TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Adam ya dube kofa ya fita “amma lallai zaka shirya yin azumi uku kenan na rantsuwar da kayi dan shiga gidan nan kamar nayi ne na gama ko kana so ko ba ka so, ko zaka bude kofa ko ba zaka bude ba ni dai sai na shiga, and I will be talking to the emir while you will be fasting saboda rantsuwar da kayi” dogari ya daga kafada yace “kai ka san me kace a karshe. In ma zagi na kayi to kai ma haka. Ni dai kofa ce ba zan bude ba sai dai ka fadi abinda zaka fada anan, in naji mai ma’ana ne in aika a fada a ciki, in marar ma’ana ne kuma in koma ciki in barka anan kayi ta maganganun ka kai kadai”

Adam yace “Ni ai da masu gidan nazo inyi magana, ma’ana mamallaka gidan ba masu saka ja da koren kaya suna tsayawa a kofar gida ba” dogari yace “in ma baki da fari ne mun saka din, gida ne dai ba zaka shiga ba”

A hankali aka sauke glass din tagar baya na motar, sannan kyakykyawar fuskar Fatima ta bayyana. Tana nan babu abinda ya ragu daga kyawunta sai ma fari data yi saboda chanjin weather, sai kuma rama da tayi sosai, ga wanda ya santa zai iya cewa ta kankance ta koma kamar sanda take secondary school, yanayin takuma yayi kama da yanayin marar lafiya. A tare da ita akwai wata mata wadda kana ganin ta kasan ita ta haifi Adam. Ta kare wa dogarin da suke cacar baki da Adam kallo, ta gane shi tsaf dan rayuwarta a gidan su bata daga cikin abubuwan data manta. For years, shine dogarin da yake gadin gate din farko na gidan, sannan tace “Auwal dogari” ya juyo da sauri jin an ambaci sunansa, suka hada ido sai ya makale a yadda yake, baki a bude yana kokarin mayar wa da Adam magana, tace “dan Allah ka bude mana kofa mu shiga” ya rufe bakin sannan ya mitstsika idonsa da sauri sannan ya sake kallonta, anya tsufa bai fara kama shi ba kuwa? Wannan kamar gimbiya Fatima fa. Gimbiya Fatima data mutu shekaru biyar da suka wuce.

Cikin rawar murya yace “gimbiya Asma’u?” Kanwar Fatima ce wadda suke yanayi. Fatima taji zuciyarta ta amsa da jin sunan kanwar ta, taji ta kosa da taga iyayenta da yanuwanta, ta kosa taga dan jaririn ta. Tace “ba Asma’u bace Auwal, Fatima ce” sai ya saki bulalar dogarai da take hannunsa, ya sake matsowa yana kuma lekawa cikin motar sannan kuma sai ya zabura kamar wanda akayi wa allurar karfi ya fita a guje, bai bude kofar gate din ba sai ya wuce cikin gidan a guje, ba zai bari wani ya riga shi kai wannan maganar cikin gida ba.

Sai dai yana shiga gate din gida ya fara kururuwa “jama’a ku zo ku taya ni gani, gimbiya Fatima ce gata can a cikin mota tare da inyamurai. Jama’a kuzo ku tayani dubawa ko ido na ne yake yi min gizo” nan take mutane sukafara cincirindon zuwa inda yake wasu kuma suna wucewa bakin gate, sai dai daga zarar sun ga abinda ya gani sai su koma da baya suna neman suma wadanda zasu gayawa.

Ganin haka yasa Adam ya tafi da kansa ya bude gate din gidan sannan drivern ya shigo da motar suka zarce zuwa gurin da aka tanada dan packing din motocin baki. Suka bude suka fito su uku sannan Adam ya biya drivern, yana tuna lokacin da shima yake a matsayin drivern taxi.

Fitowar Fatima ya saka sauran mutane suka karasa hargitse wa, wannan hayaniyar ce Adam baya so shi yasa yayi plan din neman audiance da mai martaba sarki ko wani mai fada aji direct yadda za’a yi maganar a tsanaki. Baya son hayaniyar tayi affecting Fatimah, not now, not when ta fara samun lafiya.

