TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Kan daya tabarmar taje kusa da Sumayya ta zauna tare da gaishe shi murya can kasa ” ya jikin? Allah ya kara lafiya” ya dan kalli dakunan d aduke gefe, ya san akwai mutum a cikin dakin dan haka dole yayi ajjiyar kalamansa sai wani jikon kuma. Amma shi kam yasan zuciyarsata tafi ga wannan yar karamar yarinyar da take kokarin gaisheshi. “Ya naki jikin? Ina fatan ranar nan baki ji ciwo ba” ta girgiza kanta tace “babu ciwo, Nagode” ya sunkuyo yana kokarin kallon fuskarta sai ta kara jawo hijab dinta ta kara rufe fuskar, ya danyi murmushi mai sauti yace “kin gode da me?” Tace “da ka damu dani har ka tambayi lafiya ta” yace “lallai ke ɗin ta daban ce tunda har zaki yi min godiya bayan nine ya kamata inyi miki godiya. Ki sani Hassana, bana jin akwai abinda zanyi miki wanda zai nuna irin godiya ta gare ki, duk abinda zanyi kwatanta wa ne kawai amma ninba zan iya biyan ki ba, Allah ne kadai zai biya ki. Ina kuma fatan ya biya ki da aljannar firdausi”
Sumayya tace “ameen, tare da mu baki daya” ya sake kallon dakin yana feeling uncomfortable, akwai maganganu daya ta tsarawa tun a India amma duk ba zai iya fadin su ba a wannan setting din, dole ya bar wannan ziyarar a matsayin ta godiya kadai in yaso in ya kuma xuwa ya fara kafa gwamnatin sa. Amma duk da haka zai gwada ko dan kadan ne, at least dan asan inda ya dosa.
Ya kalli Sumayya yace “kinga har na gano banbancin ku da Hassana ta” Sumayya ta bude ido tace “menene banbancin?” Yace “Hassana ta ta fiki nutsuwa, ta fiki kunya tunda gashi nan ta kasa kallona har yanzu kuma ta kasa bari in kalli fuskarta. Ki roka min ita ta kalle ni ko da sau daya ne kar ta saka yau in manta hanyar gidan mu in dawo nan in kwana”
Sumayya tayi dariya tace “in kai ka manta drivern ka aishi ba zai manta ba” ya dafe kai yace “haka ne fa. To amma ai na kasa bacci ko? In banyi bacci ba kuma kinga ba zan samu karfin da zan dawo gobe in tambayi Baba ya bani izinin fara zuwa zance gurinta ba” Sumayya ta sake dariya, Ruqayyah ma ta danyi dariya a cikin hijabin ta, tana kallon saitin fuskarta ta cikin hijab din yace “kuma na sake gano wani banbancin naku, ta fiki kyau, dan na hango dogon hancinta ta jikin hijab” Ruqayyah tayi sauri ta kuma jan hijab din gaba yadda fuskarta ba zata fito ba.
Yayi gyaran murya yace “abinda duk nake nema zan iya cewa na same su gabaki daya a gurin ki Hassana. Addini, tarbiyya, kunya, nutsuwa, kyau duk kina dasu. Ni na riga na samu mata Ruqayyah in dai kin amince kina sona ni da gaske nake aurenki zanyi in dai har iyayenki zasu bani ke” ya sake rage murya yace “amma ai ba zaki amince ba in nayi miki, ba zaki gane nayi miki ba kuma sai kin kalle ni” Sumayya ta kuma yin dariya, sai yaga tana tuna masa da Hussain ta bangaren fara’a. Sai ya samu kansa da fara yi mata hirar Hussain.
Ruqayyah ta dan bude fuskarta kadan ta mike ta zuba masa ruws a kofi tace “ga ruwa, ka sha” ya karba yana cewa “nagode sosai” sannan ya kalli Sumayya yace “kinga inda aka damu dani an fahimci ban sha ruwa ba, ke kuwa sai magana kuke saka ni” Sumayya tace “to bara in tashi in tafi in ya so sai kuyi hirar kurame tunda na fahimci ba magana zata yi maka ba” ya shanye ruwan ya ajiye cup din yace “kiyi zamanki, nine dai zan tafi. Ki mika min gaisuwata a gurin Mama sannan ki yi kokari gurin kafa min gwamnati na, ki fara da Foundation mai kyau dan ginin da nake so inyi na har abada ne”
ya mike sannan yace “in Baba ya dawo ki gaishe min dashi sannan ki gaya masa in babu damuwa gobe da kamar wannan lokacin zan dawo ina son magana dashi” ta amsa masa da insha Allah, sai ya dauko daurin kudi ya ajiye akan shimfidar yace “gashi ki sayi sweet, dan naga alamar kina da kwadayi”
Ranar Ruqayyah bata iya bacci ba. Tana ta sakawa da warwarewa.
Washegari ya dawo kamar yadda yayi alkawari. Baba kuma already yana zaune yana zamn jiransa kuma ya yanke shawarar abinda zai gaya masa, danda aka aiko ya zo sai Baba ya saka Sulaiman ya shimfida musu tabarma a waje daga gefe inda mutane ba zasu dame su ba, sannan ya fita gurinsa.
