TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

TAGWAYE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sumayya ta kuma juyowa cikin fushi tace “gaya min gaskiya Ruqayyah, zaki juyawa Hassan baya ne ki ce hussainin sa kike so kuma? Kina ganin hakan mai yiyuwa ne?” Ruqayyah tace “Ni haka kika ji nace miki? Dan Hussain ya fishi kyau ai ba wai ya fishi komai ba ne ba, Hassan shine babba, sannan shine mai kudin,” Sumayya tace “wrong. Wannan ba shine dalilin da ya kamata ki fada ba na zaben Hassan, ya kamata ki zabi Hassan ne saboda Hassan shi yake sonki ba Hussain ba, Hassan shi ya kamata ki so ba Hussain ba” Ruqayyah tace “shi nake so ɗin ai. Amma dai ai ba haka aka so ba kanin miji yafi miji kyau”.

Sumayya ta runtse idonta tana hana zuciyarta rinjayar ta gurin juyowa ta rufe Ruqayyah da duka. Sai taji cewa ta fahimci menene problem din Ruqayyah, ba wai bakar zuciya ko fada, ko son abin duniya ne da ita ba. A’a rashin godiyar Allah ne da ita. In taga abu zata kwallafa ranta akan tana sonsa amma da zarar ta samu to kuwa ya zama banza abinda ya fishi kuma take hari. And now she have her eyes on Hussain, and Sumayya knows that abinda yasa kawai ba zata rabu da Hassan ta makale wa Hussain ba shine saboda kuɗi, saboda tana son kudin Hassan din. Sai Sumayya taji tana tausayin Hassan. Tana kuma tausayin Ruqayyah saboda karin maganar hausawa da suke cewa “duk wanda bai gode Allah ba to kuwa tabbas zai gode wa azabar Allah”.

Washegari da sassafe Baba ya fita yace musu ya tafi gurin interview, suka yi masa fatan alkhairi ya tafi.

A bangaren su Hassan kuwa suma da sassafe suka fita. Hassan ya kai Hussain airport ya tafi China zai siyo injinan da wancan karon bai samu damar siyowa ba, dama kudin su ne ya hada da kudin da yake account dinsa ya bayar kudin ransom din Hassan, yanzu kuwa tunda alhamdulillah kuɗin sun dawo shine zai koma ya siyo duk da cewa yasan ba zai same su a wadancan price din ba.

Daga airport shi kuma Hassan gurin interview ya zarce, dan yasan cewa yanzu mutane suna nan sun taru suna jiransa shi kuma baya son ya bar mutane suna jiran sa.

Baba yana zaune akan layi tare da sauran mutane, wani ya fara mita “haka kawai bayan mun riga munzo munyi interview din nan, sai da akayi wata guda kuma sannan sai a dawo a sake cewa muzo mu kuma yin wata? Shikenan yanzu a duniya masu kudi basa tausayin talakawa? Wannan ai zalunci ne, gashi kuma mum zo din sannan an shanya mu a waje kamar wasu kayan wanki”.

Baba yace “haba bawan Allah, ba ka san abinda ya samu mutumin nan bane ba? Masu garkuwa da mutane ne fa suka sace shi da kyar ya tsira da ransa” wasu a gurin suka fara jajanta abin wasu kuma suka ce “ina ruwan mu to mu, mu muka sace shi ko kuma mu aka bawa kudin diyyar? Ai irin wannan abin da masu kudi suke yi wa talakawa yana daya daga cikin abinda yake jawo musu irin wancan balain”

Sai Baba yayi shiru kawai ya barsu, dan wadansu mutanen ko yaya ka kai da bayani ba zasu bude kwakwalwar su ba ballantana su fahimce ka. A lokacin ne Hassan ya shigo gurin da saurinsa, Baba ya lura da yadda yake amsa gaisuwar mutane cike da kulawa sannan ya dan bada hakurin jiransa da akayi sai kuma ya shige ciki. Sai Baba yaji dadi a ransa, yaji yana alfahari da shi yana kuma kara saka ran ya zamo surikin sa dan ya yarda dashi, sai dai ita yar tasa ce bai yarda da ita ba.

Akayi ta kira ana shiga ana fitowa har aka zo kan Baba. Ya shiga da sallamar sa. Hassan ya amsa tare da dago kai, suna hada ido da Baba sai ya mike. “A’a, Baba, sannu da zuwa.” Ya fada yana shafa kai, Baba ya zauna sannan shima ya zauna yana gaisheshi sannan yace “Baba ai da an kira ni ni sai inzo gida ba sai anzo nan ba” Baba yace “a’a, ai ba wani abin bane ba, maganar aikin nan ce ta kawo ni an kira mu ance mu sake dawowa za’a sake gwada mu” Hassan ya danyi shiru yana tunani sannan yace “wai wannan aikin dama kaima kazo wancan watan?”

