TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace “ban taba jin yammata sunce babu abinda zasuyi da kudi ba sai yau. Ni sisters dina kullum complain suke kudi yayi musu kadan, kullum suna cikin siyan kayan kwalliya, jaka takalmi, da sauransu” Ruqayyah tace “mu duk wannan basu dame mu ba”

Yayi ajjiyar zuciya sannan ya jefa kudin cikin mota, Ruqayyah taji tamkar zuciyarta ya ciro ya jefa a mota amma ta maze, yace “ban taba yin kyauta an dawo min da ita ba sai yau. Amma babu komai, nasan ta inda zan bullo muku” duk suka yi murmushi. Yayi musu sallama ya shiga mota suka matsa ya tafi.

Sumayya ta juyo gurin Ruqayyah “what? Kece kika mayar da wannan kuɗin da kanki?” Tayi ajjiyar zuciya “kar ki kara min bakin ciki akan wanda nake ji already. Ke fa kika yi min wa’azin in chanja hali, to halin nake chanja wa” ta wuce ciki a ranta tana mitar yadda Hussain zai dauki wannan uban kudin a motar Hassan yayi kyauta dashi, Allah kadai yasan irin barnar kudin da yake yi masa.

Hussain yana kallonsu ta mirror har suka shiga gida sannan ya mayar da hankalinsa fully kan tukinsa, ya girgiza kansa, shi har yanzu bai ji tayi masa ba duk kuwa da cewa bashi da wani dalili na feeling like that. He test them with money kuma sunci jarabawar amma still…….

Ya dauki wayarsa ya kira Hassana (kanwarsu) “zan turo miki kudi yanzu kije ki fitar ki danyo min siyayya irin taku ta mata, kaya masu kyau, komai guda biyu iri daya. Zan kuma yi miki aike sai ki hada da kayan ki bawa drivern da yasan gidan su Hassana akai musu ita da yaruwata”.

Bayan sun gama wayar ya kira wani dealer na waya da yake kawo masa wayoyi yace “ina son wayoyi guda biyu, latest. Ka aika min dasu gida”.

Da daddare suna zaune a tsakar gida suna cin tuwon shinkafa miyar taushe har da nama, duk a cikin kudin da Hassan ya ajiye ranar nan ne. Gaba dayansu su hudu a tray daya Inna kuma da Baba suma suna ci tare, ga maganin sauro an kunna a gefe ga iska tana kada su. Baba yana basu labari “wato gobe akwai drama, an sake aiko mana fa mu koma wannan inta uku din nan. Gashi yaron nan Hassan naga alamar bai san dani a ciki ba sai dai kawai ya ganni” a lokacin suka ji tsayuwar mota sannan aka yi sallama. Sulaiman ne ya fita, an jima kadan sai gashi da bagco guda biyu da kuma karamar leda yana ta washe baki.

“Wato yammatan nan sai kun bani tukuici, wai wannan kayan sako ne inji Hussain yace ace muku “asha yammatanci lafiya”.

Wannan littafin na siyarwa ne, in baki sani ba kika karanta a rashin sani to yanzu kin sani. In kina son cigaba ki nemi wannan number 08067081020.Episode thirteen: The Strategy

Duk suka yi shiru suna kallon sa, Hassan cikin sanyin jiki yace “saboda me Baba?” Baba yace “Saboda kamar yadda na fada ina sonka, duk su biyun yaya na ne basu da banbanci a guri na kuma suma duk ina son su, dan haka nake fatan idan sunyi aure auren nasu zai zauna har mutuwa, bana fatan ka auri yata kuma ka rabu da ita saboda wani hali nata da zaka ga baiyi maka ba, wannan shi yasa nake ganin alakar ku zata fi tafiya daidai da Sumayya, saboda a yadda na fahimta kamar halin ku yafi zama daya akan ita Ruqayyah”

Jabir yayi gyaran murya yace “Baba ita Ruqayyah tana da wani aibu ne? Wani hali da ya kamata a sani kafin a aure ta? Ko tana da wata cuta ce?” Baba ya girgiza kai, Ruqayyah yarsa ce kuma yana sonta, kuma son da yake mata ne ya saka shi wannan batu, aure ba abin wasa bane ba, ba kuma a gina shi a kan ƙarya da rufa rufa in dai har ana so ya dore. Yana son auren Ruqayyah da Hassan ya dore in dai ya kasance, shi yasa zai gaya masa in zai aure ta a haka shikenan in kuma ba zai iya ba sai ya karbi Sumayya in ita ma baya so shikenan.