Ganin haka yasa Ruqayyah ta kira Zunnur ta tambaye shi a inda suke, ita kuma ta tafi dai inda suke daga cikin gida tayi shimfida ta zauna tana yanke farcenta. Kawai haka nan taji zuciyarta tana son taji maganar da zasu yi.
A waje Hassan ne tare da Jabir, yaso Hussain yazo du taho tare amma sai ya kirkiri wani excuse ya kawo amma Hassan ya fahimci zuwa ne baya son yi kuma yaji babu dadi. Bayan sun gaisa cikin mutunci da girmama juna, sun kuma yo doguwar godiya a bisa taimakon da aka yiwa Hassan a gidan sai Jabir ya shigar da maganar kudirin Hassan na neman izinin fara neman auren Ruqayyah.
Baba ya masu kudurin su cikin nuna jin dadin wannan karramawar amma kuma sai yace “amma wani hanzari ba gudu ba, ni ba zan boye maka ba tun ranar dana fara ganinka naji zuciya ta tana sonka, naji a raina ina ma dai kai dana ne, kuma yanzu zanji dadi sosai idan ka zamo dan nawa wato in ka auri yata, sai dai, in har ka amince ina son ka chanza daga Ruqayyah ka nemi Sumayya”
Ruqayyah ta dago kai daga yankan farcen ta, ba tare da ta ce komai ba ta mike ta tafi daki tana jin zuciyarta ta zama tamkar dunkulallen garwashin wuta.
Wannan littafin na kudi ne, duk mai son siya tayi wa wannan number din magana 08067081020
08067081020Episode thirteen: The Strategy
Duk suka yi shiru suna kallon sa, Hassan cikin sanyin jiki yace “saboda me Baba?” Baba yace “Saboda kamar yadda na fada ina sonka, duk su biyun yaya na ne basu da banbanci a guri na kuma suma duk ina son su, dan haka nake fatan idan sunyi aure auren nasu zai zauna har mutuwa, bana fatan ka auri yata kuma ka rabu da ita saboda wani hali nata da zaka ga baiyi maka ba, wannan shi yasa nake ganin alakar ku zata fi tafiya daidai da Sumayya, saboda a yadda na fahimta kamar halin ku yafi zama daya akan ita Ruqayyah”
Jabir yayi gyaran murya yace “Baba ita Ruqayyah tana da wani aibu ne? Wani hali da ya kamata a sani kafin a aure ta? Ko tana da wata cuta ce?” Baba ya girgiza kai, Ruqayyah yarsa ce kuma yana sonta, kuma son da yake mata ne ya saka shi wannan batu, aure ba abin wasa bane ba, ba kuma a gina shi a kan ƙarya da rufa rufa in dai har ana so ya dore. Yana son auren Ruqayyah da Hassan ya dore in dai ya kasance, shi yasa zai gaya masa in zai aure ta a haka shikenan in kuma ba zai iya ba sai ya karbi Sumayya in ita ma baya so shikenan.
Yace “Ruqayyah tana da zafin zuciya sosai, taurin zuciya da kafiya, ko mu iyayenta muna fama da ita a kan hakan. Bata da son mutane sosai saboda tana da fada, bata da tsoro sam. Kai kuma na fahimci mutum ne mai jama’a dan haka nake ganin kamar tafiyar ku ba zata zo daya ba”
Hassan ya shafa kansa yana sauke ajjiyar zuciya, shi baiga aibu a duk abinda Baba ya fada ba, dama ai ya riga yasan da rashin tsoron da taurin zuciyar tun sanda ta taimaka masa, rashin son mutane kuma shi zai iya cewa abin dadi yayi masa dan shi din ma ba mai son mutanen bane ba dan haka kullum yake fatan kar ya samu mace mai kwashe kwashen mutane yadda zasu ji dadin zamansu su kadai.
Yayi murmushi yana kallon Jabir shima da yake murmushi, sun dai fahimci cewa Baba mutum ne mai karanci da yawa yadda har zai fada musu abinda yake ganin aibu ne akan yar da ya haifa a cikinsa saboda ya kyautata dangantakar sa da su. Hassan yace “Baba ni ina ganin wannan ai duk ba wani abu bane ba, wannan ba abinda zai hana ayi aure bane ba, kuma ni itan dai Baba in za’a bani ita nake so Sumayya kuma sai ta zama kanwata” Jabir yace “wannan haka ne, kuma kusan duk halin daka lissafa irin na Hassan ne” ya fada cikin tsokana, “haka muke ta fama dashi, baya daukan raini ga kafiya, ina jin abin nasu a sunan ne” suka yi dariya su biyu banda Baba, shi gani yake yi kamar basu fahimce shi bane ba, amma zama da Ruqayyah su kansu da suka haife ta dauke kai kawai suke yi a lokuta da dama, suna ta yi mata addu’a kuma suna saka ran idan ta kara girma zata rage, sai dai baiyi tsammanin za’a zo neman aurenta haka da wuri ba. Yayi wa Hassan tayin auren Sumayya ne saboda yana ganin Hassan da Ruqayyah ba wai saba wa suka yi da junansu ba.