TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wannan littafin na siyarwa ne, wanda yake so ya nemi wannan numberTwelve : A Kind Suggestion
Sumayya da tun da Ruqayyah ta fara lissafin ta take tsaye a bayanta rike da kaya a hannu baki a bude cikin mamaki, tasan yaruwar tata tana da dogon biri amma bata taba sanin cewa burin nata ya kai tsahon haka ba sai yau.

Gida mai hawa uku, balcony, kallon kowa a kasa, lallai Ruqayyah ta wuce duk inda Sumayya take tunani. Tace “Ruqayyah? Duk wannan lissafin kawai dan babarsa ta nuna tana so a haɗa ku? Tun shi bai ce yana son ki ba tun baku fahimci juna ba ballantana ayi zancen auren har kin fara lissafin abinda zaki samu daga gare shi? Tabbas zaki fara ginin auren ki akan tubalin toka dan kuwa shi aure ana gina shine saboda Allah ba wai saboda abin duniya da ake burin za’a samu ba”

Ruqayyah ta juyo tana kallonta, ita lissafi take yi a zuciyarta ba ta san cewaa fili tayi maganar ba amma so what? Waye baya son kuɗi? Kowa fa aka bashi daɗin su zaiji amma mutane da munafurci sai suke nuna wa kamar basa so.

Ta hade rai tace “shikenan kuma yanzu Sumayya mutum bashi da ikon ya fadi a binda yake zuciyarsa sai a sako shi gaba da wa’azi? Ni banga aibu dan mutum ya nemi duniya at the same time kuma ya nemi lahira ba. Shi yasa ake addu’a ana cewa rabbana atina fidduniya hassanatan wa fil akhirati hassanatan…….” Sumayya tace “kyakkyawar rayuwar ake nema ba wai kudi ba Ruqayyah, kudi ba shine farinciki ba, kudi ba shine abu mafi muhimmanci a rayuwa ba Ruqayyah. Happiness. Ka zauna cikin farin ciki shine abinda ake nema, wannan kuwa baya samuwa sai da wadatar zuci ba wai wadatar aljihu ba, the more kina samun kudi da more kina kara jin cewa ya kamata ki samu wasu, amma in dama baki saba dasu ba You will be contented with the little you have. Ni wannan shine abinda na fahimta, wannan shine abinda nake so. Wadatar zuciya. Kuma su kudi a fahimtata sukan kawo rabuwar kawuna ne a cikin iyali. Idan family da basu da kuɗi kamar mu din nan zaki ga sunfi haɗin kai ana haduwaa rufawa juna asiri but the moment kudi ya shigo ciki sai kiga an samu rarrabuwar kawuna musamman idan wani bangare ne ya samu kudin wani kuma bai samu ba. Ni abinda nake gudar mana kenan. Ruqayyah bound din da yake tsakanin mu yafi min gida mai hawa ukun da kike buri”

Ruqayyah ta jawo ta jikinta tace “my darling sister, ba kudi ba, babu abinda zai raba tsakanin mu, duk inda zanje a rayuwa duk matakin da zan taka a rayuwa you will always be by my side, family na will always be y top priority, shi yasa a lissafin nawa Baba na fara sakawa nasan yana wahala damu” Sumayya ta zame daga jikinta tace “how can I be always by your side idan kika auri CEO na H and H? Zaku tafi ne unguwar masu kudi ya gina muku gida mai hawa biyar. Ni ma kuma dole zanyi aure, yanzu misali in na auri……. Na auri….. Na auri Adam drivern taxi yaje ya kama mana hayar gidan kasa kinga ai mun rabu kenan, banbancin yayi yawa”

Ruqayyah ta kuma jawota tace “sai in saka mijina ya gina muku gida a kusa da gidan mu ya baku kyauta dan mu zauna tare” ta hade rai tace “kuma ba zaki auri Adam ba, kar ki ma kuma saka shi a misali” ta fita ta tafi yin alwala tana mita “na tsani wannan gayen wallahi, he is so arrogant and rude, gashi shi ba kowan kowa ba amma in yana magana kamar yafi kowa” tayi tsaki “inyamuri kawai. Watakila ma ba musulmi bane ba”.

Ruqayyah tayi ta saka ran taji Baba ko Inna Ade sunyi mata maganar abinda bakuwarsu tace amma sai taji shiru, in ta taso da maganar sai Inna Ade tayi saurin chanja topic saboda bata son sauran yaran su san da maganar, Ruqayyah ta cika tayi ta kumburin ta sai duk suka shareta saboda dama ta saba fushin ta ita kadai.

