TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

. * *

A yau, bayan shekara hudu da bude estate dinsa na farko, Hassan ya samu nasarar bude na biyu wanda kamar na farkon ya saka masa suna “Hussain Aminu Abdullahi memorial estate phase 2”. Kamar na farkon, shima wannan block shida ne sai dai wannan hawa uku ne ba biyu ba, dan haka wannan gidaje goma sha takwas ne a ciki ba sha biyu ba.

Kamar wancan karon, yan uwa da abokan arziki sun taru sosai dan taya shi murnar wannan abin farin cikin. Aunty da family dinta, yaya da jikoki, dan yanzu Hassana da na uku take goyo, Safiyya daya, Khadijah tsohon ciki, Nafisa karami, Sumayya da one year old Abdullahin ta sai Zulaihat da take ta cin yammatancin ta har yanzu. Hassana ta kira Zulaihat “zo ki dauki Ilham ki tafi da ita gurin samarin, in sun baki kin kasa karba ita sai ta karbo ta kawo min mu raba” ta fada tana miƙa mata ikram da take ta tsalala kuka. Zulaihat ta bata rai “kai yaya Hassana! Ni ya zanyi da ita?” Sumayya ta miko mata abdullahi “hada da Abdul, sai ya taya ki renon ta” Abdul ya mika wa Zulaihat hannu yana murna za’a dauke shi. Zulaihat ta bata rai tana dungure masa kai sannan tace “Aunty kin gan su ko?” Aunty tace “ina ruwan Amina? In da kinyi aure ai da ba zasu ke hada ki da rainon yayan su ba. Ki dauki yaran, maybe in samarin ki suka ganki dasu suka fahimci cewa kin iya raino zasu fahimci cewa kin isa aure”. Duk suka kwashe da dariya banda Zulaihat, ita ta gaji da wannan sa idon da suke mata suna cewa taki aure, ga Aunty tana tare mata amma tun da taga Sumayya ta haihu sai ta fara matsanta mata itama akan ta fitar da miji ayi mata aure.

Ta tura baki, “babu dan da zan dauka, ai duk kuna da yan aiki ku basu yaran mana su rike muku” ta tashi tana kokarin barin gurin wayar Aunty tayi kara. Ta fito da ita daga jaka tana duba sunan sai ta dafe kanta “innalillahi” Khadijah tace “waye?” Aunty tace “Hajiya Umma ce, wallahi shaf na manta ban aika musu maganar taron nan ba, yanzu haka labari suka ji zata kira tace min ban kyauta ba” Hassana tace “kash, walllahi an manta kuwa, amma kinga wancan ai an aika musu har suka zo ma” Aunty ta dauki wayar da kiran har ya riga ya katse tace “bara in kira in basu hakuri, ban kyauta ba wallahi”

Kafin ta kira sai wani kiran ya sake shigowa, ta tashi tsaye ta dauka yana matsawa inda babu hayaniya ta fara wayarta, bata jima da tashi ba sai sai Hassan yazo, yan samarin sa guda uku suna binsa kamar jela, ya saka hannu ya dauki Abdullahi da tun daya hango shi ya fara tsalle a cinyar maman sa, ya daga shi yana kissing forehead dinsa sannan yace “shine kika zo kika yi zamanki kika barni da mutane ko?” Ta mike tana murmushi tare da pretending hamma, ya harare ta, tayi murmushi “ba laifi na bane Habibi, laifin wannan katon yaron na hannunka ne” sai shima ya ja kujera ya zauna “nima zama zanyi, duk wanda yazo yanzu ke zaki zagaya dashi” ya zauna Sumayya ta fara zuba masa drink sannan ta zubawa boys din suma. Suna ta hada baki gurin bata labarin abubuwan da suka faru a gurin.

Sun jima a haka sannan Aunty ta dawo daga wayar da taje yi. Yanayin fuskarta ya saka kusan gaba ki dayansu suka mike tsaye, Nafisa tace “Aunty mutuwa akayi? Waye ya mutu kuma?” Aunty ta bisu da kallo daya bayan daya sannan tace “ba mutuwa akayi ba, the most strangest thing has happened, Fatima ta dawo gida, bata mutu ba”
Wannan littafin na siyarwa ne idan kika ganshi a wani guri na sata ne, in kina son ki sayi halaliyar ki ki yi min magana ta wannan number din through WhatsApp 08067081020

Ina masu bukatar hadadu kuma ingantatun turarukan wuta da khumra masu dadin kamshi kuma a farashi me sauki to ga dama tazo muku Awwaba scent nada turarukan wuta humra burners kasko shisa coal dorot stool dilka body milk dadai sauransu masu bukatar na iya nemansu a whats app ko kuma kira ta wannan lambar 08034236800
bugu da kari duk wanda ya sayi humra ko turaren wuta a cikin wannan watan akwai kyautar dilka me kyau tafiyaya daga kasar chad wadda zata gyara jiki tay expoliating skin acikin minti 20 kawai ku garzayo dan kwasar garabasa
Adress kundila zoo road kano muna tura sako ko ina da iznin Allah

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148

Leave a Reply

Back to top button