TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta yi saurin shigewa cikin wani kango yadda ba zasu ganta ba sai dai suji sautin muryarta. Tana jin sun kusa zuwa tayi shiru, taji sunzo gidan karshe suna buga kofar da karfi, mai bindigar ya ture dayan ya saka bindiga ya harbi lock din gidan, karar bindigar yana amsa amo a cikin shirun daren.

Tun harbin farko inna ade ta bude idonta, ita dama bata fiya yin nauyin bacci ba. Ta jima kwance tana tunanin anya kuwa da gaske karar bindiga taji? A lokacin ta sake jin ta biyun. Ta mike zaune tana salati, abinda da uwa, yayan ta ne suka fara fado mata a rai, matan suna cikin gida kuma dakin da suke ciki na kasa ne, an ce kuma bullet baya iya wuce katangar kasa, samarin ne take jiwa tsoro, sune suke kwana a shagon gidan makotansu tate da samari da yawa kuma ginin siminti ne kar fa bullet ya same su.

Daga nan ne kuma taji ana bubbuga kofar gidan daya ke kallon nasu. “Open this door ko mu fasa ta” taji an fada da murya mai karfi. Ta fara jijjiga Baban biyu tana salati “baban biyu ka tashi barayi sun shigo unguwar nan, gasu can suna buga gidan Maman Minal” ya mike zaune yana salati shima yana mitstsika idonsa. A lokacin ne suka ji karar dirar mutum daga katanga. Kuma kamar katangar toilet dinsu ta baya, ko dai an hauro katangar an shigo gidan ko kuma an haura an fita. Inna ade ta mike “yan biyu na!” Ta fada cikin tashin hankali “baban biyu an shigo mana gida kar a shiga dakin yaran nan ayi musu wani abu na shiga uku” ta fada tana laluben hanyar fita daga dakin. Dama fitilar su daya a gidan kuma yaran suke bawa su su kwanta a haka.

Baban biyu ya rike ta “tsaya anan kar ki fita, bara ni inje gurinsu” ba tare daya jira abinda xata ce ba ya wuce ta ya bude kofar dakin ya fita. A bakin kofar dakin yaga Sumayya a tsaye, idanuwanta a waje, da touchlight a hannunta amma kuma a kashe. Cikin rawar murya da karkarwar jiki tace cikin rada “Baba naji an hauro gidan nan ta bandaki kuma Ruqayyah tana bandakin” bai jira karashen maganar tata ba ya karbi fitilar hannunta ya tafi bandakin cikin sauri. Inna ade itama da kunnuwanta suka jiyo mata kalaman Sumayya ta fito da sauri daga dakin tabi bayan mijinta zuciyarta kamar zata bar kirjinta. Sumayya, ganin an barta ita kadai yasa itama ta bisu da sassarfa.

Yana shiga toilet din ya kunna fitilar hannunsa, haske ya karade bandakin tare da bayyanar masa da jinin da yake malale a gurin, yayi kokarin kare Inna ade kar ta gani, a lokacin ne kuma ya ga Hassan a kwance a kasan katanga yana numfashi da kyar. Wannan ya tabbatar masa da cewa jinin bana Ruqayyah bane ba na wannan mutumin ne. Amma ina Ruqayyah?

A lokacin ne suka jiyo ihu

“wayyo Allah jama’a ku taimaka min ga wani ya shigo min daki. Wayyo Allah gardi a dakina. Jama’a ku taimaka min jini ne a jikinsa”!

Ko daga bacci aka tashe su sun san muryar Ruqayyah ce. Inna Ade tace “Ruqayyah! Baban biyu wannan ai muryar Ruqayyah ce. Daga ina take wannan ihu? Yaushe ta fita daga gidan nan?” Baban biyu ya shige ciki yana tallafo fuskar Hassan, kallo daya yayi masa ya gane shi, ya kuma gane dankwalin Ruqayyah da yake daure a wuyansa. A take ya fara guessing abinda yake faruwa. Amma kuma hankalin sa ya tashi saboda fahimtar hadarin da Ruqayyah take ciki.

Hassan ya bude ido a hankali yana kallon baban biyu, cikin magagin ciwo yace “Hussain? Ku kaini gurin Hussain” shima kuma yaji muryar da take ihun daya cika gabaki dayan unguwar. Yaji kamar yasan muryar, kamar muryar wacce tace zata taimaka masa, wacce ta haura katanga saboda shi, saboda Allah tace zata taimaka masa ba dan komai ba. Ya fahimci mai take cewa a ihun nata kuma ya gane mai take yi, tana kiran mutanen da suke nemansa ne away from him and toward her, tana jawo danger away from him and unto herself. So selfless, so brave.

A lokacin suka ji mutanen da suka shiga makota suna nemansa sun fito da gudu sun tafi inda take ihun. Hassan ya runtse idonsa, Inna Ade ta saka kuka “wayyo Allah na, wayyo ‘yata”. Sai suka ji ta daina ihun, sannan kuma suka ji karar harbin bindiga, karar data cika unguwar baki daya.

