TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL
Hassan ya mike daga kwanciyar da yake yi ya hade rai yace “ai ba mintuna ko lokacin da muka hadu ɗin ne madu muhimmanci ba, abinda tayi a cikin mintinan shine abu mai muhimmanci, ni na kasa gane kan ka Hussain, yarinyar nan fa rayuwata ta ceta, I owe her my life. Amma maimakon ace ka kasance mai farin ciki da ita sai kake furuci masu daci a kanta. It hurts me wallahi, and it makes me question matsayi na a gurinka”
Hussain ya ajiye magazine din hannunsa yace “haka ne, I should be grateful to her, but bansan me yasa ba nake jin something odd about her ba, kawai ji nake sam ban yarda da ita ba” Hassan yayi murmushi yace “kamar yadda nima farkon soyayyar ku da gimbiya nake jin ban yarda da ita ba, gashi yanzu na fara sabawa da ita har muna zama muyi hira, kamar yadda na yarda da gimbiyar ka kaima one-day zaka yarda da tawa gimbiyar”.
Sai da suka yi sati uku a can sannan suka dawo Nigeria, a lokacin Hassan ya warware sosai har ya maida kibar sa kuma yayi haske abinsa, Hussain wata daya yaso suyi amma Hassan yaki yarda dan shi Allah Allah yake yi su dawo yaje yaga Hassanar sa. “Kar tayi fushi, tace naki zuwa”
Ai kuwa Ruqayyah tayi fushin, tun tana kirga kwanaki har ta koma lissafin sati, gashi iyayenta sunki kwata kwata suyi mata maganar, Sumayya ma ta share ta. She became very edgy daga an taba ta sai bala’i har yan gidan duk suka share ta suka daina shiga harkarta. A haka har suka kammala neco dinsu, shikenan suna daina zuwa makaranta tunda ba waec zasu yi ba. Wannan zaman gidan shi ya cigaba da frustrating Ruqayyah, har mafarkin Hassan take yi wai ya dawo daga kasar waje ya siyo mata sabuwar waya mai kyau ƴar yayi.
A ranar kuwa ya dawo kasar, washegari ya taho ganin ta. Drivern da ya kawo su Aunty shi ya saka ya rako shi gidan tunda ba zai gane ba. Suna yin packing yabi katangar gidan da take rabi ta langa langa da kallo yana tuno memory din ranar nan sai ya jinjina hikimar ubangiji, ya tuna sanda ya shiga gidan ta tsakanin langa langa ya kwanta a toilet din gidan yana birgima saboda azabar ciwon da yake ji a kafarsa da jinin da yake zuba a wuyansa.
Ya tuna sanda ta shigo toilet din tayi fitsari a gabansa ba tare da tasan yana gurin ba, yayi murmushi tare da alkawarin wata rana sai ya tsokane ta da abin, ya lumshe idonsa yana misalta yadda zata ji kunya ta kifa kanta a kirjinsa tana cewa “kaga bana so, ka daina tsokana ta, Allah zan rama nima” ya sake yin murmushi shi kadai yana girgiza kai, yasan da Hussain yana kusa dashi da sai ya dungure shi yace masa “idiot”.
Drivern ne ya fita ya nemo yaro sannan ya tambayi Hassan “oga Hassan wa za’a ce ana kira?” Ya sake murmushi kamar idiot sannan yace “Hassana. Kace Hassan ne yazo yana son ganin Hassana” yaron da drivern duk suka yi dariya sannan yaron ya shiga ciki.
Wanke wanken kwanuka take yi tana mitar Zunnur da ya ki cin abinci dare da Sulaiman ya zuba nasa daban ya kara mata kayan wanke wanke. Sumayya tana dora wa yara karatu akan baranda Inna kuma tana ruɗa tuwo. Yaron ya gaishe da inna sannan yace
“Inji wani mai babbar mota yace wai Hassana tazo inji Hassan”
Karaf a kunnuwan Ruqayyah, ta saki kwanon hannunta tana juyo wada sauri idanuwa a waje, suka hada ido da Inna, sai ta mike da sauri tana wanke hannunta da ƙafafuwan ta. Inna ta ajiye muciyar hannunta sannan ta bita dakin, kafin ta shiga har Ruqayyah ta birkito dukkan kayan su na cikin bagko tana neman wadanda suka fi ko wanne kyau. Inna ta tsaya tana kallonta tace “gashi kuma baban ku baya nan ballantana a tambaye shi izinin ki fita gurinsa”
Ruqayyah ta yar da rigar hannunta ta juyo idonta har ya ciko da kwalla “Inna yanzu kuma jira zai tayi a waje har sai Baba ya dawo? Baban da bamu san lokacin da zai dawo ba? Inna tunda ke kina nan ki bani izinin mana, in Baba baya nan ai ke ce wakiliyarsa” Inna Ade ta girgiza kanta tana tabbatar wa da kanta hasahen da tayi akan Ruqayyah dai dai ne, sai dai kuma abinda Ruqayyah ta fada gaskiya ne, bai kamata abar bakoa waje yana jira ba kuma ita bata da waya ballantana ta kira baban biyu ta gaya masa labarin zuwan bakon.