Yace “Ruqayyah tana da zafin zuciya sosai, taurin zuciya da kafiya, ko mu iyayenta muna fama da ita a kan hakan. Bata da son mutane sosai saboda tana da fada, bata da tsoro sam. Kai kuma na fahimci mutum ne mai jama’a dan haka nake ganin kamar tafiyar ku ba zata zo daya ba”

Hassan ya shafa kansa yana sauke ajjiyar zuciya, shi baiga aibu a duk abinda Baba ya fada ba, dama ai ya riga yasan da rashin tsoron da taurin zuciyar tun sanda ta taimaka masa, rashin son mutane kuma shi zai iya cewa abin dadi yayi masa dan shi din ma ba mai son mutanen bane ba dan haka kullum yake fatan kar ya samu mace mai kwashe kwashen mutane yadda zasu ji dadin zamansu su kadai.

Yayi murmushi yana kallon Jabir shima da yake murmushi, sun dai fahimci cewa Baba mutum ne mai karanci da yawa yadda har zai fada musu abinda yake ganin aibu ne akan yar da ya haifa a cikinsa saboda ya kyautata dangantakar sa da su. Hassan yace “Baba ni ina ganin wannan ai duk ba wani abu bane ba, wannan ba abinda zai hana ayi aure bane ba, kuma ni itan dai Baba in za’a bani ita nake so Sumayya kuma sai ta zama kanwata” Jabir yace “wannan haka ne, kuma kusan duk halin daka lissafa irin na Hassan ne” ya fada cikin tsokana, “haka muke ta fama dashi, baya daukan raini ga kafiya, ina jin abin nasu a sunan ne” suka yi dariya su biyu banda Baba, shi gani yake yi kamar basu fahimce shi bane ba, amma zama da Ruqayyah su kansu da suka haife ta dauke kai kawai suke yi a lokuta da dama, suna ta yi mata addu’a kuma suna saka ran idan ta kara girma zata rage, sai dai baiyi tsammanin za’a zo neman aurenta haka da wuri ba. Yayi wa Hassan tayin auren Sumayya ne saboda yana ganin Hassan da Ruqayyah ba wai saba wa suka yi da junansu ba.

Yace “shikenan tunda kunji kuma kun amince, kunga nan gaba ba zaku zo min da korafi ba kuma. Zamuyi ta muku addu’a, Allah yayi mana jagora baki daya, Allah ya hada kanku. Na baka damar ka neme ta, idan kuma ka chanza shawarar a tsakiyar neman ka sani ba zan kullace ka ba sai dai ba kuma zan baka Sumayya ba a lokacin”.

Hassan yace “insha Allahu hakan ma ba zata faru ba. Kowa a duniya ai dole yana da wani aibu da wadansu daga cikin mutane ba zasu so ba, ko ba Ruqayyah ba nasan bazan samu mace da take da komai ba dole sai an samu aibu”.

Suka yi godiya, sannan Baba ya jero musu doguwar addu’a duk duka shafa suka tashi. Hassan yaso yaga Ruqayyah amma kuma yana jin nauyin Baba, haka ya shiga mota suka tafi yana kallon kofar gidan da fatan ko Allah zai saka yaga giftawar ta.

Ruqayyah tana shiga daki sai ta kwanta akan katifa ta jawo zani ta lulluba duk da ba wai sanyi take ji ba, so take tayi kuka amma kukan yaki zuwa, haka taje ji lokuta da dama idan aka bata mata rai sai dai tayi ta jin zafi a ranta ba zata iya kuka ba har sai ta samu tayi masifa tukunna zata ji ta huce. Idonta ya kada yayi jawur kamar garwashin wuta. Anya kuwa Baba ne ya haife ta? Anya kuwa uban da ya haifi ya zai iya yi mata abinda Baba yake shirin yi mata? Har zai ce zai bawa Hassan Sumayya? Zai ce da Hassan kar ya aure ta? Ita kuwa wanne irin laifi tayi wa Baba da yayi mata irin wannan tsana haka?

A lokacin Sumayya ta shigo dakin, farko bata lura da Ruqayyah ba sai daga baya ta ganta a takure a karshen katifa, ta taba jikinta da sauri “innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Ruqayyah baki da lafiya? Menene ya same ki?” Sai a lokacin Ruqayyah ta samu hawaye suka zubo mata, ai kuma ta fara rera kuka marar sauti kamar zata fito da zuciyarta, Sumayya kawai ya rungume ta ta barta tayi ta kukanta sai data gama sannan tace “Sumayya Baba baya sona ya tsane ni” da sauri Sumayya ta rufe mata baki tace “subhanallah, me kike fada haka? Baba yana son mu mana, yana son mu sosai da sosai” Ruqayyah tana girgiza kai tace “yana sonki dai amma banda ni. Ni ya tsane ni kamar bashi ya haife ni ba” sai ta bata labarin abinda taji.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button