TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Adam yace da Sumayya “sister dinki drama queen ce” ta gyada kai tace “sosai. But she is not as bad as she always acts” yace “Allah yasa, dan nasan ke kullum tare mata zaki ke yi, kullum kina side dinta ko?” Ta sake gyada kai tace “yes, bayan Inna da Baba bani da wanda ya kaita. Komai zafinta dole ita din tawa ce, she is a side of me that I can never get rid of. In babu ita to babu ni kuma ba zan………” Ya daga mata hannu “bla bla bla. Naji, amma nasan kinsan cewa bata da kirki, wannan side of her din kinsan dashi fiye da kowa” ta fito daga mitar tana kara mika masa kuɗin hannunta “ga kudin ka Adam. Mun gode” ya jefa mata murmushi “ki siya wa sister dinki awara, tunda ta riga ta gama debe wa abincin gidan ku albarka ko zata cinye ba zata ko shi ba” ta rufe masa kofar sannan ta jefa masa kuɗin ta window ta juya tabi bayan Ruqayyah ba tare data kuma cewa komai ba. Ta sani, tabbas tasan Ruqayyah bata da kirki amma kuma it hurts her in taji wani ya fada, kullum tana wa Ruqayyah addu’a, kuma bata taba barin tayi wani abu marar kyau ba tare data yi kokarin gyara mata ba. Kuma sosai tana ganin gyaran, gashi nan ta fara chanzawa, gashi nan ranar nan har ta kusa rasa rayuwarta saboda taimakon wani Allah.
Ta tarar da Ruqayyah tana kokarin shan kwana, har yanzu mita take yi amma kuma daga dukkan alamu ba wai mitar mai taxi take yi ba kuma, mitar wani abun ne na daban.
“Mutane yanzu basu san a kyautata musu ba, shi yasa taimako yake da wahala, in ka taimaka ma babu abinda zaka samu” Sumayya ta kalle ta tana girgiza kant cikin takaici tace “shi taimako in dai kayi shi dan Allah ai baka bukatar komai daga gurin wanda ka taimaka wa” Ruqayyah tace “ko godiya? At least dai ai yazo yace min thank you for saving my life ko?” Sumayya tace “Rukee kenan. Kina kallon dai yadda aka fitar dashi daga gidan mu cikin jini, na tabbatar asibiti za’a wuce dashi kuma na tabbatar har yanzu yana asibitin, bai kamata ace har kin fara mita ba, kuma ai yayi miki godiya tun kafin ya bar gidan mu” Ruqayyah tace “wacce godiya yayi min? Ni me yace min ma in banda kira kamar tsohon makaho, ‘Hassana” ta fada cikin kwaikwayon muryar Hassan, Sumayya tayi dariya ita kuma tayi tsaki, “bai san yadda na tsani a ce min Hassana ba, Baba ne kawai yake fada shima kuma dan babu yadda zanyi dashi ne”.
A lokacin suka sha kwanar gidan nasu, abinda suka gani a kofar gidan ya saka su taka burki cikin mamaki, suka rike hannun juna, Sumayya ta rada wa Ruqayyah “ga mutumin naki nan yazo godiyar” Ruqayyah tace “ni Companyn sa nake so ya bani daya”.
Manyan motoci ne guda biyu a kofar gidan, irin motocin da ba a kan kowanne titi su Ruqayyah suke ganin irin su ba. Ga kuma wadansu bakaken mutane masu bakaken kaya da bakaken tabarau a tsaye a gaban motocin, twins din suka rakube suka wuce su suka shiga gidan suna masu hada baki gurin yin sallama.
Babbar tabarma ce wadda Ruqayyah ta tabbatar aro wa aka yi daga gidan su Minal a shimfide a tsakar gidan, akan ta akwai wata mata wadda idan gaskiya za’a bi zata iya girmar Inna ade amma a kamanni zata iya cewa Inna ade ta haife ta. Kana ganinta kasan cewa naira ta zauna mata. A tare da ita akwai yammata, su biyar reras, wadansu farare wasu bakake. A gaban su da tray shima da aka aro a gidan su Minal aka siyo pure water mai sanyi guda goma aka zuba akai.
Daga gefen su karamar tabarma ce wadda tasu ce ta gida, akanta Baba ne tare da Inna Ade fuskokin su dauke da faffadan murmushi. Gabaki daya jama’ar gurin suka amsa musu sallamar. Inna Ade tace “yauwa, gasu nan ma sun dawo” Aunty tana kallon yan biyun da suke karasa shigowa tsakar gidan tace “tubarkallah masha Allah, ashe suma yan biyu ne?” Inna Ade ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Hassana tace “Kai! Amma fa kyawawa ne, wacece takwarar tawa?” Inna Ade ta dago tana kallon ta tace “kuma yan biyu ne?” Hassana tace “a’a, ni suna kawai naci, yayyen mu maza ne dai yan biyun. Shi wanda kuka taimaka shine Hassan, akwai hussainin sa”.
