TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Appreciate this please……
Cikin mintuna da basu kai talatin ba gaba ki daya gidan sarautar kano ya hargitse, masi gudu nayi cike da tsoro da fargabar sunga fatalwa, wasu kuma suna tahowa da gudu dan gani ya kori ji, suna so si tabbatar wa da idanuwan su cewa gimbiya Fatimah data mutu shekaru biyar itace yanzu ta shigo cikin gidan da kafafuwanta.
Fatima ta karasa cikin sassarfa ta durkusa a gaban hajiya Fulani tana girgiza ta kadan “Hajiya? Hajiya ta?” Umma da tun shigowar Fatima ta daskare a gurin ta matsa inda Hajiya Fulani ta fadi ganin cewa jakadiya da sauran barorin da suke gurin duk sun tsorata sun ki zuwa gurin. Ta jijjigata sannan ta dauko robar ruwa ta yayyafa mata tana kiran sunanta har suka ji ta sauke ajjiyar zuciya sannan a hankali ta bude idanunwanta, ta sauke su akan Fatima datake rungume da ita tana hawaye “Fatima? Fatima zahra ke ce wannan a duniya ko dai mutuwa nayi nima nake ganin ki a can?” Fatima tace “hajiya nice mana, baki gane ni ba ko? Na rame ko? Rashin lafiya nayi sosai. Nasan kuna ta nemana duk shekarun nan” sai ta kara kukan ta tace “nima ina ta neman ku Hajiya, ina ta so in taho gurin ku amma babu dama”.
Umma da take jin su ta kamo hannun Fatima tace “mu bama neman ki Fatima, mu bamu taba neman ki ba ko sau daya saboda mu ce mana akayi kin mutu, mu a gurin mu kin mutu dan har anyiwa gawarki suttura an binne ki”
Fatima ta bude ido cikin mamaki, sai kuma ta waiga tana kallon yadda kowa a gurin yake kallon ta,wasu tana hango tsoro a idonsu. A lokacin Asma’u kanwarta ta shigo gurin, ita ma labari ya iske ta a dakinta cewa Fatima tayo fatalwa tana yawo a gidan, tana shigowa kuwa taga Fatima a durkushe kusa da iyayen su, ai kuwa sai ta zunduma ihu ta juya a guje, Fatima ta mike “Asma’u? Asma’u Fatima ce fa, Asma’u nice Fatima wallahi ba mutuwa nayi ba, karya ake yi min wallahi ban mutu ba” kuka yaci karfinta, tana jin zafi a zuciyarta cewa yan uwant data gama cin burin zuwa ta gansu ta rungume su taji dadi sune suke gudunta sun dauka fatalwa ce, wai ashe duk tunanin da take cewa babanta yana nan yana zazzage Nigeria yana nemanta ashe ba haka bane ba shi ya dauka bata duniya, for five full years, hakan yana nufin har sun fara mantawa da ita kenan. Hakan yana nufin badan Mama ta taimaka mata ba, da sai dai ta karashe rayuwarta a rufe babu mai zuwa cetonta kamar yadda da take tsammanin babanta zai yi bincike ya gano inda take sannan ya taimaka mata.
Sai ta juyo ta rungume Maman Adam, “Mama dan Allah ki gaya musu, ki ce musu wallahi ba mutuwa nayi ba ina tare daku, ki gaya musu su bar guduna ni ba fatalwa ba ce ba” kafin Maman tayi magana Hajiya ta tashi ta rungume ta, “ba sai kin rantse ba Fatima, ba sai kin nemo ma yi miki shaida bani nasan kece, tunda aka ce min kin mutu jikina yake bani kina raye kuma zaki dawo wata rana,ni na san bagawarki suka binne ba”.
A lokacin suka jiyo maganar shamaki, “takawa sannu, zaki ɗaukawa sannu, sunkuye alher” Hakan yana nufin mai martaba sarki ne da kansa ya taho gurin, abinda baya taba yi, baya taba shigowa bangaren matansa sai dai in watace a cikin su bata da lafiya ko wata a cikin yayansa. Jin haka yasa ka Fatima ta saki Hajiya ta kuma fita a guje zuwa inda yake tahowa, ita dama can tun tana karama yar babanta ce, ma’ana tafi shakuwa da babanta akan kowa, yaga tahowar ta, yakuma gane ta, ba ko girgiza ba ballantana yaji tsoro sai ma farin ciki da ya cika zuciyar sa cewa labarin da aka kai masa gaskiya ne, Fatima bata mutu ba kuma ta dawo gida.