Sai da dare bayan duk yara sun watse sannan Inna Ade tace wa Baba “Baban biyu ka fahimci inda maganar bakuwar na ta dosa kuwa? Ka gane abinda naso na gane?” Yayi ajjiyar zuciya yace “na fahimce ta uwar biyu, kawai dai nayi shiru ne kuma kema ina son ki cigaba yin shiru akan maganar saboda bama bukatar wani yazo ya gaya mana cewa mutanen nan ba sa’annin auren yayan mu bane ba, bana fatan yiwa yayana aure a gidan da za’a wulakanta su duk da dai su wadannan naga kamar ba irin sauran masu kudi bane ba, ni nafi son suyi karatu su nemi nasu na kansu ba wai su jingina da wani ba. Sannan kuma ita matar nan zata iya yiwuwa kawai nata ra’ayin ta fada bawai ra’ayin shi yaron ba, in yaron yana so da kansa zai zo ya nema. Dan haka mu bar maganar, muyi ta addu’a,idan yazo ya nema din kuma an samu daidaito tsakanin sa da yarinyar sannan mun bincika mun tabbatar da nagartarsa to alhamdulillah sai mu bashi ita” Inna Ade tace “to Allah ya shi ge mana gaba, ni ba wai maganar auren ce ta bani tsoro ba halin Ruqayyah nake gudu,dama Sumayya suka ce da sauki”

Baba ya kalle ta kawai ya dauke kai, amma maganar ta ta tsaya masa a rai. Tabbas gaskiya ta fada, duksu biyun yayansa ne amma suna da banbanci kwarai da gaske ta fuskar halayya.

A ɓangaren su Aunty bayan kuwa bayan sun koma gida su Nafisa suke ta zancen gidan. Hassana tace “Amma Aunty mutanen nan daga ganinsu suna da hali na gari, kinga yadda suka tarye mu da kulawa da karramawa? Basu da kudi amma tabbas suna da kamala” Safiyyah tace “suna kuma da addini, yanayin shigarsu da nutsuwar ƴaƴan ta birgeni” Khadijah tace “da tsaftar gidan, har muka fito banga datti ko digo ba, kayan sawarsu sun tsufa amma babu datti a jikin su” Nafisa tace “gasu kyawawa, kai twins din nan akwai kyau. Wato in suka samu kulawa sai an jinjina irin kyawun da zasuyi” Zulaihat tace “a yanzun ma ni banga alamar yunwa a tattare dasu ba, basu da rama kuma basu da datti. Hoda kawai suke bukata da jambaki” duk suka kwashe da dariya. Aunty tace “nima nutsuwa da tarbiyyar yaran ta bani sha’awa. Allah dai yasa yarinyar nan rabon Hassan ce dan ni kam nayi masa sha’awar ta sosai. Gata yarinya karama yadda juya ta ya kuma tarbiyyan tar da ita yadda yake so”

Wannan yasa washegari tana tashi ta kira Hassan, Hussain ni ya dauki wayar suka gaisa sannan ya bawa Hassan da yake kwance yana ta juyi. Ya karba ya gaishe ta sannan tayi masa bayanin zuwan da tayi gidan su Ruqayyah

“Jabir ne ya karbo min address din a gurin police, gaskiya Hassan naji dadin ganin yaran nan da iyayensu. Alamu na zahiri sun nuna cewa mutanen kirki ne, badini kuma Allah ne ya barwa kansa sani” Hassan ya shafa sajen fuskarsa yana murmushi a ransa yana jin kamar an yaye masa wani nauyi yace “naji dadi sosai Aunty, naji dadi da kika yaba dasu” sai kuma ya danyi shiru cikin jin nauyin Aunty yace “kin ganta?”

Sai da tayi dariya sannan tace “na gansu, su biyu ne ita da husainar ta. Kamar su daya komai nasu daga, daga dukkan alamu basu kammala secondary school dinsu ba dan ba gansu da uniform” ya gyada kai yana tuno fuskar Ruqayyah sanda take daure masa ciwon sa,ya lumshe ido ya bude yace “Nagode Aunty” suka yi sallama ya ajiye yana kallon Hussain take ta zabga masa harara, ya dga kafada yace “me nayi?” Hussain ya gyara zama yace “sai wani murmushi kake yi wai kai nan kayi budurwa. A dai bi a hankali” Hassan yayi dariya har sai da yaji wuyansa ya amsa sannan yace “oho dai” Hussain yace “wai yarinyar da ka hadu da ita cikin mintinan da basu wuce talatin ba, sannan kuma cikin tsakiyar dare ita ce kake ta kwarara wannan murmushi saboda ana yi maka maganar ta” ya danyi dan karamin tsaki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button