Suka fara tafiya, Fatima tana yi musu jagora dan babu abinda ta manta a tsarin gidan nasu, Maman Adam tana rike da ita, supporting her, irin rikon da akeyi wa marasa lafiya. A haka suka doshi cikin gidan, duk inda suka wuce sai mutane su dare su basu hanya, wasu kuma su fita a guje. Har suka isainda Adam ba zai iya wucewa ba sai ya dakata yana jin kamar ya bisu amma babu dama dan haka yace “Mama” maman sa ta juyo tana kallon sa sai yace “take care of her please” sai tayi murmushi ta gyada masa kai ba tare da tace komai ba.

A cikin gida, a dan karamin shamakin da yake tsakanin bangaren Hajiya Fulani mahaifiyar Fatima da kuma Hajiya umma abokiyar zamanta, kamar kullum da yamma, yau ma suna zaune tare a karkashin bishiyar da take gurin suna shan fresh air tare da jin labaruka daga barorin su.

Hajiya Fulani kawai jinsu take yi amma bata fahimtar hirar da suke yi, ita yau bata jin dadi sosai gabanta sai faduwa yake yi, dama kuma ita ba lafiya xe ta ishe ta ba dan tun lokacin da labarin rasuwar yarta Fatima ya iske ta, ballantana kuma jin irin mummunar mutuwar da tayi, tun daga ranar har yau bata kuma kasancewa cikin farin ciki ba, bata kuma jin wani labari dazai saka ta farin ciki ba, bata kuma jin dadin rayuwa ba, tana yin rayuwa ne kawai dan da akwai rai a jikinta.

Sai da yawa ta kan ce “ni kullum sai inke jin kamar Fatima zata shigo gidan nan, har jin taku nake yi kamar nata” sau da yawa idan tayi wannan maganar sai mai martaba ko kuma duk wanda tayi wa maganar ya amsa mata da cewa “ai dama dole zaki ke jin haka, tunda baki ga gawar ta ba, kullum gani zaki ke yi kamar bata mutu ba zata dawo”. In mai martaba ne sai ya kara da cewa “ni ma kaina dana binneta da hannu na ji nake yi kamar ba ita na binne ba, tunda babu sauran wasu kamannin ta a tare da ita”.

Yau ma wannan feeling din take ji, kamar Fatima zata zo ta zauna a tsakiyar su kamar yadda ta saba yi in dai tana gidan. Takan ce “tsakiyar ku yafi dadin zama, in juya duk ta side din da nake so in kwanta akan cinya”.

Hayaniyar da gidan ya dauka shi ya katse labarin da wata baiwa take basu, sannan kuma sai ga wasu bayi su biyu sun shigo gurin a guje kamar an koro su, jakadiya ta mike “kai! Lafiyar ku kuwa? Wanne irin rashin hankali ne haka?” Suka zube a kasa suna tuba sannan daya tace “wata mata muka gani yanzu mai kama da gimbiya Fatima” Hajiya Fulani ta mike tsaye, Hajiya umma ta mike itama tana tambayar “a ina? Ko yar uwa ce?” Sai suka ce “gasu nan zasu shigo nan gurin ita da wata mata, kowa gudu yake yi in ya gansu, kamar an tsaga kara ita da marigayiya”.

Hajiya Fulani ta fara tafiya da sauri zuwa hanyar shigowa gurin daga waje, zuciyarta tana gaya mata Fatima ce ba mai kama da Fatima ba, kafin ta karasa su ka shigo, Fatima a rike a hannun Maman Adam. Kallo daya tayi mata tasan cewa yarta ce Fatima, tasan cewa gawar dasu Mai martaba suka binne bata Fatima bace ba.

A hankali Fatima ta saki hannun Maman Adam sannan ta mika wa Hajiya Fulani hannu tace “Hajiya ta, umma na na dawo gida”

Jin muryar ta ya tabbatar wa da Hajiya Fulani cewa Fatima ce, mai makon ta amsa mata ko kuma ta kama hannun data mika mata sai ta zame ta yanke jiki ta fadi.

Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020

Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800
bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa
Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin AllahBack From The Dead

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button