TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Ya ajiye wayar yayi kamar zai je dakinsa sai kuma ya fasa ya koma dakin Hassan ya dauko key din mota ya fito ya dauki hularsa ya fita da sauri, har yaje gaban mota kuma sai ya koma cikin gidan da sauri ya hau saman Aunty yana bin kofofin kannensa yana knocking cikin sigar kida, kudan duk a tare suka fito tunda ba wani dogon bacci suke samun yi ba. Fuskarsa kawai suka kalla suka rude da ihun murna, gabaki daya suka rungume shi shima ya bisu daya bayan daya yana rungume wa.

Aunty ta fito tana kallonsu, sannan ta daga hannunta sama tace “alhamdulillah. Allah mun gode maka”.

Sanda aka fito da Hassan, duk family dinsa suna bakin kofa suna jira amma shi bacci yake saboda allurar baccin da akayi masa. Wuyansa a nade da bandage, kafarsa ma haka. Aunty ta fara sharar hawaye, Hussain yana kallon doctor yace “akace min minor ne ciwon, menene haka?” Doctor yayi murmushi yace “ba wani abu yallabai, bawai ciwon bane yasa kuka ganshi haka wahalarda yasa ne, daya kwana biyu zai warware, harbinsa akayi a wuya amma bullet din bai shiga ba gogar gurin kawai yayi. Kafarsa kuma targade ne sai kuma ciwo da yaji a kafar itama. Duk it has all been taken care of”.

Da kyar Hussain ya iya sakin hannun Hassan yaje yayi sallah, yana dawowa ya koma ya zauna ya cigaba da rikon hannun. Sauran yanuwan a zagaye dasu. A haka Hassan ya farka ya gansu.

Daya bayan daya yake binsu da kallo, duk suma suna kallon sa da murmushi a fuskokin su har ya iso kan Hussain. Ya lira da yadda yayi baki ya rame, ya danyi masa murmushi yace “hello bro” Hussain yace “hi bro. Welcome back” Hassan yace “na dawo gida, amma kafin in dawo na samo matar aure a inda naje” duk suka bude ido suna kallonsa cikin mamaki. Hussain yace “matar aure kuma?” Safiyyah tace “tare aka kama ku?” Khadijah tace “a ina take?” Nafisa tace “ya kamannin ta suke” Zulaihat tace “yaya sunanta?”

Yayi murmushi yana kokarin mike wa zaune yace “no ba tare aka kama mu ba, a can dai unguwar take, she is the most beautiful, brave, and selfless person I have ever met” ya juya yana kallon Hussain yace “sunanta Hassana and she saved my life”.

Anan muka kawo karshen free Episodes na littafin tagwaye. Anan ne kuma muka fara labarin. Wannan tafiyar ba irin sauran ba ce ba, wannan tafiyar da zafi muka debo ta.

Ga dai Hassan da hassanar sa (Ruqayyah, Rukee) ga kuma Hussain da gimbiyar sa, sannan ga Sumayya a gefe.
Shin yaya wannan tafiyar zata kasance?
Shin cikin wadannan su wanene iyayen Amir?
Shin menene ya faru har Amir ya samu kansa a yashe a kofar gidan marayu?
Wacece matar data kira Amir zata bashi labarin iyayensa kuma menene alakar sa da ita?
Yaya zata kare tsakanin su?

Zaku samu amsar wadannan tambayoyin in kuka turo kudinku ₦300 ta account
GT Bank
Account Name : Nafisa Usman Tafida
Account Number : 0139433741

Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin
08067081020

Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin
08067081020.

Nagode, sai na jiku.
Saura Episodes biyu mu gama free ????Episode Eleven : The two sides of a coin

Hussain ya kama Hassan yana mayar da shi kwance, yana cewa “wannan Hassana ba dan sunan ta ba da na fara kishi da ita tun yanzu” Hassan ya runtse idanunsa cikin nuna jin zafin ciwon wuyansa yace “ba zata kula ka ba, komai neman maganar ka ba zata kula ka ba. Ita kamilalliyar yarinya ce” Hassan ya nade hannayensa a kirjinsa yana bata rai yace “me kake nufi da kamilalliyar yarinya ce? To waye kuma ba kamilallen ba?” Aunty ta matso tana dariya tace “zaku fara ko? Hussain sai kace ba kai bane mai kuka kana neman Hassan ba shine daga dawowarsa zaku fara musu. Ni na dauka in ya dawo ba zaku kara rigima ba” duk suka yi murmushi Hussain yace “ban fa yi kuka ba Aunty, kar ki sa ya raina ni mana. Kawai dai ina mamakin yadda mutum zai shiga irin halin da ya shiga sannan the very first thing da zai fada bayan ya dawo hayyacin sa shine wai ya samu mata” ya karasa maganar yana rike baki “mata fa? Hassan din? Ni na dauka duk macen da Hassan zai kira da mata sai tayi passing through different stages na gwaji. Ko guda daya ta fadi kuwa to an cire ta a list amma wannan cikin dare daya har tayi passing? Ni nafi tunanin zafin ciwo ne ya saka shi wannan maganar” Hassan yana daga kwance ya harare shi yace “ko kakan zafin ciwo ba. Nasan abinda nake yi kuma nasan duk mutumin da zai saka rayuwarsa on the line to save someone da bai taba gani ba a rayuwarsa to kuwa tabbas dole a kira shi dukkanin suna na gari da yake available. Like I said, she saved me. Nasan Allah ne mai raya wa kuma na yarda Allah ne yasa ka zan ga yau, zan ganku, amma through Hassana taimakon Allah yazo min. Don’t you think this means something?”