Sumayya ta kwalla kara “Hassana!!!” Hassan ya maimaita a hankali “Hassana!” Yaji sunan ya zarce zuciyarsa ya zauna a gurin da wani abu bai taba zama ba. Sunan mahaifiyarsa ne, sannan kuma female version of his own name. Ya tuno fuskarta sanda ta durkusa tama daure masa ciwonsa. So Young, so beautiful, so brave, so selfless. Sai yaji a ransa cewa zai iya bayar da tasa rayuwar saboda ita, me yasa ya gudu har ya shigo gidan nan ya saka yarinyar nan in danger? Me yasa bai tsaya kawai mutanen can sun harbe shi kowa ya huta ba? Ya fara addu’a a hankali “ya Allah indai wani zai mutu Allah ka dauki raina ka bar yarinyar nan. Allah ya bani dama da kuma ikon kwatanta sakawa yarinyar nan da kwatankwacin abinda tayi gare ni. Allah ka ……….”

A lokacin suka ji jiniyar police ta cika unguwar, sai kuma harbe harben bindiga ya biyo baya. Sannan kuma shiru. Shiru except for kukan Sumayya da Inna. Sai kuma kamar daga sama suka ganta ta durgo daga katanga. Duk suka juya suna kallonta ita ma tana kallonsu. “Hassana?” Baban ya fada. “Hassana” Hassan ya maimaita yana mika mata hannunsa kamar mai kiranta zuwa gare shi. Ta taho straight ta durkusa a gabansa tace “it is okay, yan sanda sun kama su. It is over”


Hassan ya sauke idonsa daga kallon agogon daya kafawa ido kusan mintina ashirin da suka wuce, ya gaji da kallon kofar ya koma kallon agogo kuma zuciyarsa tana bugawa tare da kowanne bugu na hannun agogon. It is already after 3am. Tun 1am yake zaune a guri daya yana jiran shigowar Hassan kamar yadda kidnappers din suka yi mishi alkawari “zai zo gida da ƙafafuwan sa” they said, but he was a fool to believe them. Ta ya akayi ma ya yarda da maganar barayi? Barayin ma na mutane.

Ya cire hular sa ya ajiye a gefe, duk ta dame shi ciwo take sakawa kansa yana yi. Ya cire agogon hannun sa shima yayi jifa dashi, ji yake komai ya fita daga ransa dan uwansa yake so ya gani, gabansa faduwa yake yi, ji yake kamar ya dora hannu aka yayi ta rusa kuka amma kuma sai ya tuna da cewa shi fa Hussain ne. Jarumi ne shi.

Sanyi yaji ya fara ratsa shi, irin sanyin da yake kadawa idan assuba ta gabato. Ya lumshe idonsa sai yaji wani ruwa ya zubo daga idon nasa zuwa kan kuncinsa. Yayi sauri ya goge. Ba zai iya tuna ranar da ya taba yin kuka ba. But he can’t take it anymore. He just can’t allow himself to think, baya son yayi imagining wani abu ya faru da danuwansa, yayi komai da suke bukata ya cire police ya kai musu kudi shi kadai yayi isolating kansa duk a banza? For the first time in his life da yayi abu with care kuma shine zaiyi failing?

Wayarsa tayi kara a gefensa, ya juya slowly yana kallon screen din “commissioner of police” ya gani. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ya fada ya sake fada, sai da kiran ya katse wani ya sake shigowa sannan ya dauka. Bai iya yin magana ba. Commissioner yace “yalllabai albishir nazo dashi. Mun samo Hassan” ya fada muryar sa cike da farin ciki.

Wani sanyi ne ya taso daga kafafuwan sa ya dire har kansa. Sannan kuma wani dumi mai dadi ya ratsa zuciyarsa da kwakwalwar sa ya fara saisaita masa tunanin sa. Ya mike tsaye “a ina? Yana ina? Lafiyar sa kalau? Is he okay?” Ya jera tambayoyin da suka saka commissioner din yin murmushi sannan yace cikin kwantacciyar murya “dan uwanka yana raye, kuma alhamdulillah mun samu nasarar kama barayinsa, sannan mun karbo maka kudinka daga hannun su” cikin zakuwa Hussain yace “bar maganar barayi da kudi, ina Hassan yake?” Commissioner yace “muna asibiti yanzu tare dashi. An shiga dashi theater room” Hussain yace “asibiti kuma, wani abin ya same shi ne?” Commissioner yace “a’a, kawai dai ya danji ciwo ne kadan, but it is not that serious. Na kira kane saboda nasan zaka so a fito dashi kana gurin, shima kuma nasan zai so yana fitowa ya ganka” Hussain yayi murmushi, rabon da yayi murmushi tun sayi daya daya wuce “na gane. Nagode. Gani nan zuwa”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button