TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace “shikenan tunda kunji kuma kun amince, kunga nan gaba ba zaku zo min da korafi ba kuma. Zamuyi ta muku addu’a, Allah yayi mana jagora baki daya, Allah ya hada kanku. Na baka damar ka neme ta, idan kuma ka chanza shawarar a tsakiyar neman ka sani ba zan kullace ka ba sai dai ba kuma zan baka Sumayya ba a lokacin”.
Hassan yace “insha Allahu hakan ma ba zata faru ba. Kowa a duniya ai dole yana da wani aibu da wadansu daga cikin mutane ba zasu so ba, ko ba Ruqayyah ba nasan bazan samu mace da take da komai ba dole sai an samu aibu”.
Suka yi godiya, sannan Baba ya jero musu doguwar addu’a duk duka shafa suka tashi. Hassan yaso yaga Ruqayyah amma kuma yana jin nauyin Baba, haka ya shiga mota suka tafi yana kallon kofar gidan da fatan ko Allah zai saka yaga giftawar ta.
Ruqayyah tana shiga daki sai ta kwanta akan katifa ta jawo zani ta lulluba duk da ba wai sanyi take ji ba, so take tayi kuka amma kukan yaki zuwa, haka taje ji lokuta da dama idan aka bata mata rai sai dai tayi ta jin zafi a ranta ba zata iya kuka ba har sai ta samu tayi masifa tukunna zata ji ta huce. Idonta ya kada yayi jawur kamar garwashin wuta. Anya kuwa Baba ne ya haife ta? Anya kuwa uban da ya haifi ya zai iya yi mata abinda Baba yake shirin yi mata? Har zai ce zai bawa Hassan Sumayya? Zai ce da Hassan kar ya aure ta? Ita kuwa wanne irin laifi tayi wa Baba da yayi mata irin wannan tsana haka?
A lokacin Sumayya ta shigo dakin, farko bata lura da Ruqayyah ba sai daga baya ta ganta a takure a karshen katifa, ta taba jikinta da sauri “innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Ruqayyah baki da lafiya? Menene ya same ki?” Sai a lokacin Ruqayyah ta samu hawaye suka zubo mata, ai kuma ta fara rera kuka marar sauti kamar zata fito da zuciyarta, Sumayya kawai ya rungume ta ta barta tayi ta kukanta sai data gama sannan tace “Sumayya Baba baya sona ya tsane ni” da sauri Sumayya ta rufe mata baki tace “subhanallah, me kike fada haka? Baba yana son mu mana, yana son mu sosai da sosai” Ruqayyah tana girgiza kai tace “yana sonki dai amma banda ni. Ni ya tsane ni kamar bashi ya haife ni ba” sai ta bata labarin abinda taji.
Sumayya ta dora hannu aka fuskarta rubuce da tashin hankali sannan ta sauke tace “me ya kaiki Ruqayyah? Me ya kai ki zuwa kiji abinda zasu ce, ina ruwanki” Ruqayyah tace “magana ta fa zasu yi, zuciyata tana ta gaya min inje inji abinda zasu ce ashe akwai dalili, ashe zuciyata bata yarda da Baba bane ba”
Sumayya tace “wato ke kuma shikenan duk abinda zuciyarki ta gaya miki shi zakiyi? Ba zaki yi tunani da kwakwalwar ki ba sai kiyi aiki da zuciyarki? Ban shiga ran Baba ba Ruqayyah, bansan menene dalilin sa na fadar abinda ya fada ba amma nasan ba wai dan baya sonki bane ba sai don yana tsoron halinki, yana tsoron kar kije gidan kiyi ta musu halayyar ki azo aji kunya, kuma ni banga laifinsa ba” Ruqayyah ta fara ture ta tana kokarin mikewa tsaye tana kunkuni, Sumayya tace “ko me zaki ce sai dai kiyi ta cewa amma ni dai ba zan daina gaya miki gaskiya ba, kuma ina so ki sani, ko maza sun kare a duniya bazan auri Hassan ba dan haka kar ma ki saka wani abu a ranki, tunda Hassan ya nuna yana sonki to kuwa tabbas ya haramta a gareni. Amma in baki chanja hali ba zaki yi loosing dinsa, ko Baba bai hana shi ke ba shi da kansa zai gudu yace ya fasa”
Ruqayyah tayi hanyar kofa zata fita kuma sai ta tsaya, sai ta juyo tana kallon Sumayya tace “menene zai saka yace ya fasa?” Sumayya ta jawo ta ta dawo da ita zaune tace “halinki. Yadda na fahimce shi shi kamilar mace yake so mai kyawawan dabi’u, to in kina so ya aure ki sai kin zama mai wannan halin, abu mafi muhimmanci kuma sai kin cire son abinsa a zuciyarki, dan in dai ya fahimci kudinsa kike so bashi ba to kuwa zai gudu, ki nuna kudinsa bai dame ki ba, kinuna masa kina sonsa sosai, watakila ma kiga har kin fara son nasa da gaske”
Ruqayyah tace “waye yace miki bana sonsa yanzu” Sumayya tayi murmushi tace “ina fata. In ma kina sonshi to kinfi son dukiyarsa a kansa, ba Hassan kike so ba CEO na H and H kike so, ko ba haka bane ba?” Ruqayyah tace “shi din dai shine duk biyun, to menene abin damuwa a ciki?”.