Sai tace “bana son ku tsaya dashi a waje, bana son kuma ku zauna a cikin motarsa, gashi kuma bamu da soro ballantana ya zauna. Abinda za’a yi bara in sallami yaran nan sai ayi masa shimfida a tsakar gida ku zauna ku gaisa, dake da Sumayya zaku je. Ni kuma zan zauna a daki. Ki kiyaye ni Ruqayyah, in kika nuna masa halinki wallahi xan saka baban ku ya gaya masa kar ya sake zuwa gidan nan” Ruqayyah tayi saurin gyada kanta, ta yarda, ta yarda da ko wanne sharadi in dai za’a bata wannan chance din. Wannan chance ne one in a million ta samu kuma ba zata yi wasa da shi ba.
Tana cikin shirya wa Sumayya ta shigo itama ta wanko fuskarta, duk basu yi kwalliya ba sai mai da suka shafa suka saka kaya da dogayen hijabs dinsu. Sannan Sumayya ta shimfida tabarmi guda biyu a kasan bishiya sannan ta shimfida sallaya a saman tabarma daya. Ruqayyah kuma ta dauko sabon kwanon shan ruwan Inna Ade ta debo ruwa ta ajiye sannan ta dora kofi akai.
Sumayya ce ta fita kiransa. Yana motar dai a zaune suna hira shi da drivern, lokaci zuwa lokaci yana kallon kofar shiga gidan zuciyarsa tana son ganin fitowarta. Sai ga Sumayya ta fito, idonta ya sauka kan motar amma da yake tinted glass ne bata hango na ciki ba amma shi ya hango ta, yaji bugun zuciyarsa ya karu, ya dakata da hirar da yake yana samun damar kare mata kallo tare da tunowa da waccan fuskar da ya gani ranar nan. Abinda ya fara fahimta a tare da ita shine yadda take tafiya cikin nutsuwa. Ta tsaya a gaban motar cikin yanayin rasa abinyi. Sai kuma tayi sallama tare da knocking window din. Yaji dadin sallamar da yaji tayi. Ya sauke glass din window din a hankali sannan ya sauke idonsa cikin nata. Tayi murmushi mai fadi, ko ba’a gaya mata ba ta san shine wannan duk da cewa ranar nan bata wani ga fuskarsa sosai ba.
Ta dan durkusa kadan tace “ina yini, sannu da zuwa” ya jefa mata best smile dinsa yace “lafiya lau…..” Sai ta katse shi “ammmm an ce ka shigo ciki, Ruqayyah Hassana tana ciki” ya kankance idonsa yana kallonta cikin mamaki, sai ta danyi yar dariya tace “ni sunana Sumayya….” Yace “Hussaina?” Ta daga masa kai ya bude kofar motar ya fito ya na kallon ta yace “gwara in gane ki sosai kar aje ayi min chanje”
ta sake dariya, ya fahimci tana da fara’a sosai tace “baza ayi maka bama, ka kwantar da hankalinka” suka jera yana cewa “amma kuna kama sosai fa” tace “haka ake cewa, amma if you get to know us zaka gane banbancin mu” ita ta fara shiga sannan shi, abinda ya fara lura dashi shine tsaftar gidan da kuma alluna alamar ana koyar da karatu a gidan. Sai kuma yaga shimfidar da akayi masa sannan yaji kamshin tuwon da yake kan wuta. Ya zauna akan shimfidar sannan Sumayya ta durkusa ta sake gaishe shi, ya amsa mata cikin kulawa sannan ta tambaye shi mutan gida.
A lokacin Ruqayyah ta fito daga dakin su, kanta akasa, hannayenta a boye a cikin hijab dinta, fuskarta cike da wani yana yi mai wahalar fassara. Tun da tayi taku na farko taji idonsa ya saukaa kanta, sai taji wani irin yanayi ya lullube ta taji abin duk ba yadda tayi tsammani bane ba, taji ta kasa dago kai ta kalle shi, taji kuma tana son ta kalle shi din.