Baba yayi murmushi yace “nazo mana, ai ba zaka gane ba tunda mutanen da yawa” Hassan yayi shiru yana tunani, shi dai ba zai iya hana Baba aikin nan ba ba kuma zai iya bashi ba. Aiyukan na labourers, messengers da kuma na masu gadi ne, ba zai iya saka Baba aiki ba, ba zai iya aikensa ba ba kuma zai iya kullum yana bude masa kofa in zai shigo ba. A matsayin sa na surukinsa hakan bai dace ba.

Ya gyara zama yace “Baba, yanzu misali in aka samu wani kasuwanci haka aka baka, zaka iya hakura da aikin nan?” Baba yace “to Hassan, ni dai ban taba yin kasuwanci ba, ni abinda na sani shine aikin karfi shi nake yi nake ciyar da iyali na har yanzu. Dan haka ba lallai ne in na fara kasuwancin ya dore ba tunda ban san kan abun ba, aikin dai shine, nasan abinda kake tunani kuma ina so ka cire komai daga zuciyarka ka gwada ni idan naci ka bani, wannan shine taimako mafi girman da zaka yi min”.

Hassan yayi ajjiyar zuciya yace “Baba ba zan so in ke ganin ka kana wahala ba, nafi so inke ganin ka kana hutawarka” Baba yace “amma zaka ji dadi in ka ganni ina neman halak dina ko? Hutu kuma ai da saura na tunda da karfi na ba wai shekaru na ne suka ja ba, in lokacin hutawar yayi zan huta ne”.

Haka suka yi ta ja in ja, a karshe dai a dole Hassan ya buga offer ya bawa Baba ya sallame shi saboda wadanda suke kan layi suna jira. Amma a ransa ya kudurce abinda ya kamata yayi akan lamarin.

Baba yana zuwa gida da murnar sa ya fara bawa iyalinsa labari “alhamdulillah, aiki ya samu, aikin gadin nan dai da nake ta buri gashi nan Allah ya kawo shi” ya bude takardar yana nuna musu ita upside down. Inna ta karba tana dubawa duk da ba gane wa take yi ba fuskarta lullube da farin ciki. “Masha Allah baban biyu, Allahu ya sa albarka a ciki, Allah yasa ka fara a Sa’a. Amma na dauka ba yanzu za’a baku ba sai an gama tantancewa” ya zauna yana cewa “haka ya kamata, amma yaron nan Hassan kinsan shine mai abin, a take ya buga min takarda a matsayin mai gadi ya bani”.

Ruqayyah data fito daga toilet da buta a hannunta ta saki butar “mai gadi?” Ta fada, fuskarta tana nuna bacin ranta “wanne irin maigadi kuma? Yanzu Hassan din ne da kansa ya baka aikin maigadi a kamfanin sa? Wannan ai cin fuska ne”

Inna Ade tace “haba Ruqayyah, in ba’a gode masa ba ai kuwa ba za’a zage shi ba. Aikin gadin bashi baban naku yake nema ba? Ba dan shi ba kuma aikin gadin ma zai iya rasawa ya koma ya cigaba da leburanci da dako” cikin bacin rai Ruqayyah tace “amma wannan lokacin ai ya wuce, wannan sabuwar rayuwa ce, a matsayin sa na wanda zai zama surikinsa ba kamata yayi ya bashi babban office a kamfaninsa ba?” Baba ya fara fada “bana son diban albarka Hassana, da wanne takardun zai bani aikin office din? Me zanyi a office din? Shi cewa yayi ma in hakura da aikin ya bani jari inyi sana’a nace a’a, saboda ni bana son dogara da wani. In ba zaki yi murna da abinda Allah ya bamu ba ki wuce ki bani guri”.

Bata kuma cewa komai ba ta wuce daki tana kunan zuci. Tabbas sai ta takawa Hassan burki, in dai yana sonta sai ya chanja wannan aikin, wannan ai ita zai zubarwa da kima a idon yan’uwansa da sauran jama’ar sa, shikenan kuma sai ace babanta shine mai gadin kamfanin mijinta? Ina! Ai sam ba zata sabu ba.

Da daddare dan halak din yazo zance.

Yaune zuwansa zance officially na farko. Yayi mata kwalliya sosai ya kuma gama shiryo kalaman da zai yi mata. Yayi packing sannan ya aika kiranta. Ita ma kuma a nata bangaren ta saka ran zai zo kuma ta shirya nata kalaman. Dan haka ana cewa ana sallama da ita ta saka hijab ta fesa daya daga cikin turaren da suke cikin kayan Hussain. A bakin kofar gidan ta tsaya ta gyara expression din fuskarta zuwa irin wanda tasan yana so, na yarinya mai kunya da nutsuwa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148Next page

Leave a Reply

Back to top button