Daga dan nesa su Ruqayyah suka durkusa suna gaishe da bakin. Duk suka amsa da fara’ar su. Aunty ta miko hannunta, ku zo kusa dani ku zauna kunji yayan albarka? Wacece hassanar a cikin ku?” Da sauri Sumayya ta nuna Ruqayyah itama Ruqayyah ta nuna Sumayya. Duk aka kwashe da dariya. Inna Ade tace “Ruqayyah ki amsa mana anayi miki magana” Ruqayyah ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da tsinke a kasa tace “na’am” Aunty ta taso da kanta tazo har gabanta ta ruko hannunta tace “zuwa nayi har gida inyi miki godiya Ruqayyah. Nagode Nagode Nagode, Allah ya biya ki da gidan aljanna” duk sukace ameen banda Ruqayyah da take murmushi kasa kasa tana boye fuskarta.
Aunty tace “Allah yasa wannan abu daya faru ya zama silar zumunci a tsakanin mu daku zumunci na har abada. Dan mu kam abinda kukayi mana ba zamu iya biyan ku ba, bamu da kudin da zamu iya biyan ku fatan da zamuyi kawai shine mu hada jini daku idan kun amince. Shine kadai sakayya”.
Bayan baƙin sun tafi, Inna da Baba sun tafi rakasu mota su kuma su Ruqayyah sun shiga daki suna cire uniform dinsu sai Ruqayyah ta daga labule tana leken waje tace “ni banga ana shigo da kwalayen ba” Sumayya ta ce “wadanna kwalaye kuma?” Ruqayyah tace “kina nufin wai hannu rabbana suka zo mana gida? Sai pure water din mu da suka shanye?” Sumayya tace “ho! Rukee. Wai duk bayanin matar nan baki fahimta ba?” Ruqayyah ta saki labulen tana kallon ta tace “wanne bayani fa? Ni ban fiye gane dogon bayani ba nafi son in ga aiki a aikace” Sumayya tazo ta kama hannun ta tace “ni abinda na fahimta daga bayanin ta shine kamar tana neman aure ne a gidan nan. Kamar tana nema wa wannan mutumin da naji sun kira da Hassan auren ki”.
Ruqayyah ta saki hannunta tana kallonta dalala da baki cikin mamaki, she never thought it possible, ta dauka yana da aure sannan da jerin manyan yammatan da suke rushing a kansa, bata taba tunanin mutane irin su zasu nemi hada zuri’a da irinta ba shi yasa dam bata gane bayanin ba. Ita jira kawai take taga an miko.
Sai ta kama rawa tana juyi a dan karamin dakin nasu, Sumayya tana dariya cikin taya yaruwarta farin ciki. Har sai da hajijiy ata kama Ruqayyah ta fada kan katifar su tana birgima. Sumayya tazo tana janye kayan shanyar su data debo tana cewa “ni daga mana kaya kar kiyi masu squeezing ki kara min wahalar guga” Ruqayyah ta jawo ta ta fado jikinta tana cewa “ke ta guga kike yi? Yar uwarki zata zama matar CEO na H and H amm kina damun kanki da guga?” Sumayya ta mike zaune tana dariya tace “zata zama kika ce, ba wai ta zama ba. In banyi gugar ba ai ba zaki samu kayan sakawa ba in CEO din yazo ganin ki” Ruqayyah ta mike tsaye tana kallon kanta, ta dauko mudubi ta kalli fuskarta sannan ta ajiye tana cewa “farko aiki zan saka shi ya fara bawa Baba, Babban aiki irin wanda hatta yan Zariya sai sun san yarsa tayi babban kamu. Sannan sai in saka ya rushe gidan nan ya gina mana wani, irin gidan Alhaji Kabiru sabon kudi wanda aka saka tiles har a jikin bango. Kuma ginin hawa uku nake so, kasa su Zunnur ne zasu zauna tare da abokansu da suke kwana tare a shagon Bala, hawana biyu kuma inna ade da Baba, hawa na uku ni da Sumayya, sai im saka ayi min personal balcony a can sama inda zan ke hawa ni kadai ina kallon kowa a kasa na, ina kallon duk unguwar nan a kasa na, ina kallon kaduna a kasa na. And that, will only be the beginning”