Sun jima suna hirar abin a tsakanin su, Sumayya tana ta bawa Ruqayyah shawarwari a ranta kuma tana fatan Hassan bai karbi tayin Baba ba saboda in ya karba dole zata yi wa Baba musu, dan ba zata iya auren Hassan din Ruqayyah ba. Ko da ace ita yace yana so zata iya barwa Ruqayyah shi dan a zauna lafiya. Ita farin cikin family dinta shine gaba da komai a gurinta.
A bangaren Ruqayyah kuwa hankalin ta ya kwanta sosai ta jin ikirarin Sumayya na cewa ba zata auri Hassan ba, kuma tasan indai Sumayya tace haka to Baba ba zai matsa mata ba. Sai kuma ta fara duba shawarwarin da Sumayya ta bata, ta kuma yarda lallai Hassan mace ta gari yake nema kuma indai ta nuna masa iri dabiun ta zai iya cewa ya fasa sai dai duk su biyun suyi asarar sa, ita kuma bata fatan wannan irin babbar asara ta same su. Ba dai mace ta gari yake so ba? To kuwa tabbas zai samu mace ta gari. Ita Ruqayyah ta kama shi a cikin faratan ta kuma ba zata taba releasing dinsa ba har sai burin ta ya cika, burinta na zama matar CEO of H and H.
Tagwayen sunyi ta jira suji Baba yayi musu magana akan abinda suka tattauna da Hassan amma bai ce musu komai ba, dan haka suka kasa tantancewa ko Hassan ya karbi tayin Baba ko kuma bai karba ba. Ruqayyah kuma tayi iyakacin kokarin ta na dannewa bata nuna wa Baba cewa taji tayin da yayi wa Hassan ba, sai dai a zuciyarta ta kuduri aniyar cewa zata tabbatar cewa watarana yayi nadama, wata rana sai yayi nadamar zaben Sumayya akan ta.
A bangaren Hassan kuwa fushi yake yi sosai da Hussain saboda halin ko in kula da yake nunawa akan Ruqayyah, rigima a tsakanin su har gaban Aunty “Aunty yaron nan wai yaje yaga yarinyar nan yayi mata godiya akan abinda tayi min amma yaki, kiri kiri yake nuna min kiyayyar sa akanta” Hussain yace “ni nace maka bana sonta? Ni nace maka ina kinta? Kawai hankali na ne bai kwanta da ita ba” Hassan yace “ta yaya to hankalin naka zai kwanta da ita idan baka je ka ganta ba? Ta yaya zaka yarda da ita in baka fahimce ta ba?” Hussain ya mike yace “alright, send me the address, zanje gobe mu gaisa shikenan?” Hassan yace “ba shikenan ba, sai kaje sannan maganar zata wuce”.
Suka mike a tare suka fita suna cigaba da rigimar, aunty ta bisu da kallo sannan ta girgiza kanta, ita da aka zo gurinta da niyyar tayi Shari’a amma ba’a bar ta tace komai ba har aka gama shari’ar.
Bayan sun fita daga gurin Aunty dai suka ajiye maganar Ruqayyah suka koma hirar Company, dama batan Hassan ne ya tsayar da maganar amma yanzu tunda komai ya lafa zasu cigaba da shirye shiryen su. Hassan yace “already dama na riga nayi sanarwar wadanda aka yiwa interview su dawo a sake musu, tunda na rasa duk bayanan su a cikin mota ta data bata” Hussain ya daga kafada yace “shikenan, duk abinda kace haka za’ayi. Ina dai son mu gama daukan ma’aikata as early as possible saboda in samu in mayar da hankali na kan ginin gidan can da kuma sauran al’amuran biki” Hassan ya juya ya kalli side din da twin houses dinsu suke.
Gida ne Hussain ya siya ajikin gidansu, mai gidan ne Allah yayi masa rasuwa sai magada suka saka gidan a kasuwa shi kuma Hussain ya siya, katon gida ne na gaske, amma Hussain ya saka akazo akayi flat dashi, a lokacin sai da suka yi ta rigima da Hassan saboda shi yana ganin rashin dacewar hakan. “Wannan ai almubazzaranci ne” shi kuma Hussain yace “plan din mutum daya ne a gidan, ni kuma so nake muyi twin houses ni da kai yadda zamu zauna da iyalan mu seperately but together, sannan kuma ga Aunty a kusa damu”.