Tana zuwa ya shige jikin sa tana kuka, “wallahi ban mutu ba Takawa, ina imo, ina can an rufe ni an hana ni tahowa, ina can bani da lafiya Baba”. Bai amsa mata ba sai ya rungume ta yana shafa kanta, a ransa yana tasbihi ga ubangiji daya dawo masa da Fatima duk da cewa bai taba addu’a akan hakan ba, bai taba yi ba saboda bai san cewa hakan zai iya kasance wa ba, bai san cewa tana da rai ba.
Sai kuma ta cika shi da sauri ta dago kai tana kallonsa sa, zuciyarta a karye, yana yin fuskarta kadai ya isa ya saka mai karyayyiyar zuciya yayi kuka, tace “Baba ina Hussain? Ina Hussain dina? Baba dan Allah ka gaya min ba gaskiya ba ne ba abinda naji, dan Allah ka gaya min bai neme ni ba saboda shima ya dauka na mutu, ka gaya min cewa yana nan yana kukan rashina ba wai ni ce zanyi kukan rashin sa ba”.
Dauke kansa yayi gefe ya lasa hada ido da ita, hakan yana kara tabbatar mata da maganar da Adam ya gaya mata amma kullum take gayawa zuciyar ta cewaba haka bane ba, kullum take saka ran cewain ta dawo goda zata tarar cewa ba haka bane ba, amma expression din fuskar maimartaba sarki kadai ya saka ta fahimtar cewa yaudarar kanta take yi, Hussain ya mutu, shekaru biyar da suka wuce, ita da Hussain sai a Darussalam.
Sai ta sake shi sannan ta zame zuwa kan kafafuwan sa, idanuwan ta a kasa amma hawaye ya tsaya a cikin su, Kamar yadda duk tunani ya tsaya a zuciyarta fuskar Hussain kawai take gani.
Ta tuno da maganar sa
“wannan ciwon da yake damuna jarabawa ta ce, abinda zai same ni kuma jarabawar ki ne”
Ta girgiza kanta kamar ta girgiza lokacin daya gaya mata maganar “no, no, no, Hussain, babu abinda zai same ka, please babu abinda zai same ka, ba zan iya ba Hussain, ba zan iya rayuwa babu kai ba” Hajiya ta zo gurinta tana kuka ita ma, tana cewa “zaki iya Fatima, Allah ya san zaki iya shi yasa ya dora miki, sai ki karba kuma ki gode masa bisa ga sauran ni’imomin da yayi miki” ta dago tana kallon ta, her mind racing, sauran ni’imomin da Allah yayi mata? Hajiya tana nufin dan ta kenan? Danta da suka haifa ita da Hussain? Mai kama da Hussain?
Ta mike da sauri ta fara waige waige tana neman sa, tana neman yaro dan shekara biyar mai kama da Hussain ko da Hassan, yaron da tasan zata yi dedicating duk kan sauran rayuwarta a gun tabbatar da cewa ya samu kyakykyawar rayuwa ba tare da yayi kukan maraici ba, yaron da tasan zai goge mata dukkanin kewa da kadaicin Hussain.
“Ina yake?” Tace tana bin mutanen gurin da kallo, “Allah sarki, ya dauka bashi da uwa bashi da uba ko?” Ta share hawayen ta “it must have been so hard on him, it must have been so hard on all of you” amma sai ta ga duk suna binta da kallon rashin fahimta, wa take nema? Wa take nufin ya tashi ba uwa ba uba?
Ganin kallon da suke yi mata ya sake tsinka zuciyarta, God please no, not her son please. Bata son tayi musu tambayar dan bata shirya jin amsar da zasu bata ba, zuciyarta ba zata iya dauka ba. Sai ta tambayi kanta “me ya saka ta dawo gida, me nene yayi mata saura a gida? Ina ma dai da gaske ne abinda suke tunani, ina ma dai ta mutu a ranar nan kamar yadda suka yi zargi.
Duk da haka tana so taji me ya faru da dan nata, ta kama hannun umma “ina Da na?” Ta tambaya da wata irin murya data huda zuciyoyin duk wadanda suke gurin “ko yana gurin Hassan ne? Ku kawo min mota in tafi Kaduna in ganshi, ku gaya min inda yake don Allah”.
Ummah tace “Fatima ke zamu tambaya ai inda yake, mu gawar da aka bamu muka binne da ciki a jikinta dan haka bamu nemi inda abinda yake cikin ki yake ba, mu duk mun dauka tare muka binne ku. Kin haihu ne dama kafin kuyi accident din? A ina kika haihu? A ina kika bar babyn?” Fatima ta dafe kanta da hannayenta biyu tana jin yadda kan ta yake juyawa, “innalillahi wa inna ilaihir rajiun” ta ringa fada cikin muryar ban tausayi. Duk iyayenta suka yi kanta kowa yana kokarin rarrashin ta