Aunty tayi replacing kujerar da Hussain ya tashi daga kai tace “ban san yarinyar da kake magana akanta ba, amma na san ka Hassan, nasan kuma duk abinda ka zaba kuma har ka yaba dashi to kuwa abu ne mai kyau. Dan haka bani da kokwanto cewa duk sanda naga yarinyar nan nima zan yaba da ita”

Hussain ya kalli agogon sa yace “don’t stress yourself da tunani, rest, ka koma baccinka. Ni zan je gurin police suna ta jirana tun dazu suna so suyi briefing dina akan case din. In ma dawo kuma zan samu doctor muyi maganar fitar da kai waje dan kafi samun cikakkiyar kulawa” daga haka ya bar dakin. Zuciyarsa tana cike da farin cikin dawowar danuwansa amma kuma bai san dalilin da yasa yaji hankalin sa bai kwant da maganar da dan’uwan nasa ya dawo da ita ba.

A gurin police ne ya kuma samu wani shock din, shock din ganin Salisu a zaune a kasa duk rigarsa jini, kafadarsa daya a nannade da bandage. Yana ganinsa yace “Salisu? Me kake yi anan? Ciwon menene kaji haka a hannunka? Salisu ya sunkuyar da kansa kasaya kasa dago kai su haɗa ido. Hussain ya kalli dan sandan da yake wajen yace “me yake yi anan gurin ga kuma ciwo nan a jikinsa? accident yayi? A kaishi asibiti mana” police din ya saka kafa ya daki Salisu a bayansa yace “juya ka bashi labarin a inda kaji ciwon jikinka?” Salisu ya sake dunkule wa guri daya sam ya kasa dago kansa. Hussain ya rike dan sandan da sauri “ya zaka dake shi, ga ciwo a jikinsa ga kuma duka? Wanne irin police ne kai?” A lokacin commissioner ya fito, suka zazzauna shi da Hussain suka gaisa ya kuma taya Hussain murnar warwarewar lamura sannan yace “ka san wancan yaron?” Ya fada yana nuna Salisu, Hussain ya hadiye abinda yaki tafiya a makwogwaron sa saboda fara fahimtar inda maganar ta dosada yayi. Yace “yaron mune, a gidan mu aka haife shi a gidan mu ya taso, a hannun mu yayi karatunsa, a yanzu haka mahaifiyar sa tana cikin gidan mu tana shirya mana abinda zamu bukata in muka koma gida” commissioner ya girgiza kansa yace “am sorry to inform you cewa shine mastermind na wannan kidnapping din” Hussain ya mike da sauri kamar wanda aka yi wa allura, Salisu ya fara kuka yana rarrafe ya rike kafar Hussain “oga Hussain dan Allah kayi min rai kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne oga Hussain, nayi nadama ba zan sake ba. Ba hali na bane ba ka sani sharrin shaidan ne” Hussain ya saka kafa ya doke shi tare da ja da baya kamar wanda yake gudun ya sake taba shi yace “sharrin shaidan? Salisu? Wannan shine sakayyar soyayyar da muke yi maka ni da danuwana? Wannan itace muguntar da zaka saka alkhairin mu da shi? Dama yanzu duniya har ta kai wannan lalacewar Salisu? Dama yanzu har dan Adam bai mayar da saka alkhairi da mugunta komai ba a duniya? Dama yanzu duniya ta zama babu wanda zaka yarda dashi komai kuwa kyautatawar ka gare shi? Shikenan komai dan adam ya aikata sai ya kira shi da sharrin shaidan. To auzubillahi minash shaidanir rajim. A yanzu mutane sune shaidanun kansu basa bukatar taimakon wani shaidan wajen aikata ta’asa” commissioner ya jashi ya zaunar dashi a kujera yana bashi hakuri. Hussain ya sake cewa “Hassan fa, rayuwar Hassan yayi wasada ita, har harbin Hassan fa akayi ba dan yana da sauran kwana ba da yanzu mun dawo daga sutturar sa” Salisu yace “wallahi oga Hussain bansan zasu cutar dashi ba. Alkawari suka yi min cewaba zasu cutar dashi ba. Nayi kokarin hana su cutar dashi shine suka harbe ni su suka yi min wannan harbin sannan suka bishi” commissioner yace “kadan ma kenan, dama ai karshen irinku kenan. Wadannan mutanen sun saba kashe mutane akan kudin da bai kai wannan yawa ba ma. Ko ba dan ka shiga tsakaninsu da Hassan ba dama kashe ka zasuyi su raba kuɗin a tsakanin su. Kai da tunani kake xasu baka? Kuma su barka da raj ayi tracing dinka ka tona musu asiri? Ai anyi irinka da yawa kuma basu kai labari ba” Hussain ya mike yana cewa “babu hannuna a cikin case dinka Salisu, ban sanka ba daga yau, danuwana ma bai san ka ba. Ko an sallame ka kar kabi koda hanyar gidan mu ce. Babu mu babu kai har abada” Salisu ya fara kuka wiwi yana bada hakuri, commissioner yace “ballantana ma ba za’a sake shi din ba, za’a hada shi da sauran a tura su court a yanke musu hukunci dai dai da laifin su”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button