TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Maman Adam ce tazo itama tace “ku barta dan Allah ta huta, kar ku gaya mata abinda zai bata ranta Please” duk suka juyo suna kallonta, suna lissafin inda zasuyi placing dinta. An enamy or a friend? Amma sai aka dauki shawarar ta aka shigar da Fatima cikin gida, nan da nan kuma aka guda da shewa da murnar dawowar Fatima gida, labari ya bazu ko’ina cewa gawar da aka binne ba ta Fatima bace ba. Sai dai kowa aka gayawa labarin sai ya tambaya “how comes?” Lallai akwai zare cikin nadi.

Duk wannan murnar da ake yi Fatima bata tare da murna, bata kuka kuma bata dariya, tana dai zaune kawai tana kuma yin duk abinda aka umarce ta tayi batare da musu ko doki ba.

Kafin wani lokaci maganar ta zagaye ko ina, duk yan uwan Fatima sun samu labari kuma da yawadaga cikin su wadanda basa gida sun kamo hanyar gida, hatta wadanda basa kasar sun nemi next flight to Nigeria sun yi booking, Asma’u kuma da take gida already ta dauki hotunan Fatima ta tura wa yan uwadan su tabbatar da gaskiyar magana.

An sauki Adam a gurin saukar baki maza a waje, an kuma sauki Mama a kebantaccen guri a cikin gida har sai anji labari daga bakin Fatima tukunna kafin ayi tunanin matsayin ta a cikin maganar, sai dai ba Fatima ba kadai duk wanda aka gaya wa dawowar Fatima sai ya tambaya “har babyn suka dawo tare?” Amsar, ita take saka su cikin jimami da kuma tunanin ya akayi aka kwana a ragaya?

Bayan anyi sallar magrib ne maimaita sarki ya kira iyalinsa gabaki daya, immediate family dinsa, wadanda da yawa daga cikin su sun iso gidan kuma duk suna son suji inda maganar ta kwana.

Bayan sun zauna ne, fuskokin su dauke da mixed feelings na farin ciki da kuma jimami, Fatima a kusa da baban ta, fuskarta unreadable, sai aka gabatar da addu’a tare da godiya ga ubangiji akan wannan abin farin cikin daya same su tare da kuma neman jagorar sa akan duk hukuncin da zasu yanke.

Tambayar da tafi damun kowa a gurin ita Takawa ya fara yiwa Fatima. “Fatima Zahra, ina kike tsahon shekarun nan kuma mai ya hanaki dawowa gida? Ko kuma neman munki sanar mana a inda kike mu muje mu taho dake?” Ta dago kanta tana kallon sa, sannan cikin karamar murya tace “ina imo, bani da lafiya, kuma an rufe ni ba’a barina na fito ko da kofar gida, ban san yadda zanyi in neme ku ba” suka fara kallon juna cikin mamaki sannan Hajiya Ummah tace “imo? Ya akayi kika je imo?” Duk suka dawo da hankalin su kanta suna jiran amsa, amma ga mamakin su sai suka ga ta juya hannayenta, alamun bata sani ba.

Umar ya gyara zamansa yace “Fatima abinda ke cikin ki a lokacin fa? Kin san yadda akayi kika rabu dashi?” Idonta ya ciko da kwalla, ta dora hannunta akan cikinta sannan tace “ban sani ba Yaya, ni bansan komai ba, ni dai na ganni acan baninda lafiya, Adam ya gaya min accident mukayi ni bansan ma munyi accident din ba, ya gaya min tsinta ta yayi a daji sai kuma babansa ya hada mu gaba daya ya tafi damu can, ya gaya min shima bai ganni da ciki ba, yace sanda ya ganni babu ciki a jikina amma da alamar na haihu ne a lokacin, ni na dauka a inda muka yi hatsarin na haihu, na dauka an kawo muku babyn kuma kuna ta nemana, na dauka….” Muryarta ta makale saboda kukan da ya ci karfin ta, Hajiya, Ummah tare da yan uwan Fatima mata suna taya ta kukan.

Mazan kuma suna ta kokarin amfani da kwakwalwar su wajen ganin sun fahimci menene ya faru. Abubakar yace “tunda ga Fatima anan a gaban mu, wacece kenan muka binne da tsohon ciki? Menene dalilin da yasa aka faya mana cewa Fatimah ce bayan ba ita bace ba?” Umar ya juya gurin Fatima yana tausayin yadda take kuka na rashin sanin inda danta yake ga kuma mikin mutuwar mijinta, yace “Fatima Zahra, ki daure, ki tuna, ranar da kuka yi accident din menene ya faru? Dake da waye a cikin motar? Shin kunyi accident din ma ko ba kuyi ba? Ko wani cover up aka shirya dan a salwantar da ke da kuma abinda yake cikin ki? Ki tuna Fatima, ki bamu labarin menene ya faru, wannan ne zai taimaka mana gurin gano inda yaron yake”.

