumayya ta amince da hakan ba dan zuciyarta tana so ba sai dan bata taba yi masa musu, ko abu taga yayi va dai dai ba bata musa masa directly sai dai indirectly ta kawo masa shawarar da zata rushe waccan maganar ba tare da ya fahimci abinda tayi ba.

Wannan kenan……………

Bara mu leka Kano. Shekaru biyar bayan mai martaba Sarkin Kano tare da yayansa sunje sun binne konanniyar gawar mace da ciki, wadda suka yi tunanin ta yarsu kuma yaruwarsu gimbiya Fatima ce. Experience din da har yanzu yake fresh a zuciyoyin al’ummar gidan musamman mahaifanta.

Ana tsakiya da hidimomin yau da kullum kamar yadda aka saba, sai ga baki sunzo a airport taxi, tun daga bakin gate aka tsayar dasu ana tuhumar su da su fadi daga inda suke kuma wa suke nema. Hakan ya faru ne saboda lura da akayi da cewa ba hausawa bane ba, duk da cewa ba za’a iya fadin direct wanne addini suke bi ba.

Na mijin da yake gaba tare da driver ne yayi Magana

“Sunana Adam, ina son ganin maimartaba sarki”

Kallon da dogarin ya watsa masa ne yasa yayi saurin chanja maganar sa “ko kuma wani a cikin manyan gidan wanda yake kusa”

Dogarin ya kuma bata rai, gashi dai hausa yake yi amma yafi kama da inyamuri. “Me zaka yi musu in ka gansu?” Adam ya dauke kai, dama yasan haka zata kasance, shi yasa ya nemi da su fara aiko da sakon zuwansu kafin suzo dan shi baya ciki da wulakanci, zai iya fita yanzu ya wanke dogarin nan da mari. Ya hadiye bacin ransa, wai me yasa kananan ma’aikata suke da wulakanta mutane ne bayan su kuma manyan nasu ba haka suke ba.

Cikin bacin ra yace “kwadon su zanyi in cinye. Ina ruwanka da abinda zanyi musu, ji nake kai aikinka shine isar da sako kuma na baka sako ka tsaya kana bata min lokaci da tambayoyi marasa amfani” shima dogarin ya kufula “an bata maka lokacin, aikina ba isar da sako bane ba tunda ni ba masinja bane ba, aikina shine kula da lafiya da dukiyar mai martaba tare da iyalinsa, kai kuma kayi kama da marasa gaskiya shi yasa na tsare ka na hana ka shiga, kuma ko duk garin nan zasu taru wallahi ba zan barka ka shiga gidan nan ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button