Ta goge hawayen idanunta, duk da cewa tana goge su wadansu suka yi replacing dinsu. Tun sanda ta dawo hayyacin ta, tun sanda ta fara tuna ko wacece ita tare da taimakon Adam, babban abinda take kokarin tunawa shine yadda akayi ta haihu, saboda tana so ta tuno koda fuskar danta ne, ta tuna feeling din nakuda da fitowarsa daga jikinta, ta tuna muryar sa sanda yayi kukan sa na farko amma ta kasa tunawa. Abu na biyu da take kokarin tunawa shine accident din da Adam yace sunyi, menene ya faru, amma abinda kawai take tunawa shine Hussain ya mutu, bata san ya akayi ta sani ba amma ta san ta san Hussain ya mutu kuna shine last abinda ta sani.

“Kiyi kokari ki tuna Fatima” Asma’u ta fada tana shafa kafadar ta, ki tuna a ranar tunda safe me kikayi har zuwa tafiyar ku Abuja, ke da waye a cikin motar? Me ya faru a cikin motar” tayi shiru tana kallon Asma’u, daga alama tunani take yi, sai ta runtse idanunwanta ta yare da dafe kanta da hannunta, ta jima a haka sannan tace “Hussain…….. Hussain ya tafi Abuja shi da Hassan da Adam a mota, ni kuma bana son ya tafi, hankali na ya tashi da tafiyar sa. Bayan na lissafa lokacin daya kamata su sauka sai na kira wayarsa amma baya dauka, nayi ta kira amma baya dauka dai hankali na ya tashi, na kira driver nace yazo ya kaini Abuja gurin Hussain, sai muka tafi tare da ……..tare da ……..matar Hassan, Ruqayyah, tace ita ma tana son taje taga Hassan. Sai muka tafi, mun kusa shiga Abuja sai Hassan ya kira ta yace mata mu koma gasu nan sun gama abinda suke yi zasu taho, muna juya mota sai aka ce min Hussain ya mutu ……” Sai ta rufe fuskarta tana kuka “shikenan abinda na sani”

Umar yace “waye ya gaya miki Hussain ya mutu?” Ta bude idonta da suka juye saboda kuka tace “ban sani ba Yaya Umar, ba zan iya tunawa ba” ya matso kusa da ita “okay, just close your eyes ki tuna sanda kuke zaune a motar, a ina kika zauna?” Ta rufe idonta a tana tunani sannan tace “a baya nake, a side din driver”

Suka kalli juna suna tunawa cewa gawar da aka samu a gaban mota take, yace “good. Ruqayyah fa? A ina take?” Ta kara tunani Tace “a baya itama, tare muke da ita a baya” yace “waye a gaba, akwai mutum a gaba” tayi shiru, her eyes squeezing, tana jinta kamar a cikin motar take, tana jin tension din son taji halin da Hussain yake ciki, tana tuno maganganun su da Ruqayyah da kuma maganar da Ruqayyah suka yi da Hassan a waya da kuma umarnin da Hassan ya bayar, she remembered the driver, da yadda yake kokarin juya motar, and then…..then she remembered her face sanda ta juyo daga seat din gaba tana kallon su da budaddun idanu, she remembered her voice, kamar yanzu take mata maganar tace “Ruqayyah? Ba Hussain dinku ne Hussain Aminu Abdullahi ba? Ya mutu! Yanzu ake fada a twitter wai ya mutu a wani asibiti a abuja!” Fatima ta tuna yadda dan cikinta ya harba da karfi a lokacin. Ta dafe cikin ta tana tsananin missing dinsa.

Ta bude idonta tana kallon Umar, ta gyada kai da sauri tace “na tuna ta, na tuna kamannin ta da komai, kawar Ruqayyah ce tare suka shigo gida sanda zan fita, ita ce a gaba, ita ce ta gaya min Hussain ya mutu” Abubakar yace “zaki iya tunawa ko da akwai ciki a jikin ta?” Ta gyada kanta ba tare da tayi wani tunani ba tace “tsoho ma kuwa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button